Duniya Na Cikin Rikici Fiye Da Shekarun Baya –Rahoto — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Duniya Na Cikin Rikici Fiye Da Shekarun Baya –Rahoto

Published

on


Duniya tana cikin rikici da rigingimu yanzun fiye da shekaru goma da suka gabata, yawanci na sakamakon rikice-rikicen da ke tasowa ne a yankunan gabas ta tsakiya da kuma kasashen Afrika, wanda hakan ke sabbaba asarar tiriliyoyin daloli na tattalin arziki, wani bincike ne na duniya ya tabbatar da hakan a ranar Larabar makon da ya gabata.

“Rashin zaman lafiya na ta kara ja baya a hankali cikin shekaru goma da suka shude,” in ji, Stebe Killelea, shugaban sashen tattalin arziki da zaman lafiya, wanda yake da shalkwata a kasar Australiya.

“Dalilin rashin zaman lafiyar ne na sassan gabas ta tsakiya da wasu yankunan Afrika ke shafan wasu sassan na duniya,” kamar yadda Mista Killelea, ya shaida wa wata kafar yada labarai ta tattaunawar da suka yi da shi ta waya.

Tun a shekarar 2015 ne kasashen Turai ke fuskantar kwararar ‘yan gudun hijira sakamakon yake-yaken da ake a kasashen Libya da Siriya.

Akalla ‘yan gudun hijara daga kasashen Afrika, gabas ta tsakiya da kuma wasu masu yawa ne daga kasar Afganistan suka yi kokarin tsallakawa kasashen Turan ta kasar Turkiyya ko kuma ta ruwa.

A bisa kididdigar cibiyoyin bincike, sun kiyasta cewa rigingimu sun janyo wa tattalin arziki asarar sama da dala triliyon 14.8 kusan dala 2000 ga kowane mutum guda kenan a shekarar 2017 kadai.

“Idan da ace kasashen da ke da karamcin zaman lafiya kamar su, Siriya, Kudancin Sudan da Iraki, za su zama tamkar kasashen da suka fi ko’ina alamun zaman lafiya kamar su, Iceland ko Newzealand.

“Hakan zai kara samar wa da tattalin arzikinsu dala 2000 ga kowane mutum a kasashen nasu, in ji masu binciken.

“Kamar yadda kuke iya gani ne, zaman lafiya yana tattare ne da tattalin arzikin kasa,” in ji Mista Killelea, wanda ya bayyana sakamakon binciken da binciken da kadai ya iya kwatanta tattalin arziki da rigingimu.

Kasashen Turai ne binciken ya sanya a sahun gaba na sashen duniya da ya fi ko’ina zaman lafiya, inda kuma binciken ya siffanta yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afrika a matsayin sassan da ke da karancin zaman lafiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta fada a watan Mayu cewa matsalolin da ke addaban dan adam sun fi yawa a bana a kasar Siriya fiye da kowace shekara cikin shekarun bakwai na rikicin na Siriya.

Sassan yammacin sahara na Afrika su ke da kusan rabin mutane milyan 11.8 da yakuka suka daidaita a duniyar nan.

Advertisement
Click to comment

labarai