An Zana Jan Layin Zaben 2019 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

An Zana Jan Layin Zaben 2019

Published

on


  • Makarfi Ya Bayyana Muradin Yin Takara A PDP
  • Orji Kalu Ya Fara Yi Wa APC Kamfen A Arewa

Alomomi na nuna cewa an zana jan layin babban zabe mai gabatowa na shekarar 2019. Inda ‘yan takarar shugabancin kasa suke ta yekuwar bayyana muradinsu na yin takara.

A gefe guda kuma jam’iyyun siyasar da ake da su suna kara zage damtse don tunkarar wannan babban zabe, su ma daidaikun ‘yan siyasa na ci gaba da tallata kawunansu ga jam’iyyu da al’ummar Nijeriya.

A jiya ne tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, kuma tsohon Shugaban Rikon kwaryar jam’iyyar PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya shiga sahun mutanen da ke da burin shiga fadar Shugaban Kasar Nijeriya ta ‘Aso ‘Rock’ a shekarar 2019.

Sanata Makarfi ya bayyana muradinsa ne a wata zantawa da yayi da manema labarai jiya a garin Kaduna. Inda ya yi shelar cewa; “Bayan tuntubar membobin jam’iyyarmu maza da mata, da masu ruwa da tsaki, ina shaida cewa zan nemi jam’iyyarmu ta tsayar dani takarar Shugabancin Nijeriya.”

A daya bangaren kuwa, tsohon Gwamnan Jihar Abiya, Orji Kalu ya aiwatar da wata jaula a garin Jigawa, inda ya yi wa Jam’iyyar APC kamfen.

A jiya ne Orji Kalu ya ziyarci tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, inda ya bayyana cewa tsohon Gwamnan, Alhaji Sule Lamido abokinsa ne na kut da kut, amma ba zai zabe shi ba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa kamfen.

Orji Kalu ya ce, yana goyon bayan a sake zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda wannan ne zai haifar da hadin kan Nijeriya, ta yadda shi ma Buharin zai iya kammala ayyukan da ya dauko.

Ya kara da cewa, ba ya goyon bayan takarar Sule Lamido, saboda dan PDP ne, jam’iyyar da ya ce, ‘ta tarwatsa lalitar Babban Bankin Nijeriya’ a zamaninta.

Wannan ziyarar ta Orji Kalu zuwa Jihar Jigawa an shirya ta ne domin yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Inda a wurin taron Kalu ya yi wa Obasanjo wankin babban bargo bisa wasikar da ya rubuta yana sukar salon gwamnatin Buhari.

 

Advertisement
Click to comment

labarai