Babu Shugaban Da Ya Bai Wa Gyaran Hanyoyi Muhimmanci Kamar Buhari –Sanata Gaya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Babu Shugaban Da Ya Bai Wa Gyaran Hanyoyi Muhimmanci Kamar Buhari –Sanata Gaya

Published

on


Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, Mai wakiltar Kano Ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, Shugaban Kwamitin Majalisar Kan Ayyuka. Jigo a jam’iyyar APC a matakin kasa, jiha da karamar hukumar. A wannan tattaunawa da ya yi da LEADERSHIP A Yau Asabar, ya yi tsokaci kan zaben Shugaban in APC da za a gudanar a yau da kuma irin ayyukan da kwamitinsa ya gudanar. Ga yadda ta kaya…

Gwamnatinku ta APC ta cika shekaru uku a bisa karagar mulki, wasu nasarori ko kuma wasu tangarda aka samu kawo yau?

Farko dai gwamnatina guda biyu ce, akwai gwamnati a matakin kasa ta shugaba Muhammadu Buhari da kuma a jihar Kano akwai gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ke shugabanta. Idan ka sake dawowa matakin kasa, kasancewar ni Sanata ne yau Allah ya kaddara shekarunmu sha biyu kenan ana yi. Sannan, an yi tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari tun kafin ya ci har Allah ya ba shi nasara a yanzu wanda kuma muna yi masa fatan sake maimaitawa. Buhari ya taka rawa sosai saboda ya zo ne da abubuwa guda uku, a dan siyasa alkawuransa basu yi yawa ba. na farko, ya ce zai kawo zaman lafiya a Nijeriya musamman a Arewa Maso Gabashin kasar wuraren da suka shafi Maiguri, Borno, Yobe, su Adamawa, su Gombe da sauran jahohin da suke kusa da su. Na biyu, ya ce zai yi maganin masu cin hanci da amsar rashawa, zai yi maganinsu ya kame su. Alkawari na uku shine ya ce zai gyara tattalin arzikin kasar Nijeriya. Da na daya da na uku Buhari ya yi kokari domin an samu zaman lafiya Arewa Maso Gabas da sauran yankunan da suke kasar nan, a fadin kasar nan, an samu yawaitar tashe-tashen boma-bomai, za ka ga duk inda za ka wuce a yi ta sanya shigayen bincike suna cajeku, ka ga an samu saukin wannan, a ta bangaren Maiduguri ka ga an farmaki ‘yan Boko Haram din nan daga yankunan da suka mallake, inda suka fantsama zuwa wasu yankuna. Ka san idan ana yaki ba a rana daya ne kawai za a ce gashi an kawo karshensa ba, indai ba irin yakin kasa da kasa ba ne wanda za a iya cewa an janye, kamar yadda aka yi yakin Biyafara aka ce daga yau an daina yakin. Amma in aka ce maka irin yakin sunkuru da yakin ‘yan daba ko yakin ‘yan gurguzu, baka san da wa kake yakin ba, babu kuma ranar kareshi. Amma idan ka koresu daga inda suke a tare ka yi babbar nasara. To, Shugaba Muhammad Buhari ya yi nasara a wannan barin. Na ukun da na ce maka ya yi kokari, wato tattalin arzikin kasa, yanzu za ka ga tattalin arzikin ya fara farfadowa, duk da kayyaki sun yi tsada, amma jama’an kasa sun fara shiga taitayinsu, yanzu misali idan muna shigo da shinkafa ta miliyan dubu, wato kashi 100 bisa 100 ke nan a da, yanzu kashi biyar a cikin dari, idan da ana shigo da buhu dubu to yanzu buhu biyar ake shigowa da shi ko kuma hamsin. Ashe ke nan ka ga an samu sauki, tun da buhu dari tara da hamshin a Nijeriya ake nomashi, yanzu sauran kashi biyar dinma shugaban kasa Buhari yana neman ya sanya dokar da zai tsaida ya kasance muna noma shinkafarmu da kanmu. Kuma shinkafar Nijeriya din nan da muna cewa ba ta da kyau kaza-kaza wai ta waje ta fi kyau, yanzu da aka fara cin ta Nijeriya din sai jama’a suka ji mu kanmu ta fi zaki a gare mu. Ke nan ga gani idan aka samu yadda za a yi a kara inganta shinkafar cikin gidan nan, aka samu injina na sarrafa shinkafar nan sai ka ga yanzu idan ka ga shinkafar Nijeriya da ta kasar wajen sai ka ga ta Nijeriyar ma ta fi kyau domin ta fi zaki da kuma lafiya, ka ga wannan ci gaba ne da aka samu. Muna kuma fatan wannan tsarin nasa ya bijiro mana har ta kan Alkama, domin a kasar nan muna da wuraren shuga Alkama a Kano, Sokoto, Katsina, Jigawa har zuwa Keffi, duk za a iya noma Alkama a wadannan wuraren, don haka muke neman Buhari ya taimaka mana domin fito da wata sabon tsari kamar yadda aka zo mana kan shinkafa a bijiro mana ta Alkama, domin yawan Alkamar da ake shigowa da ita Nijeriya ta kusan fin yawan shinkafar da ake shigowa da ita, da Alkamar nan ake yin Burodi da sauran sarrafe-sarrafen da ake yi, don haka idan aka samu fitar da Alkama hakan zai taimaka wa Nijeriya sosai, kuma hakan zai kawo ci gaba sosai.

Sai mu dawo kan na biyu, Batun yaki da cin hanci da rashawa, yanzu idan ka zo ka ce za ka yaki cin hanci da rashawa koda ka hadu da kai da wasu ba fa karamin aiki ba ne, yanzu idan kuka hadu ku biyar kuka ce zaku yaki cin hanci da rashawa, wata kila ma daya daga cikinku shima yana cikin lamarin cako-cako don haka ba karamin aiki ne ake yi kan yaki da wannan ba. yawancin hassadar da Buhari ke samu yana samu ne ta wajen irin wadannan da ake yaka.

 

Akwai kuma wasu nasarorin kawo yanzu?

Idan ka dauko irin ayyukan hanyoyi da Buhari ke yi, kasancewar nine shugaban kwamitin hanyoyi a majalisar dattawa, Buhari ya bayar da gudunmawa sosai a maganar hanyoyin Nijeriya. Muma majalisar dattawa mun bayar da gudunmawa sosai wajen ganin ababuwa sun tafi a tsare, ta fuskacin tabbatar da cewar an tsara aiyukan nan yadda kowace yanki ta samu cin gajiyar nan. babu wani shugaban da ya  tallafa kan aikin hanya kamar shugaba Buhari tun da ake kafa siyasa a Nijeriya, tun da akwai hanyoyin da PDP ta bari a Nijeriyar nan. hanya tun daga Kano har zuwa Abuja tun lokacin da Babangida ya yi ta ba’a taba yi wa titin nan komai ba koda baci ne sai da Buhari ya zo aka fara gyarawa, yanzu za a yi sabon titi, wadannan ci gaba ne, akwai hanyoyin da suka shafi Yarbawa da yankunan Inyamurai da sauransu, akwai gadar Okari wato Ibi tun Sardauna ake son a yi gadar nan amma bana ta shigo cikin kasafin kudin nan bana. Akwai kuma wata Gada da ta shigo daga Bida ta shiga kasar Nufawa wato Fetagi ta kuma shiga Kwara wannan Gadar a duk lokacin nomar rashi shinkafa ake yi ita ma wannan gadar Buhari ya shigo da ita cikin kasafi. Tabbas Buhari yana aiki a kan hanyoyi sosai a Nijeriya.

Ana ta maganar wadanda rikicin Boko Haram ya rabasu da muhallansu ta yadda za a farfado musu da nasu muhallan don su koma, wasu aiyuka kuka yi a zahirance da za su kai ga taimakawa?

Na farko dai nine Sanata na farko da ya ce a kafa hukumar kula da tallafi da gyara shiyyar Arewa Maso Gabas, nine na gabatar da kudirin samar da wannan hukumar domin jahohi shida da rikicin Boko Haram ya shafa su samu ingantuwa, a zahirance ma mun kara har da jahohin Kano da Filato, inda jahohin suka zama 8. Kamar lokacin da aka yi Niger Delta Commission akwai jahohi biyu da basu cikin yankin Niger Delta aka shigo da su, ba don koma ba don hakan ya taimaka wajen tsara abun yadda ya dace. Ni ne na fara kawo batun, na kuma kawone domin tausaya wa jahohin da rikicin Boko Haram ya shafa, daga bisani ne Sanatocin wannan yankin na Arewa maso gabas suka tashi tsaye suka ce ta yaya wani Sanata daga wata jiha wai ita Kano amma ya fi su damuwa da lamarinsu, sai suka tashi tsaye suka mara wa kudurin baya, irin su Danjuma Goje, Indimi da sauransu suka ce dole sai sun shigo cikin lamarin, na ce ai ba wata matsala aka sanya sunayensu, ranan sai aka yi taro a majalisa dukkanin Sarakunan yankin suna yi ta min godiya, suka bayyana cewar kai Kabiru ba kawai sanata ne daga Kano ba, kai sanatan Nijeriya ne. ka ga wannan abun ina alfahari da yinsa kuma ya kawo mana ci gaba sosai, saboda haka ana ware kudi na musamman domin tallafa wa wannan yankuna, sannan kuma ana ware kudade domin gyara musu hanyoyi da sauransu.

 

Kawo yanzu jam’iyyarku tana fama da rikicin cikin gida a cikin wannan shekaru ukun, wasu ma na ganin wasu daga cikinku ke ruruta lamarin don son wasu su yi shugabanci me za ka ce?    

Gidan da ake da arziki shi ake fada a ciki, idan ana talauci a gida ana fama da yunwa waye zai yi fada? Kowa ya fita yana nemo abun da zai ci. wannan kuma kowa a gida yake an kuma kafa gwamnati to dole ka samu fada irin wannan. Amma duk fadar nan da ake yi ba irin fadar nan da za a sanya wuka a yanka jiki ba ne, a’a fada ne ake yi na ganin kowa ya iya gyara, amma tun da Allah ya ba mu shugaba Muhammadu Buhari ya kamata a ce an dinke matsalar. Allah ya bamu nasara abun da ba mu tsamanin za mu same ta, a da talakawa da illahirin jama’an Nijeriya suka dukufa yi wa shugaba Buhari da APC addu’a har Allah ya sa aka ci zabe, to bai kamata don mun yi nasara mun ci zabe mu zo kuma mu yi irin amsar sadar Almajiri idan ya je ya amsho towonsa da shinkafa sai ‘yan uwansa su taho a guje suna wawar neman abincin har abincin ya je ya kife a kasa, bamu fatan hakan, abun da muke fata shi ne a yi kokari a hade kai a tsakanin gwamnatin tarayya da majalisar tarayya abu daya ne babu bambanci. Kamar ka ce da gwamna ne da majalisar jiharsa, na yi gwamna na san martabar gwamna na san martabar majalisa, duk wanda yake gwamna a Nijeriya kuma yana zaune lafiya za ka samu yana hada kai da ‘yan majalisarsa, saboda haka ya kamata shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya hada kai da ‘yan majalisarsa, shi Uba ne mu ‘ya’ya ne, ‘ya’ya za su iya laifi ubansu ya yi musu fada ya ce ‘ya’yan nan meye sa kuka yi laifi? Sai su ce baba mun tuba, mu kuma ba za mu je duniya mu ce baba ya yi laifi ba, domin ba za ka zo ka ce wa ubanka ya yi laifi ba.

Ba za ka fito duniya kana cewa baba ya yi kaza ba; ba za ka ce babanka ya yi laifi ba, sai dai ka yi kuskus ka ce baba a gyara kaza. Amma Buhari yana da kyakkayawar nufi yana da zuciyar ganin an taimaka, kuma shi soja ne mai son a yi komai da gaggauwa, ita kuma majalisa da demokradiyya daban take, kamar yadda yake fada da kansa shi a yanda ya sani a da, shi ne duk wanda yake barawo ne a kamasa barawo ne kawai, a kaisa a dakatar da shi ko a daure shi, ba za a sake shi ba har sai an tabbatar da shi ba barawo ba ne. to dokar yanzu ba haka take ba, ba za a taba tabbatar da kai mai laifi bane sai an je kotu, kotu ta tabbatar da shi barawo ne, in ma ka kamasa kotu ta ce ka sakeshi, duk irin wadannan abubuwan fa ba daidai bane amma yana karantawa yana ganewa, muma muna karantawa muna ganewa za a hadu a gaba a tafi tare. Ita tafiyar mulkin Nijeriya kala-kala ne babu wanda bai da amfani, in zabe za a yi kowa na da amfani, liman yana da amfani fasto yana da amfani, karuwa tana da amfani, shugaban gidan giya yana da amfani, duk suna da kuri’a daya-daya, idan ka ce baka son kuri’ar shugaban gidan giya to wata kuri’ar ka kara domin yana da kungiyarsa da kuma mambobin masu shan giya ai, in ka ce ba ka son karuwa ita ma tana da kuri’arta, sai a hada da karuwa da shugaban gidan giya a kori shugaba mai kirki, amma in kai shugaba mai kirki ne kana kuma tafiya da kowa, a sannu a hankali kana nusar da su sai ka ga karuwa ta yi aure, barawo sai ya daina sata, mai shan giya sai ya daina, matasa masu aikin banza sai su daina. Amma kafin ka hau dole sai ka nemesu don a hadu a gyara. Buhari ya dau hanyar gyaran nan, amma fa ba a rana daya ba, muna fatan Allah ya bashi nasara a zaben da ke tafe domin ya ci gaba da daurawa daga gyaran da yake yi.

 

Me za ka ce kan babban zaben APC na kasa ganin cewar akwai hasashen rashin jituwa da wasu jiga-jigai?

Duk abun da zaman lafiya bai bada shi ba tashin hankali ba zai bayar da shi ba. mun yi karatu a siyasar nan mun dade muna yenta tun 1982 ne ke siyasa har zuwa yau, maganar gaskiya duk yadda ka ga ana samun rashin jituwa a siyasance to ba a samun nasara daga karshe, amma yadda muka taho a Kano matsalar babbace, matsaloli biyu ce wacce bana son na maka dalla-dallah a jarida, ba don komai ba saboda da gwamna Ganduje da Kwankwaso, Kabiru Gaya da Shekarau dukka mun yi gwamna a Kano, dukkaninmu kuma ya kamata mu san idan gwamna ya na kan kujera mu bashi mutuncinsa. Ni na yi gwamna, dukkaninsu na rigasu yin gwamnan jihar Kano, na rigasu barin gwamna don haka nine na gaba da su a gwamna, nine wansu a gwamna, a shekaru wasu sun fini, amma abun da na sani yau, da na yi gwamna Shekarau a lokacin na ma’aikacin gwamnati, Ganduje na ma’aikacin gwamnati, Kwankwaso na ma’aikcin gwamnati dukkaninsu kuma sun bani girma amma na yi gwamna, Kwankwaso ya girmeni a shekaru amma na yi gwamna, amma da na ke gwamna hatta marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ai ya bani martaba ai uba ne a wajena, duk wanda Allah ya daga gwamna ya zama shugabanka ne ka bashi girmansa kawai. In ka bashi girmansa shi kenan kaima sai ya girmamaka, wannan shine matsalarmu a Kano. Kai kuma gwamna idan ka zo gwamna ka baiwa kowa mutuncinsa. Idan Allah ya baka mulki ka rungumi kowa, shi ya sa ni a rayuwata na ke da juriya ba don komai ba idan ka ce za ka bata da masoyi gobe sai ka rasa masoyi. Amma idan ka duba dukkanin lamarin idan da an bi ta wasu hanyoyi da ba za a samu irin wannan ba, amma muna fatan lamarin ya zo mana da sauki.

 

A matsayinka na tsohon gwamnan Kano ya kake kallon kamun ludiyin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje?

Yana iya kokarinsa maganar gaskiya. Wato idan mutum ya yi mulki kwana bakwai a jihar Kano ka ga  ba a yi fada ba to ka gode mishi, ballantana Ganduje shekarunsa uku, wanda kuma hudu zai yi, yanzu ma har ana cewa 4+4 ka ga kenan ana da sha’awar ya koma. Ni zai shaida yana kokari, duk wanda zai ce bar ya sanya gwamnan a sikeli ya gani yana aiki ko yaya ba zai kai i-ni ba, saboda ni na yi gwamnan na san matsalarta na kuma san yadda kujerar take. Matsalolin mutane ta ninka fiye da lokacin da ni na yi gwamna, yana kokari muna fasa fatan ya kara.

 

Me za ka ce kan zaben APC wanda zai gudana yau?

Zaben APC na cike gurbi ko na zaben shugabanin na kasa muna kan kokarin ganin ba a samu matsala ba; duk zaben da za ka yi ba a yi rigamar zaben fidda gwani ba ai shi ya fi sauki, duk zaben da za a yi a taro a gida daya ya fi sauki, duk zabe ne na cikin gida kai wane yi hakuri tafi ka je ka nemi wannan, kai wane nemi wannan, wannan shine siyasa ta gari. Amma yanzu kamar yadda Oshomele ke neman, sai a samu wani tsohon gwamna shi ma kato to za a samu matsala a jam’iyya, amma da yake mai nema dinma dan jiharsa ne kuma ma kamar ba a san mutumin ba lamarin zai zama babu matsala, duk zaben da za a yi a samu maslaha ai itace zabe. Yanzu misali a kano in za a sake dan takarar gwamna a zaben 2019 ai babu dan takara sai Ganduje, duk wanda ma zai fito sai mu ce masa ka hakura, haka ‘yan majalisunmu da sanatocinmu idan mutum yana abu mai kyau don me za a ce a canza shi? Wadansu da dama shugabanin za su koma kujerunsu, wasu kujerun kuma za a yi zabe. Duk da yake za a kai dare Amma insha Allah za a yi lafiya a kare lafiya, kuma zai kara hada kan jam’iyya.

Shawarata ga Oshomole shine yana da aiki a gabansa cewa akwai baraka a APC, amma duk da barakar da ke APC ta fi PDP kokari, domin ita PDP bata da kai bata da gindi, don haka ya kafa kwamiti mai karfi da zai je ya gyara barakokin da suke akwai. Kamar misali matsalolin ‘yan majalisu da gwamnatin tarayya a gyara matsaloli, matsalolin gwamnoni da ‘yan majalisun su a gyara tsakani, ‘yan majalisu da jama’ansu a gyara, ana yin wannan APC ta gyaru, idan hakan ta kasance babu wata jam’iyyar za ka ji ta.

 

Me za ka ce kan barazar cewa wasu idan aka yi zaben nan basu samu ci ba za su fice daga jam’iyyar?

Wannan dalilin ne ya sanya na ce maka idan Oshimole ya ci sai ya kafa kwamiti koda sun tafi za su dawo. Wadanda suka fita daga PDP ai akwai dalili gwamnatin Jonathan an gaji da ita ta rigaya ta tafi ta yi alkafira. APC babu irin wannan alkafirar matsalolin ne kawai kuma za a gyara.

 

Wasu shawara za aka bai wa ‘yan uwanka masu gudanar da wannan zaben?

Shawarata mu mara wa tsarin da jam’iyyar ta fitar baya domin a samu nasarar gudanar da zabe mai nagarta. Kuma mu nuna wa daya jam’iyyar darasi na cewar za mu gyara gidanmu za kuma nu gyara kasar nan.

Advertisement
Click to comment

labarai