Kawo Sabon Kwanturola Ya Zame Wa Tsararru Rahama –Abdullahi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Kawo Sabon Kwanturola Ya Zame Wa Tsararru Rahama –Abdullahi

Published

on


Magaji Ahmed Abdullahi, Shi ne Kwanturolan Hukumar Gidajen yari, wanda ya yi gudu har da zamiya wajen bayyana irin nasarorin da shugaban Hukumar na kasa ya cim ma cikin shekaru biyu da ya yi a kan wannan mukami. A tattaunawarsa da wakilanmu na Kano Abdullahi Muhammad Sheka da Na’ima Abubakar, ya yi dogon bayani kan nasarar da ya samu zuwansa Kano. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

Za mu so ka gabatarwa da mai karatu kan ka da kanka?

Sunana Magaji Ahmed Abdullahi, kuma a halin yanzu ni ne shugaban Hukumar Gidajen Yari ta Jihar Kano.

 

Mai girma shugaban kasa ya kuduri aniyar rage cinkoson gidajen yarin kasar nan, jihar Kano ce jihar da ta zarta sauran yawan jama’a, shin ko ya halin gidajen yarin da ke karkashin ikonka suke cika a Kano?

Kamar yadda aka sani na smau gidajen yari goma a Jihar Kano wanda babbansu shi ne wanda ke Kurmawa wanda ke dauke da mutane a halin yanzu guda 2081 sai kuma na Goron Dutse wanda ke dauke da mutum 1,550, sai na Wudil mai mutum 600 sauran da suke  Sumaila da Rano da Tudunwada da Kiru da Gwarzo da Bichi da DawakinTofa suna rufe mutane ba su wuce 90 ba.

Maganar Cinkoso da ka tambaya shi ne mutanen da ke cikin wadanan gidajen yari sun fi karfi adadin da aka gina gidan domin ajiyewa, misali Gidan Kurku na Kurmawa an gina shi bisa zaton ajiye mutun 750, amma yanzu akwai sama da mutun dubu biyu a cikinsa, haka Goron Dutse an yi shi domin a je mutum 680 amma yanzu suna da sama da 1500. Wannan ta sa cinkoso ya zama babban kalubale ga tafiyar da gidajen yari na kasa a yau. Kuma wannan cinkoso na haifar da abubuwa da suka hadar da rashin tsafta, cututtuka ga ma’aikata da kuma daurarru da kuma wuraren koyon sana’a ya yi karanci.

Sannan kuma matsalar cinkoso alokuta da dama kan haifar da matsalar kokarin guduwar wasu daurarrun da kuma fuskantar matsalar tawaye. Saboda haka a lokuta da dama gudanar da harkokin gidan kan fuskanci matsala da kuma barazana ga jami’an na gidajen yari.

 

Kan rage cinkoso a gidajen yarin  kasar nan, zuwa yanzu da gwamnatin ta shiga shekaru uku a kan karagar mulki, shin ko kwalliya ta fara biyan kudin Sabulu?

Zuwan wannan gwamnatin ta taimaka kwarai da gaske, domin gwamnati ce mai hangen nesa, kasancewar hankalin ta na kan wadanda suke waje da kuma wadanda ke daure. An samu shugabanni masu kaunar kawo sauyi cikin harkokin gidajen yari, wanda suka tsara yadda sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga har cikin gidan Kurkun Kurmawa inda ya ganewa idonsa halin da gidan yarin ke ciki, wannan tasa dole na godewa Gwamnan kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Ministan Harkokin cikin gida mai ritaya Abdurrahaman Bello Danbazau da shugaban Hukumar gidajen yari na kasa Alhaji Jafar Ahmad.

Bayan kammala  ziyarar wanna gidan Kurkuke ne da komawar shugaban Kasa, wanda ba a taba samun wani shugaban kasa da yake kan karagar mulki da taba shiga kurkkuku ya duba halin da daurarru ke ci sai Muhammadu Buhari, komawarsa ke da  ya kafa wani kakkarfan kwamiti karkashin  Mai Sharia Ishak Bello, wanda suka yi aiki ka’in da na’in.

 

Ministan Harkokin Cikin gida ya kaddamar da ginin gidan yari irin na zamani a Kano inda aka bayyana cewa har da tsarin koyar da sana’u da kuma harkar noma, me za ka ce dangane da wannan hobbasa na gwamnatin tarayya?

Kamar yadda na fara ambata maka cewar kafa wancan kwamiti da na ambata ne suka bayar da shawarwarin samar da karin gudajen yari inda aka tsara gina  sabbin gidajen yari guda shida a shiyyoyin kasar nan, kuma kamar yadda aka sani Gwamna Ganduje shi ne gwamnan da ya fara bayar da fili tare biyan diyya ga masu gonaki.

An fara aiki gina wannan gidan yari wanda zai dauki mutum 3,000 anan ana aikin a garin  Janugza kuma tuni aiki ya yi nisa domin aiki anci kashi 60 daga cikin 100. Tsarin wannan aiki an tanadi Komai akwai dakunan kwana irin na zamani, ga wurare koyar da sana’u, harkar noma sashin kula da lafiya, an tabbatar da cewa idan an gama aikin wannan gidan yari babu wata mai kasa mai irin wannan gidan yari.

 

Ranka ya dade mene ne dalilin da ke kawo wannan cinkoso a gidajen yari?

Kamar yadda na fada tun da fari an gina wadannan gidajen yari shekaru aru-aru, misali gidan yarin Farauruwa an gina a shekara  1910 shekaru  108 da suka gabata kuma an gina shi bisa tsari na  mutum 750, amma yanzu mutane da ke cikin gidan yarin Kurmawa sun haura mutun dubu biyu. Saboda haka dole a samu cinkoso, musamman idan aka yi la’akari karuwar al’umma sannan kuma jihar Kano jiha ce ta cibiyar kasuwanci wadda ke karbar baki daga ina hakan ya sa dole a samu yawaitar masu aikata laifuka iri daban-daban.

 

Wasu na ganin da zarar an ambaci gidan yari ana nufin wani wurin kunci ne, shin  ranka ya dade kila jama’a za su so jin abin da ake nufi da gidan yari?

Gaskiya ne jama’a sun yi wa Kalmar gidan yari mumuunar fahimta domin wuri ne na gyaran halayya, kasancewar da yawa ma zauna wannan gida wasu kaddara ceta kai su, don haka wuri ne da ake kokarin saita halayyar wanda ya tsinci kansa acikin gidan tare da fatan idan ya koma cikin jama’a ya zama nagartacce.

 

Wanda duk ya sha inuwar gemu ba kamar makogoro ba, shin ya kake ganin irin gudummawar shugaban Hukumar gidajen yarin kasar Alhaji Jafaru  Ahmad?

Kamar yadda na ambata duk inda ka hangi nasara babu shakka an samu jajirtaccen jagora, Alhaji Jafaru Ahmad sanin kowa ne  gogaggen ma’aikaci ne hakan ta sa a shekara biyu da zuwansa wannan hukuma, bayan ya yi wa  harkokin hukumar kallon tsanaki ne ya fara da aiki gyaran tarbiyar ma’aikata, tabbtaar da gaskiya da rokon amana.

Hazalika wannan jagora namu ya tabbatar da bayar da gudummwarsa ga ma’aikata, musamman batun  ciyar ma’aikata sama da dubu  20,000, kafin zuwansa akwai masu shekara 15 ba tare da samun karin girma ba. Ni kai na ina matsayin mukaddshin kwantarola tsawon shekara goma sha daya, sai da Allah ya kawo shi sanan na motsa zuwa Kwantirola.Haka kuma  kwanan nan za a kara fitar da wani Jerin  sunayen wadanda ake sa ran ciyarwa gaba,

Cikin tagomashin da hukumar gidan yari ta samu zuwan wannan bawan Allah ya tabbatar inganata harkar tsafata tsakanin ma’aikata ta fuskar samar da uniform saiti biyu ga dukwa wani Jami’in gidan yari da ke kasarnan, Sannan kuma Ja’afar Ahmad ya gwangwaje dukkan manyan jami’an wanna hukuma da motocin aiki sabbi.

 

Ya danganta ka take tsakanin ka da Jami’an wannan Hukuma tunwanka Kano?

Alhamdulillahi Koyi muke da jagoranmu na kasa, shi ma’aikaci na son ka kyautata masa, saboda haka tun zuwa na Jihar Kano abinda na mayar da hankali kenan wajen tabbatar da kyakkyawar danganta tsaknina da abokan aikina, duk wani hakki nasu na kanyi bakin kokari wajen ganin sun same shi, kuma alhadulillahi ido ba mudu ya sasan kima, ina samun hadin kan abokan aiki na yadda ya kamata

 

Mene ne sakonka ga al’ummar Kano, musamman kan abin da ya shafi batun gidajen yari?

Sakona bag a Jama’ar Kano kadai ba harma kasa baki daya shi ne jama’a su fahici mu hidimace muek yi wa al’umma, da yawa mutane har yanzu ba sa san muhimmacin gidanyari ba, mune tsaron baki daya, don haka mu rumbune na bayanai don haka wannan aiki ne mai muhimmanci ga kowa, kamar yadda aka sani shi gadan yari tunda Allah ya yi halitta yana nan a tsarin  wanda duk y aaikata laifi aje a hukunta shi. Kiran da zan yi ke nan jama’a su fahimci ayyukan gidjjen yari aiki ne na tsaftace al’umma mu matsayin rariya muke, wannan shi ne kira na ga jama’a. da wasu  da suka shiga cikin hali irin nasu, su hada kansu suma su kasance ma al’umma  alakakai a rayuwar su. Yarinya wata kuma idan ba sa’a aka yi ba, sai a nemi  bukatar sai an yi aikin banza da ita daga baya kuma a ba ta damar wucewa da karatu zangaya ta gaba, wadda kuma bata bada hadin kan hakan ba, sai ta kasance ta baya ga dangi a makaranta. Wani malamin shi al’amarin anshi ma yana da ban tsoro dalili kuwa a rashin adalcin da wasu kan tafka sai ya kasance, wadanda basu kamata su wuce zangaya ta gaba ba, sai watarana a ce ai sun wuce shekarar karatu ta gaba.

Shi al’amarin ai bai tsaya a makaranta ba da gida kadai , sune wuraren kadai da akan nuna shi rashin adalcin ba, saboda kuwa idan aka leka yadda ake  daukar ma’aikata, nan ma abin bai canza zane ba, saboda kwamacalar da akan yi, na rashin adalcin daukar ma’aikata. Wani abin haushi sai a buga sanarwa a jaridu ana bukatar daukar ma’aikata, wasu suna bata lokacinsu da kudinsu, saboda su samu halartar ita yin jarabawar ko kuma ganawa da masu neman aikin, bayan kuma su wadannan masu shirya ita jarabawar ko ganawa da masu neman a dauke su aiki, sun san iyakar mutanen da za a dauka, amma maimakon su yi ma wasu  adalci, sai sun sa , sun kashe kudadensu da dukiyoyinsu, amma sai duk kidan nasu ya kare a jinjina.

Ana dai bata ma wasu lokaci ne  kawai bayan an san ko mutum nawa ne za a dauka, ba kuma dole bane sai sun zo, sun rubuta jarabawa bas u wadanda za a daukar, irinsu ‘ya’yan Mowar an dade da basu offer din,(Takardar Shaidar Daukar Aiki) ko sun cancanta, ko kuma basu cancanta ba. ‘Yan Borar kuma sai su tafi da iyawarsu can , ba abin da ya damu kowa. Ta haka ake daukar wasu aiki saboda alfarmar data sa aka ki yi ma wasu adalci na  a, basu dama saboda suma sun iya , sai kuma an gwada akan san na kwarai. A basu aiki su kasa yin komai, har ma a kai ga gane shin me ke faruwa ne, dan haka sai su yi ta kwaba shirme a  wajen aikin, saboda daman an daukesu ne ba tare da sun yi jarabawar da kuma ganawa da wadanda za a dauka aikin ya kamata su yi.

Maganar Hukumar shirya jarabawar shiga jami’oi da kuma sauran manyan makarantu (JAMB) wannnan shekarar fiye da dalibai miliyan daya da rabi ne, suka dauki jarabawar, idan kuma ba sa’a, aka yi ba, zai yi wuya a dauki rabin miliyan da ba su damar zuwa jami’oi da sauran manyan makarantun ba, wannan ya nuna ke nan, sauran kamar ba a yi masu adalci ba ke nan, ga kuma yaudara saboda kuwa ai ita Hukumar ya dace ta san yawan daliban da za su samu damar shiga makarantun, don haka me kuma zai sa a sa wasu su bata kudadensu ta wajen sayen fom da kuma rubuta ita jarabawar da kuma lokaci , bayan kuma an san daga karshe ba daukarsu za a yi ba.

Tsakanin ita Hukumar zabe da kuma jam’iyyun siyasa sun san irin rashin adalcin da sukan yi wa al’umma, a dalilin rashin tsayar masu da wadanda suke son su zaba, maimakon haka ma, sai a basu wanda zai ta gasa masu Aya a kan Kunba , ba yadda zasu yi. Don haka ya dai kamata wai auren na gida yarinya ko bata ci abinci ba ta ga Mama da Baba, duk al’amuran da nayi bayani akansu, ana amfani da rashin adalci, wanda kuma daga karshen idan abin ya kai karshen mizanin shi, to abin fa ba wani kyau zai yi ba, a kula da yin adalci , a kuma guji yin zaluci. Saboda Allah Subhanahu wata’alah mahillancin mu ya yi koyi da ayi  adalci da kuma hani ga yin zalinci , saboda shi adali ne.

 

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai