Ganduje, Saraki Da Barau Za Su Kaddamar Da Fim Don Hana Rikicin Addini — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

Ganduje, Saraki Da Barau Za Su Kaddamar Da Fim Don Hana Rikicin Addini

Published

on


Gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje da hadin gwiwar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Dr. Bukola Saraki, da sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Barau I. Jibril, za su kaddamar da wani sabon gagarumin fim din Hausa mai suna ‘Mutum Da Addininsa’, domin kawo karshen rikicin da ke faruwa a tsakankanin kabilun Najeriya kan bambancin addini da kuma muhimmancin zaman lafiya.

Shugaban kamfanin da ya shirya fim din Mutum Da Addininsa, wato Chali Enterprises, Alhaji Aliyu Salilsu, shi ne ya bayyana wa manema labarai a cikin makon nan, inda ya yi karin haske da cewa, za a kaddamar da fim din ne ranar 15 ga Yuli, 2018, a babban dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar Kano, wato Choronation Hall, inda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zai kasance uban taro.

“Mai girma Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Barau Jibri, shi ne babban mai kaddamarwa, sannan kuma Mai girma gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje zai kasance mai masaukin baki a wajen taron kaddamarwar,” in ji Alhaji Chali, wanda dan kasuwa ne mai sayar da finafinan Hausa da shirya su.

Ya kara da cewa, “wadannan manyan mutane sun amince tari gabaran kaddamar da wannan fim din na Mutum Da Addininsa ne, saboda irin sakon da ya kunsa na kira ga jama’a da su zamo masu hakuri da juriya a zaman tare, musamman kasa irin Najeriya, wacce ta ke da mabambantan addini da kabilu.

“Haka nan kuma Mutum Da Addininsa ta tabo batun almajiranci, wanda ke addabar al’ummar Arewacin Najeriya. To, kowa ya san gwamnan jihar Kano Kadhimul Islam ne, wato mai yiwa addini hidima. Don haka ya ke ba mu dukkan goyon bayan da ya kamata kuma ya dauki wannan fim tamkar nasa ne, saboda magana a ke yi a kan hidimar addini da kuma taimakon maras karfi.

“Shi ma Sanata Barau kowa ya san shi a kan hidimtawa al’umma. Don haka ne ya ba mu dukkan hadin kan da ya kamata wajen ganin ya kaddamar da wannan fim, wanda sadakatul jariya ne.

“Lokacin da mu ka ziyarci Sanata Saraki ya yi nazari kan irin sakonnin da fim din Mutum Da Addininsa ya kunsa ya yi matukar farin ciki da abinda ya gani, saboda hanya ce ta dinke barakar da ke tsakanin mabiyan manyan addinan kasar, musamman Musulunci da Kiristanci. Bisa wannan dalilin ne ya bar dukkan abinda ya ke a lokacin ba mu cikakken lokacinsa kuma ya dauki alkawarin daukar nauyin fim din.

“Wannan taro ne wanda ba a taba yin irinsa a Kannywood ba, saboda ya hada manyan mutane daga ko’ina a Najeriya da kuma manyan addinan kasar, kamar masu daraja malamai da limaman coci.”

Magaji Maikarama, wanda dan kwamitin kaddamarwar ne, ya shaida wa wakilinmu cewa, an kashe akalla Naira miliyan 36 wajen shirya fim din, sannan kuma an ziyarci jihohi da dama a yayin daukar fim na Mutum Da Addininsa, wadanda su ka hada da Edo, Lagos, Neja, Kano, Filato, Kaduna da Abuja.

Sannan Maikarama ya kara cewa, “sako na uku kuma a cikin fim din bayan kawo karshen rikicin addini da almajiranci, Mutum Da Addininsa ya ja wo hankali kan batun shaye-shaye da matasa su ka tsinci kansu ciki a wannan zamanin. An yi jan hankali mai yawa a kan hakan, saboda wannan ma matsala ce wacce ta damu kasarmu a lokacin nan.”

Shi ma Salisu Kani Dandago, wanda daya daga cikin mambobin taron kaddamarwar ne, ya yi karin haske da cewa, “manufar shirya wannan fim din ita ce, tabbatar da cewa an samu zaman lafiya da ’yan uwantakar juna a Najeriya ba tare da la’akari da bambamcin addini ko al’ada ba. Irin wannan kashe-kashe da ke faruwa a kasar nan da sunan addini, mun yi amannar cewa bai dace ba kuma wadannan shugabanni da ke kokarin kaddamar da fim din Mutum Da Addininsa sun yi allawadarai da faruwar hakan ne. Don haka su ka shigo ciki ka’indana’in, don tabbatar da cewa an samu nasara mai dorewa kuma Najeriya ta samu zamalm lafiya mai wanzuwa a cikin al’umma.”

Fim din Mutum Da Addininsa dai ya kunshi manyan jaruman Kannywood irinsu Ali Nuhu, Tijjani Faraga da kuma jarumai mai tasowa, Maryam Habila.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!