Connect with us

MAKALAR YAU

Fyade A Cikin Aure?

Published

on

A yan kwanakin nan shafin Facebook ya cika da maganar, shin ana yin fyade a cikin aure? Maganar ta yi yawo, asali da harshen Ingilishi sannan zuwa yaren Hausa. Ban san wace mace ce ta assasa hirar ba, amma bisa yadda na kalli maganar daga rubutun Adamu Tilde yana nuna mace ce ta taso da maganar. Rubutun Aliyu Jalal kuwa cikin harshen Ingilishi, yana nuna mata basu bawa maganar muhimmanci ba kamar dai yadda suka saba a duk maganganun da ake a shafukan sada zumunta koda sun shafesu. To amma ina ga hakan yana da alaka da rashin yawan mata a Facebook da Twitter idan an kwatanta da maza, da kuma tsoronsu na kada a kallesu ta wata fuskar maimakon a fahimcesu. Maganar kunya ma tana daga ciki, tunda maza sun fi fitowa su yi maganar da idan mace ta yi za a kalla da fuskar rashin kunya.
Maganar fyade a cikin aure, tsakanin masu ganin ana yi da wadanda suke ganin babu yadda za a ce ana yi, tana bukatar fadada bincike don sanin tushen abin. Idan ya kasance tilasa yin jima’i ba tare da macen na so ba sunansa fyade, kuma ya zama hakan na da alakar cutar da mace irin yadda jima’in karfi yake janyowa; to ko bamu kira hakan da fyade a harshe ba zai zama babbar cutarwa ga ita macen. Kalmomi da sunaye ba su ne suke bamu ma’anar abu ba, tsarin yadda aka yi abin shi ne zai bayar da ma’anarsa. Kuna ganin wanda ya gina gida kuma ya kira gidan da mota zai bayu ga komawar gidan mota? Ko karuwar da take zaune da dadiro mai kula da ita kamar miji za a kirata da matar aure ko da tace auren tayi? Don haka, ko da an kira yin jima’i da karfi “fyade” ko an kirashi “soyayya”, ba dai a canjawa tuwo suna.
Tun asali akwai bukatar ilimin jima’i, ba wai ga yara kananu a makarantu ba, ga su wadanda suke shirin yin aure. Mafi kankantar lokaci ace an fara koya musu yadda banbancin jima’i yake tsakanin mace da namiji da kuma yadda za su iya tunkarar junansu. Bahaushe yana da irin tsarin koyar da ilimin jima’i ba sai an aro “Sed Education” agun turawa ba. A yanzu duk an lalace ne. Litattafai irin su “Gishirin Ma’aurata” an canja musu ma’ana. Maimakon kuma a samu sahihiyar hanyar koyar da zamantakewar aure sai wadanda suke shirin aure su zubar da awoyi wajen kallon fina-finan batsa (blue film) wanda masana sun tabbatar da ba ya nuna zahirin abinda yake faruwa a jima’in gaske. Wasu ma’auratan, abin takaici, shi wannan suke kalla domin su koyi salo-salo na karyar jima’in.
Fyade babbar illace da take lalata rayuwar mace, babba ko yarinya. Mafi muni daga ciki shi ne yana dauke mata sha’awar jima’in kwata-kwata. Don haka wasu daga malaman musulinci suka ce duk namijin da aka kama ya yi wa mace fyade to dole sai ya biyata diyyar rai! Wannan yana nuna tamkar wacce aka yi wa fyade an kasheta a tsaye ne. Idan ya kasance tursasawa ita take janyo illar da fyade yake janyowa, wa zai so ya mayar da matarsa gunki? Wa zai so rashin hakurin minti biyar ya janyo masa hakurin auren baki daya?
Akwai bukatar maza su san banbancinsu da mace wajen yadda sha’awar jima’i take tashi. Sabanin namiji da take ciyoshi yazo gun matarsa, ita mace namijin ne zai tayar mata. Don haka a mafi yawan lokaci namiji ne yake fara kusantar iyalinsa ba mace ba. Wannan yana da alaka da tsarin mata, ba wai kunya bace (dukda da akwai kunyar wani lokacin). Wannan tasa Manzon Allah (saw) ya gayawa sahabbai cewa duk wanda zai nufi iyalinsa da jima’i to ya aikata dan sako. Suka tambayeshi, mene ne dan sako? Ya fahimtar da su irin su sumbata (kiss), shafe-shafe da sauransu. A wani hadisin har misali ya basu da cewa hatta bunsuru ba ya kusantar iyalinsa tafarar daya. Kai za ka so ace bunsuru ma ya fi ka iya tafiyar da akuya akan yadda kake tafiyar da iyalinka?
Kafin a je maganar matar ta ki yarda da miji ya yi tarayya da ita, ya kamata a kalli me ya janyo matsalar da har matar aure take gudun mijinta. Ba tsayawa wa’azi da gayamata cewa mala’iku suna tsinemata zaka yi ba. Ka tsaya ka tambayi kanka domin watakila kai mala’ikun suke tsinewa. Wasu suna kwanciya da iyalinsu kamar sun zo shan ruwa. Irin dai abinda Manzon Allah (saw) ya hana har yake cewa duk wanda ya gama bukatarsa to ya tsaya matarsa ta biya tata. Tun a farkon aurensu ya fara da shi kansa kawai ya sani. Daga ya gama abinda zai yi sai ya tashi ya tafi ko da ita tana rabin hanya. Wata malamar ilimin jima’i (Sedology) tana bayar da misalin irin wannan yanayi sai take cewa :
“Tamkar ace kai da budurwarka ne ko matarka kun fita zuwa wani kayataccen guri, dukanku kuna farin ciki. Ana ta tafiya a jirgin kasa ko mota kuna ta hira mai dadi. Kun ci rabin tafiya, kana Allah-Allah aje gun, kawai baka lura ba sai kaga abokiyar tafiyarka ta tsayar da motar ta koma gida! Ko da ka ji dadin farkon tafiyar to daga karshe bakin cikin hukuncin da ka dauka zai shafe duk wani farin ciki da ka fara diba da farko. Daga karshe kuma sai ka ji ba zaka kara daukota ku fita yawon ba.”
To tamkar haka abin yake faruwa ga wasu matan. Mazansu su suke janyo matsalar da take sanyawa fara tsanar tarayya da su. Daga nan kuma sai miji ya fara tunanin yi wa matarsa dole tunda hakkinsa ne yake ganin ta hanashi don haka sai ya kwata da karfi.
A al’ummar kuwa da ta sanya manufar aure akan jima’i kuwa dole duk lokacin da aka kasa cinma manufa a dinga samun rabuwar aure ko lalacewar zamantakewarsa. Tun asali shi Allah (SWT) ya dora mazaunan aure su zama soyayya da jin kai ne, maimakon jima’i. Duk kam mai kaunar matarsa kuma yana tausayinta babu yadda za a yi ya iya yi mata dole don ta ce ba zata kwanta da shi ba. Zai yi mata uzuri dubu saboda soyayya. Amma wanda dama yake ganin ya aure injin jima’i ne to fa babu ta yadda zai iya hakura tunda yana ganin ya zubawa injin mai, aiki kawai ya ragemasa.
Don haka, maganar yin dole a jima’i yayin aure akwaita, ko da an kira hakan da fyade ko ba haka ba. Sau dayawa matan da ake zargin suna kukan cewa ana yi musu fyade a gidan aure, su ne kuma suka fi kowa neman hanyar da za su bawa miji damar jin dadin aure. Su ne kuma zaka gani suna ta yawon neman “kayan ni’ima” daga wannan kasuwa zuwa wannan kasuwa. Su ne hankalinsu ya fi tashi idan suka lura mijinsu baya kula su. Su siyo matsattsun kayan gwanjo ko kuma na yan kanti. Mafi yawan lokaci rigimar matan aure akan bashi za ka ga ta kayan gwanjon da aka ranto don a yi masa kwalliya ne ko kuma na kayan ni’imar da za a sha don ya ji dadi ne.
Ya kamata mu tsaya mu kalli abin ta fuskoki dayawa ba ta fuskar zaton cewa an dauko wannan daga gun turawa bane. Matsalar jima’i ba iya turawa ta shafa ba, duk mutum ta shafe shi. Masu zuwa kallon fina-finan batsa basa lura da turawa ne suke yi ko bakake ne balle kuma Hausawa. Su dai abinda ya shafesu su kallo abinda za su gwada akan iyalinsu. Idan kam ya zama cewa ana koyo abinda za a gwada akan iyali daga gun turawa to tabbas za a hadu da matsala irin ta turawa. Don maganin hakan, akwai bukatar a koma a kalli me ya janyo iyaye da kakanni basu da matsala irin tamu? Shin saboda su don ba su kalli fina-finan batsa bane ko kuma don “Gishirin Ma’aurata” suka karanta? Fadin cewar a dinga kula da abinda iyali za su karanta ko za su kalla a wannan zamanin na intanet ba zai yiwu ba. Ana bukatar hakan amma ba duk abinda ake bukata ne zai yiwu ba. Abinda ya kamata shi ne mu koya kuma mu koyar da yadda tsarin jima’i yake tsakanin ma’aurata ga wadanda suka kusa yin aure.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!