Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Buhari Ta Taka Rawar Gani Wajen Daga Tattalin Arzikin Kasa -Alhaji Ya’u

Published

on

Wani fitaccen dan kasuwa, kuma mai fada a ji a harkar noma, Alhaji Ya’u Adamu Danfulani ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ta taka rawar gani wajen daga tattalin arzikin kasa da inganta tsaro. Alhaji Adamu Danfulani ya sanar da haka ne cikin zantawarsa da Jaridar Leadership A YAU ASABAR ,a makon da ya gabata a Zariya
Ya ce Gwamnatin shugaba Buhari sai san barka ta harka farfado da tattalin arziki ,da tabbatar da tsaro da inganta harkar noma a kasa
Ya kara da cewa, rashin zaman lafiya tsakanin makiyaya da sauran abokan zama abu ne wanda yake bukatar zama don a fahimci matsalolin jama’a, tare da girmama juna.
Amma ya ba gwamnati shawara da ta duba bangaren tsaro musamman sojoji,da gwamnati ta tantance wadanda take turawa wajen kwantar da tarzoma don kaucewa fada wa jama’a wanda ba su da hannu a wajen da aka samu barkewar rikici.
Danfulani wanda ya kasance fitaccen dan kasuwa a harkar takin zamani, kuma mai fada a ji a harkar noma ya ce samarwa da makiyaya matsuguni na dindindin, na daya daga cikin hanyoyin da zai kawo karshen rikicin makiyaya da manoma Wanda ya ki ci ya ki cinye wa a kasar nan.
Adamu Danfulani wanda kuma shi ne shugaban kamfanin Hulhulde intanashonal kamfani,ya shawarci gwamnati da ta ba kowanne bangare kulawa ta musamman, da samar da matsuguni ga makiyaya tare da ba su ingantaccen ilimi ga ‘ya’yansu don kawo karshen rikicin
Ya kara da cewa, karanci abincin dabbobi ya sa Fulani makiyaya ke tafiye-tafiye zuwa wurare don samarwa dabbobi abinci
A cewarsa,”noma da kiwo tamkar Danjuma ne da Danjimmai, dukkansu sana’a ce wadda suke da asali, manomi bai iya rayuwa sai da makiyayi, kamar yadda makiyayi ba zai samu jin dadin rayuwa ba sai da manomi domin shi ke samar da abinci”
Ya kara da cewa, kasashen da sukaci gaba kamar kasar Indiya sun samarwa da makiyaya matsuguni na musamma tare da samar musu da kayan more rayuwa kamar, makarantu don koyar da ‘ya’yan makiyaya da Asibiti da sauransu,
Ya ce hakan ya sa makiyaya ke gudanar da sana’ar kiwo ba tare da shiga gonakin manoma don kiwo tare da samarwa da dabbobinsu abinci
A cewarssa a wadannan kasashen,duk makiyayi za ka ga cewa manomi ne don ya rungumi sana’ar kiwo da gudanar da noma a wuri daya
Fitaccen dankasuwa kuma wanda yake shi ma makiyayi ne ya ce yin hakan shi ne zai kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a kasar na.
Shugaban kamfanin Hulhulde Inbestment ya jinjinawa gwamna Malam Nasiru El-rufa’i saboda kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen tabbatar da tsaro ga al’ummar karamar hukumar Birnin Gwari da jihar Kaduna
Ya ce wannan kokari da ya yi ya kawo dauki ga al’umma musamman bangaren Birnin Gwari da Zamfara da suransu shi ne ke alamta shugabanci na adalci da sanin hakkin jama’a.
Don haka, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da ba gwamnatin shugaba Buhari dukkan goyon bayan da ya kamata don ci gaban kasa da samar da dawwamamen zaman lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!