Connect with us

KASUWANCI

Hanyoyin Da Mu Ke Bi Don Bunkasa Harkar Noma A Nijeriya –Farfesa Abubakar

Published

on

Wakilinmu IDRIS UMAR ya samu zantawa da babban Daraktan Sashen Bibiyar Nazarin aikin gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, FARFESA IBRAHIM ABUBAKAR a kan yadda cibiyar ta ke gudanar da ayyukanta a fadin kasa baki daya don cigaban harkar noma da kirkiro sabbin dabaru a kimiyyance, ga yadda zantawarsu ta kasance kamar haka.

Da farko za mu so ka gabatar da kanka ga masu sauraro
Suna na Farfesa Ibrahim Usman Abubakar, kuma ni ne Shugaba aikin gona a karkashin jami’ar Ahmadu Bello dake nan Zariya. Sannan uwa ga duk wata cibiya da ke fadin wannan kasar tamu Nijeriya da Afrika baki daya.

Farfesa ko za ka gaya mana me wannan cibiya taku take gudanarwa a bangaren aikin noma?
Kwarai kuwa wannan cibiya ta kunshi abubuwa da yawan gaske da suka shafi aikin gona, Ka ga na farko wannan cibiya ta na gudanar da bincike kuma tana ilimantarwa a dukkan abinda ya shafi noma da abin da ake nomawa har da masu noman, daga kan tsirrai har bangaren dabbobi kusan shekara 100 da suka gabata.
Ka ga bangaren tsirrai mun shahara a kan abubuwa guda tara da suka hada da Auduga, da gyada da dawa, da wake, sai masara, da shinkafa, da filawar – bi – rana, da Rake, da Abarba, da Ayaba, da sauransu bincikenmu ya yi nisa a kansu. Don yanzu haka mun kirkiro sabbin fasahar tsirrai kusan kala 50, daga ciki akwai gyada, yanzu haka muna da kala 26. Wake kuwa muna da a kalla kala 17, ita kuwa Auduga muna da 14, duk wanda ka ji na lissafa a cikinsu to in ka je kasashen waje za ka ga suna alfahari da su bisa ga yadda wannan cibiya take tsayawa da kyau wajen gudanar da bincikenta a kowanne bangare. Don haka muna gode wa Allah da ya sa muka zama zakaran gwajin dafi a duniya baki daya.

To ko Farfesa zai fada mana ko ta yaya manoma ke amfana da irin wadannan bincike musamman manoma da suke karkara?
Kwarai kuwa akwai hanyoyi da yawan gaske da manoman kasarmu manya da kanana suke amfana da binciken da wannan cibiya ta ke gudanarwa. Na farko a nan jami’ar muna da wata cibiya da ake kira NEARLS aikinta shi ne shelanta sabbin dabarun noma a kasa baki daya, don haka duk lokacin da wannan cibiya ta kammala wani nazari a kan wani cigaba da ta samu, to sai ta mika shi ga wannan cibiya ita kuma sai ta shelanta shi ga masana harkar noma, su kuma su dauke shi ga malaman gona daga nan su kuma sai su kai shi ga manoma don gwaji.

Ta yaya ake ganin samfuri kafin Manoma su fara amfani da shi don gujewa matsalar da ka iya biyo baya?
A kwai hanya guda daya, hanyar kuwa ita ce, da an gama nazari a kan samfuri, to akan tura masana zuwa ga manoma don nuna masu banbancin na da da na yanzu, misali sai a je gonarsu a sami wani waje sai a shuka irin da suke amfani da shi a waje daya, sai kuma a sami waje a shuka sabon samfuri da aka zo masu da shi, sai a cigaba da rainon su har zuwa girbi to ta nan ne ake fahimtar mai kyau da mara kyau.

Wace hanya kuka bi don samun wadannan nasarorin da ake alfahari da ku a wasu kasashen ketare?
To gaskiya a iya sanina abubuwan da suke sa har muke samun wasu nasarorin har ake yaba binciken mu, bai wuce guda biyu zuwa uku ba. Na farko muna da kwararrun masana a dukkan bangarorin da muka shahara a kai, na biyu wannan cibiya tana da dakunan gwaje-gwaje na musamman, sai na uku duk wanda ka gani a wannan cibiya to mai kishin cigaban kasarsa ne don haka gwamnatin kasarmu ke sanya idanu a kan lamarorin da suka shafi wannan cibiyar da manufofinta a kowane lokaci.

To a yanzu wane kira za ka yi wa Manoma?
Gaskiya kirana ga Manoma shi ne, su gane cewa ita wannan cibiya ta IAR an kirkireta ne saboda Manoma, don haka duk manomin da ya samu wata matsala to ya garzayo ya fada a daidaiku ko a kungiyance don daukar mataki, saboda da yawan lokaci Manoma kan samu matsala da gonakinsu sai su yi shiru sai ta gama lalata amfanin gona mai yawa ta fada jihohi sannan a sanar da mu wanda hakan bai dace ba.
Kuma ko da an sami iri daga wajen mu daga baya aka ga wata matsala to kada a yi nauyin baki a sanar da mu a kan lokaci don daukar matakin gaggawa misali a lokacin baya mun fitar da wani irin dawa mai auki wanda Manoman karkara sun saya sun yi amfani da shi yana da auki sosai fiye da wanda suke shukawa a gonakinsu, amma sai daga baya suka daina saye bisa ga wani da suka hango daga irin namu, amma babu wanda ya zo ya sanar da mu abinda suka gano.
Sai da muka tambaye su shin ko lafiya muka ga ba kwa sayen wancan irin dawar? Sai suka ce wannan irin dawar yana da auki, amma ba ya dumamen tuwo mu kuma ba mu yi sai da dumamen tuwo. To ka ga da sun fada tun da sauri da an fara nazari a kai saboda sun ce da an yi tuwo da shi ya kwana sai ya wargaje a cikin ruwan dumame, don haka muna kira ga Manoma da su matso kusa a ci albarkacin juna, musamman ma da ya ke yanzu wannan cibiya ta yi nisa a kera mashinan amfanin gona na zamani kamar injin casar masara da na shinkafa da na busar da tumaturi da matsar gyada don dai kawai a saukakawa Manomi.

Farfesa wane kalubale wannan cibiya take fuskanta a halin yanzu?
Kalubale da wannan cibiya ta ke fuskanta a halin yanzu bai wuce na kudi, domin duniya yanzu an cigaba a fannin bincike, don haka muna da dakunan bincike masu yawa wanda daga cikin na’urar da muke amfani da su wasu sun tsufa da bukatar a sami na zamani don a zamanin da muke ciki a yanzu duk rana ana samun cigaban zamani, don haka in ka yi wasa sai a barka a baya.
Na biyu duk gine-ginen da muke amfani da su in ka duba duk sun tsufa don wani ginin ya shekara 50 da gina shi, don haka da bukatar sabbin gine-gine, in gwamnati ta yi mana haka, to gaskiya za mu ji dadi. Don haka muna kira ga wannan gwamnati mai kishin harkar noma da ta tallafawa dakunan binciken aikin gona don samo sabbin dubarun aikin gona.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!