Saraki Ya Kaddamar Da Kamfanin Takin Zamani Da Za A Gina A Kan Dala Biliyan 3.2 A Jihar Ribas — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Saraki Ya Kaddamar Da Kamfanin Takin Zamani Da Za A Gina A Kan Dala Biliyan 3.2 A Jihar Ribas

Published

on


Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya kaddamar da ginin kanfanin takin zamani na “Indorama Eleme Fertiliser and Chemicals Limited” a jihar Ribas.
Shugaban majalisar ya kuma amince da ci gaba da shugabancin gwamna Wike a karo na biyu inda ya ce, zai kasance a ofis a shekarar 2021 lokacin da kanfanin zai fara aiki. Da yake gudanar da bikin kaddamarwar, saraki ya ce, Dala Biliyan 3.2 da aka zuba jarinsa a jihar Ribas wani abu ne dake nuni da cewa, jihar Ribas na haba haba da masu zuba jari daga fadin duniyar nan.
Ya kara da cewa, “Ina taya al’ummar jihar Ribas murnar samar da yanayin da za a zuba irin wanna jarin ina kuma bukatar sauran jihohi su dauki wannna salon a jihar Ribas don samun cikakken ci gaba.”
Shugaban majalisar dattijan ya kuma lura da cewa, samar da takin urea a jihar Ribas, takin da mafiya yawan manonan jihohin Arewa ke amfani dasu zai yi matukar tasiri wajen hada kan kasa.
“Manoma ke amfani da takin Urea, musamman manoman da suka fito daga Arewacin kasar nan, wannna yana kara nuna mana bukatar samun hadin kai a tsakanin ‘yan kasa.
Dole mu karfafa juna ba tare da banbancin siyasa ko addini ba. in har babu zaman lafiya ba za a taba samun takin urea ba. Dukkanmu dake a Nijeriya dole mu hada hannun don ci gaban Nijeriya.” Inji shi.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya ce, kanfanin Indorama ya yi aiyyuka masu inganci a jihar ta hanyar zuba jari masu amfani, Wike ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar zata yi kokarin ganin an samar da zaman lafiya a jihar tare da samar da yanayin da za a kuma kare dukiyar kanfanin na Indorama.
“Mun anfana da romon daya fito daga kanfanin “Indorama Eleme Fertiliser and Petrochemicals Limited.” Muna matukar farin ciki da jin dadi ga shuwagabannin kanfanin,” inji shi.
Gwamnan ya yi matukar mamakin maganan da wasu ke yin a cewa, babu yanayi kyakyawa na zuba jari a jihar, amma gashi an samu zuba jari daga kasashen waje har na Dala Biliyan 3.2.
“Ina matukar alfaharin cewa, a cikin lokacin ina gwamna a Ribas ne na kaddamar da bangaren farko dana biyu na kanfanin samar da takin zaman, in har zamu iya samun zuba jari na dala Biliyan 3.2 a jihar Ribas ta yaya za a ce babu kwanciyar hankalin da za a iya zuba jari a jihar Ribas, lallai a kwai zaman lafiya a jihar Ribas da Nijerya baki daya.” Inji shi.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!