Connect with us

WASANNI

Manchester City Za Ta Gwada Lafiyar Mahrez A Wannan Satin

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta amince ta biya fan miliyan 60 domin siyan dan wasan gaba na Leicester City, Riyad Mahrez, mai shekara 27, kuma ana sa ran za a gwada lafiyar dan kwallon na Algeria nan da sa’a 48, kamar yadda jaridu suka rawaito daga kasar Ingila.

Manchester City dai tad ade tana neman Mahrez wanda ya taimakawa Leicester City ta alshe kofin firimiya a shekaru biyu da suka gabata kuma ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon firimiya na shekarar.

A watan Janairun daya gabata dai kungiyar Leicester City ta kusa siyarwa da City dan wasan sai dai daga baya kungiyar taki amincewa da tayin da Manchester City tayi wanda hakan yasa daga karshe dan wasan yayi yajin aikin fita daukar horo.

An bayyana cewa Leceister City tana son dan wasa Ahmad Musa yam aye gurbin na Mahrez idan yabar kungiyar bayan da tauraruwar dan wasan ta haska a gasar cin kofin duniya wanda a a yanzu haka yake gudana a kasar Rasha.

Sai dai Mahrez yana tsoron zama a Benci a Manchester City idan yakoma sakamakon kungiyar tanada kwararrun ‘yan wasan gaba sai dai ana zaton kungiyar za ta iya siyar da dan wasa Bernardo Silba dan kasar Portugal wanda yakoma kungiyar daga Monaco.

Manchester City dai tana shirin siyan dan wasa Jorginho daga kungiyar Napoli domin kara karfin ‘yan wasanta na tsakiya bayan da dan wasan ya haskaka a kakar wasan data gabata.

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar, Pep Guardiola dai ya bayyana cewa abune mai wahala ya iya sake lashe kofin firimiya sai dai ya ce zai siyi wasu ‘yan wasan domin ganin ko zai iya lashewa a karo na biyu.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!