Dole Sai Ingila Ta Kula Da Motsin Modric, Cewar Machael Owen — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Dole Sai Ingila Ta Kula Da Motsin Modric, Cewar Machael Owen

Published

on


Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Manchester United, Machael Owen, ya bayyana cewa dole sai ‘yan wasan tsakiyar kasar sun kula da motsin dan wasa Modric idan har suna son su doke kasar Crotia a wasan da zasu fafata a yau.

A yau Laraaba ne  kasashen Ingila da Croatia za su fafata da juna a matakin wasan dab da na karshe na gasar ta cin kofin duniyar da ake fafatawa  a yanzu haka a kasar Rasha.

Tuni masharhanta suka fara tsokaci kan wannan haduwa, in da manazarta kan kwallon kafa daga Birtaniya ke cewa, tilas ne Ingila ta takura dan wasan tsakiya na Croatia wato, Luka Modric matukar ta na son kaiwa wasan karshe a gasar.

Wani marubucin labarin wasanni a Birtaniya ya tunatar da jama’a irin barazanar da Modric ke da ita, in da ya ce, yana cikin tawagar da ta casa Ingila 2-0 a wani wasa da suka buga a shekarar 2006 a babban birnin kasar Zagreb, a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin kasashen Turai.

Kazalika ana ganin kwarewar Modric wajen amfani da dukkanin kafafunsa biyu, ka iya zama karin barazana ga tawagar Ingila a wasan na ranar Laraba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!