Mata ‘Yan Nijeriya Sun Fara Kokawa Akan Halin Da Suke Ciki A Kasar Saudiya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Mata ‘Yan Nijeriya Sun Fara Kokawa Akan Halin Da Suke Ciki A Kasar Saudiya

Published

on


Ganin yadda mata ‘yan Nijeriya suke gogoriyon zuwa kasar Saudiya domin neman ayyukan yi wanda da damar su sun yiwa tafiya saudiyar gurguwan fahimtar. A halin dai da ake ciki wasu daga cikin matan da suka samu damar tsallakawar sun fara kokawa akan kunci da samuwar da suke ciki.

Hadiza wata ‘Yar jihar Kaduna ta nuna nadamarta wannan balaguron, inda ta bayyana ma wakilin mu cewar halin da mata ‘yan Nijeriya ke ciki a kasar saudiya abin tausayi ne, ni kamfani ta kawo ni kasar dan yin aiki, mu ba fita mu ke yi ba. Ta cigaba da cewar muddin za ki rike kan ki, ki tsare mutuncin ki lallai za ki ga takura sosai, domin albashin da ake biya idan ka lissafa ba wani abin kirki ba ne.

Matashiyar tace yanzu shekara ta daya da watanni amma tsakani da Allah ina nadamar wannan tafiyar, domin ina da ‘yaya, ina da ‘yan uwa kuma kudin da ake biya bai iya biya maka bukatar ka ta yau da kullun, don haka ya kamata ina jawo hankalin gwamnatin tarayya akan ta sanya idanu sosai akan yadda ake safarar mata da sunansa aiki, domin wasu kamfanonin bai kamata a ce an ba ta damar yin ayyuka ba a wasu kasashen ba.

Zargin da ake wa wasu mata ‘yan Nijeriya da ke nan saudiya cewar suna karuwanci da zubar da kimarsu gaskiya ne, domin da daman su wahala ce ke jefa su a wannan halin. Gaskiya hukumomin saudiya suna kokarin su akan tsaftace kasar su amma kam mutanen mu suna babalarsu, domin samun biyan bukata.

Hajiya Zulai wata asalin jihar Fulato ta bayyana cewar yaudararta aka yi domin an nuna ma ta cewar aiki za tayi idan an tafi kasar saudiya amma abinda ta gani ko kare ba zai ci shi ba, kan hakan ne yasa ta bijire tayi duk abinda ta ga za ta iya yasa ba ta cika watanni uku ba ta samu nasarar dawowa gida. Tace har haukar karya sai da na kirkira kan haka yasa jami’an da suka samu nasarar tafiya da mu suka yanke shawarar dawo wa da ni gida Nijeriya inda aka watsar da ni a jihar Kano hakan yasa na samu nasarar dawo wa gida Jos.

Zulai tace lallai rayuwar mata ‘yan Afirika da ake safarar su zuwa saudiya na fuskantar kaskanci a hannun jami’an da ke tafiya da su domin da daman matan da ta iske a can indai ba aure ya kai su ko suna da mazan aure ba lallai akwai yiwuwar su fada cikin miyagun halaye.

Tace ita kam da barin gida Nijeriya da sunan neman kudi a wata kasar laraba wa sai dai aikin Ibada, tace na taba zuwa aikin hajji ban haka neman kudi a wata kasar ta ke ba shi ya kai ni a wannan halin kuncin da na samu kaina, ba albashi wadatacce, ba kyakkyawar kulawa domin ko aikin aka kai a gidan larabawa daukar ka su ke yi tamkar bawa mai bauta, kuma inda muke kullun a boye mu ke shi yasa ake mana abinda aka ga dama.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!