Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Bauchi Ta Dauki Nauyin Kiristoci 10 Don Halartar Bukin Easter A Isra’ila

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta dauki nauyin manyan limaman addinin kirista guda goma domin su halarci Urshalima a bikin Ista ‘Easter’ domin yi wa kasa addu’ar zaman lafiya da hadin kai a wannan shekarar.

Daukan nauyin ya biyo ta hanun hukumar jin dadin Maniyyata aikin hajjin Kiristoci reshen jihar Bauchi (BCPWB), inda aka nemi su yi wa kasa addu’a na zaman lafiya da ci gaba.

Babban sakataren hukumar jin dadin maniyyata ziyarar muhallin bautan kiristoci reshen jihar Bauchi Mr. Daniel Shawulu shine ya shaida hakan a hirarsa da manema labaru a ranar Talata, a lokacin da suke aikin tantance maniyyatan da za su sauki faralin daga Bauchi.

Ya ce, “A yau, muna kan tantance manyan Limamai goma da gwamnatin jihar Bauchi ta dauki nauyinsu domin ziyarar kasa mai tsarki don su yi wa kasar Nijeriya addu’a na ci gaba da wanzuwar zaman lafiya,” A cewarshi.

Ya ce, “Fastoci guda goma daga jihar nan su ne je Hajji a kasar Israel a ranar 14 ga watan Yulin 2018,” In ji shi.

Ya bayyana cewar aikin hajjin wanda ya kamata a gudanar a watan Afrilun 2018 ya gamu da jinkirin ne a sakamakon wasu dalilai da suka sha karfi.

Mista Shawulu ya shaida cewar limaman kiristan za su shirya babban taron yin addu’a a kasar nan a lokacin da suka isa Israila a lokacin da suke gudanar da aiyukansu na hajjin domin yi wa kasa addu’a da ci gaban zaman lafiyar Nijeriya.

Ya bayyana cewar wannan shirin irinsa ne na farko a tarihin jihar Bauchi inda ya bayyana hakan a matsayin gagarumar ci gaba.

Mista Shawulu, wanda ya wakilcin Daraktan mulki da albarkatu na hukumar, Mr Nathaniel Mua’ azu, ya jinjina wa gwamnatin jihar Bauchi a bisa daukan nauyin limaman kiristan zuwa wannan  kasar don gudanar da ibadarsu.

Ya kuma shaida cewar an duba gayar cancantar manyan limaman da aka dauki nauyinsu domin su wakilci jihar Bauchi wajen gudanar da wannan gagarumar aikin.

Sakataren ya bayyana cewar akwai tawagar likitoci da malaman jinya kan lafiya da ake tantancesu domin ziyarar, ya kuma yi kira ga matafiyan da su kasance masu gudanar da abaubuwan da za su kawo ci gaba wa kasa.

A na dai sa ran za a tashi daga jihar Bauchi zuwa kasar Israila din ne a ranar Asabar 14 ga watan Yulin 2018 da ke tafe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!