Connect with us

LABARAI

NLC Ta Garkame Ofishin MTN A Jigawa

Published

on

A Jiya ne kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Jigawa ta jagoranci mambobinta yadda suka garkame ofishin MTN dake jihar.

Shugaban kungiyar ta NLC Kwamred Usman Ya’u Dutse ne ya jagoranci tawagar da safiyar ranar ta Laraba a babban birnin jihar dake Dutse.

Kwamred Ya’u ya bayyana cewa, wannan yunkuri ya biyo bayan umarnin da uwar kungiyar ta kasa ta baiwa ‘ya’yanta na rufe duk wani ofishin kamfanin MTN dake wannan kasa har sai su kula da hakkunan ma’aikatansu.

Ya ce, “babu ko shakka mun‎ dauki wannan mataki ne domin kwatowa ma’ikatan wannan kungiyar hakkunansu, sakamakon gazawa da kamfanin ya yi a wannan kasa, yadda a sauran kasashe kuwa yake biyansu cikakkun hakkunansu”.

LEADERSHIP A Yau ta gano cewa, a daidai lokacin da manajan kamfanin a jihar ya sami labarin zuwan wannan tawaga na nan tafe, tuni ya bada umarnin rufe ofishin tare da ranta a na kare.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!