Shugabannin Afirka Za Su Yaki Tsatsauran Ra’ayi A Kasashensu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASASHEN WAJE

Shugabannin Afirka Za Su Yaki Tsatsauran Ra’ayi A Kasashensu

Published

on


Shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka da suka yi taro a Mauritia a makon da ya gabata, sun yi alkawarin kara kaimi wajen yakar kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a nahiyar, musamma ma a yankin Sahel.

Wannan alkawari, na zuwa ne bayan wasu hare-hare da kungiyoyin masu ikrarin jihadi suka kai a wasu kasashen yankin Sahel, ciki har da wani hari da ya halaka sojojin Jamhuriyar Nijar 10 a kudu maso gabashin kasar, da wani hari a kan hedkwatar rundunar hadin gwiwar kasashe biyar da ke yaki da masu ikrarin jihadi ta G5 Sahel a Sebare da kuma wasu hare-hare biyu da suka auku a Mali.

Sai dai wasu kwararru sun yi gargadin cewa, da wuya kungiyar ta AU ta iya kara assasa karfi rundunar hadin gwiwar ta G- Sahel, wacce aka kafa a bara.

A wani labari mai nasaba da wannan, wasu mata masu rike da manyan mukamai, sun yi kiran neman karin tallafi daga kasashen duniya, domin taimakawa mata da ‘yan mata su tsira daga matsalolin rikice-rikice da ayyukan ta’addanci da rashin ci gaba da da kasashen yankin Sahel ke fama da su.

Ministar harkokin wajen Sweden, da mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, da wakiliya ta musamman kan harkokin mata, zaman lafiya da tsaro ta kungiyar Tarayyar Afirka ne suka yi wannan kira, bayan da suka kammala wata ziyarar hadin-gwiwa da suka kai Jamhuriyar Nijar da Chadi, inda suka hadu da mata daga bangarorin al’uma daban-daban.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!