Connect with us

SHARHI

Bai Dace A Shafa Wa Manufar ‘Canza Fasahohi Da Kasuwanni’ Kashin Kaji Ba

Published

on

A kwanakin baya bayan nan, rikicin ciniki na kara tsanancewa tsakanin bangarorin Sin da Amurka. A lokacin da ake samun wannan rikici, wani abu da ya kamata a lura da shi, shi ne wata manufar da kasar Sin ta taba gabatarwa, yayin da take kokarin neman janyo jari daga kasashen waje, wato manufar “Canza fasahohi da kasuwanni”.
Yanzu haka wannan manufa ta zama wani bangare da kasar Amurka ta fi yin suka a kai, kana tana kokarin shafawa manufar kashin kaji. To ko mene ne ma’anar wannan manufa?
Da farko, “Canza fasahohi da kasuwanni”, wata manufa ce ta bai daya da kasashe daban daban su kan dauka, ta neman hadin gwiwa da wasu kasashe a fannonin tattalin arziki da fasahohi.
Yadda aka yi amfani da jari, da fasahohi masu ci gaba na samar da kayayyaki, da na kula da ma’aikata na kasashen waje, da kokarin shiga tsare-tsaren kasa da kasa na samar da kaya, da sayar da kaya, gami da samar da hidima, don kara saurin samun ci gaba, wani mataki ne da kasashe da dama, musamman ma kasashe masu tasowa, suka saba da dauka, a mataki na farko na aikinsu na bude kofar kasuwannin gida. Game da manyan kamfanoni masu mallakar fasahohi, yadda ake nuna saukin kai da yarda da karin mutane yin amfani da fasahohinsu, wata hanya ce da dole a bi, don sanya fasahohin su haifar da mafi yawan riba, da mayar da moriya ga wadanda suka yi kokarin kirkiro sabbin fasahohin. Saboda haka, manufar “Canza fasahohi da kasuwanni” tana da amfani ga dukkan bangarorin 2, wato mai samar da fasahohi, da mai yin amfani da fasahohi.
A nata bangare, kasar Amurka ta dora cikakken muhimmanci kan hadin gwiwarta da kasashe daban daban a fannin kimiyya da fasaha. Ban da daukar mataki na koyon fasahohi masu inganci na sauran kasashe, kasar tana mai da hankali kan matakin shigo da kwararru daga kasashen waje, don kara kwarewar kasar a fannin kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da matsayinta na kan gaba a fannin mallakar fasahohi masu ci gaba. Kowa ya sani, bayan babban Yakin Duniya na 2, kasar Amurka ta karbi kwararru da yawa daga nahiyar Turai. Daga bisani, ta dade tana kokarin janyo hankalin masu ilimin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, domin su je aiki a kasar Amurka.
Duk da wannan manufarta, kasar Amurka ta yi suka kan matakin da kasar Sin ta dauka na komowar kwararru daga ketare, da gayyato dalibai Sinawa da suka yi karatu a kasashen waje domin su koma gida. Za a iya ganin cewa, sukar da kasar Amurka ta yi ba ta da hujja balle ma wani dalili. Yadda kasar Amurka ta zabi kasar Sin ita kadai, don yi mata suka kan manufarta ta “Canza fasahohi da kasuwanni”, tamkar raba kafa ne dangane da ra’ayin hadin gwiwa a fannin fasahohi.
Na biyu, Sin ta bi ka’idojin kasa da kasa yayin da take “canza fasahohi da kasuwanni”.
Tabbatar da ikon mallakar ilmi shi ne tabbacin yin kirkire-kirkire, kuma kasa da kasa suna dora muhimmanci gare shi. Sin ta shigar da fasahohin da ake bukata wajen bunkasa tattalin arziki ta hanyar yin cinikin ikon mallakar ilmi. Tun daga shekarar 2001, yawan kudin da Sin ta kashe a wannan fanni yana karuwa da kashi 17 cikin dari a ko wace shekara. Ya zuwa shekarar 2017, yawansu ya kai dala biliyan 28.6. Sin tana da babbar kasuwa da kuma samun albarkatu a fannoni daban daban, tana kuma kara bude kofa ga kasashen waje, da tabbatar da moriyar kamfanonin kasashen waje da suka zuba jari a kasar.
A sakamakon samun karuwar jarin da kamfanonin kasashen waje suka zuba a kasar Sin, kasar Sin ta zama kasa mai tasowa mafi jawo jarin kasashen waje a duniya a cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata. Yayin da ake samun bunkasuwar fasahohi da sana’o’i, Sin ta samu moriya da dama daga hadin gwiwar fasahohi da tattalin arziki a tsakaninta da Amurka, don haka Sin ta nuna girmamawa game da wannan. Haka zalika kuma, ya kamata kasar Amurka ta gano kokarin da kasar Sin ta yi wajen bin ka’idodin kasa da kasa, da tabbatar da ikon mallakar ilmi, da kuma moriyar da za a samu ta hanyar samun fasahohi daga kasuwanni.
Wasu kamfanonin kasar Amurka dake kasashen waje sun bayyana cewa, bunkasuwar kasuwar kasar Sin ta taimake su wajen tinkarar rikicin hada-hadar kudin da ya faru a shekarar 2008.
Na uku, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan manufar bude kofa ga waje da kuma yin kirkire-kirkire da sauran kasashe.
Bude kofarta ga ketare babbar manufa ce da kasar Sin take tsayawa a kai ba tare da tangarda ba, ko za ta sha wahaloli iri iri ma, ba za ta canja wannan niyya ba. Bisa alkawuran da ta dauka a lokacin da aka shigar da ita cikin kungiyar WTO, da ka’idojin kungiyar, kasar Sin ta riga ta gyara ka’idoji da dokoki fiye da 2300, har ma ta yi watsi da takardun gwamnati dubu daruruwa. A watan Janairun shekarar 2005, bisa alkawarin da ta yi wa WTO, ta soke dukkan matakai da suka sabawa na karbar harajin kwastam, ciki har da amincewarta ga shigowar kayayyaki daga ketare ba tare da neman samun izininta ba. Ya zuwa shekarar 2010, ta cika dukkan alkawuran rage harajin kwastam da take karba daga kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, ta yadda ya zuwa yanzu harajin kwastam da take karba daga wasu muhimman kayayyakin da ake shigowa da su ya yi kasa da na kasashe masu arziki.
A tsakanin shekarar 2001 da ta 2017, yawan kayayyakin da kasar Sin take shigowa da su daga ketare ya karu da 13.5% a ko wace shekara. Sin ta zama kasa mafi girma ta biyu wajen shigo da kayayyaki daga ketare. A lokacin da ake yunkurin nuna adawa da bunkasar tattalin arzikin duk duniya bai daya, ba ma kawai kasar Sin ta yi kokarin kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban ba tare da shinge ba ne, a’a ta kuma tsayawa tsayin daka kan matayinta na kara bude kofarta ga ketare. Alal misali, ta dauki matakin rage harajin kwastam sosai, kuma ta shirya bikin baje koli na kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare, domin kokarin shigowar karin kayayyaki. Bisa sabbin matakan sa ido kan yadda baki ’yan kasuwa suke zuba jari a kasar Sin, yawan fannonin da ba su iya zuba jari a cikin su ya ragu zuwa 48 daga 63. Kuma kasar ta riga ta sassanta sharudan zuba jarin waje a fannonin hada hadar kudi, da kayayyakin yau da kullum, da aikin gona, da motoci, da jiragen ruwa da na sama, da layukan dogo, da kuma tsarin turakun tattara wutar lantarki. Sakamakon haka, yanzu ana iya gane yadda kasar Sin take kokarin daga matsayinta na bude kofarta a bayyane kwarai.
Manufar yin kirkire-kirkire tare da sauran kasashe ba ma kawai zai iya tabbatar da samun sabuwar fasaha ba ne, har ma zai kara yiyuwar hadin kan kasa da kasa a wannan fanni. Lamarin da zai ba da muhimmiyar ma’ana ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da ma ci gaban fasahohin duniya. A cikin shekaru 40 da suka gabata, bayan da kasar Sin ta bude kofa ga waje, ta ci gajiya sosai daga tsarin kirkire-kirkire tare da sauran kasashe, kana tana da fahimta sosai a kan batun.
Ko da yake kasar Sin ta samu ingantuwar kirkire-kirkire bisa karfin kanta yanzu, amma ba ta son canja wannan aniyar ta ta farko. Nan gaba, ‘yan Adam za su fuskanci sarkakiyar muhallin zamansu, da yawan kalubaloli, fasahohin kimiyya kuwa muhimman hanyoyi ne na warware matsalolin, lamarin da yake kara nuna muhimmancin hadin kan kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha. Sabo da haka, ko da sauyawar yanayin duniya, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa yin kirkire-kirkire tare da sauran kasashe bisa tushen kiyaye hakkin mallakar ilmi, kuma tana maraba da kasa da kasa da su hada gwiwarsu tare da Sin, ta hanyoyi daban daban.

(Sanusi Chen, Kande Gao, Bello Wang, Zainab Zhang, dukkansu ma’aikatan sashen Hausa na CRI)
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!