Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Gurfanar Da Uwa Da Danta Da Laifin Kai Hari Ga Dan Haya Da Wuka

Published

on

An gurfanar da uwa da danta a Kotun yanki dake jihar Legas domin zargin su da yin amfani da wu ka wajen ji wa dan haya ciwo lokacin da suke fa da. Ekaete John dan shekara 55 dake sana’ar tireda shi kuma Isaac Godwin dan shekara 20 daya ke aiki a kamfani, suna zaune a gida mai namba 27 da ke layin Segun Adetiba a unguwar Alakuko da ke jihar Legas, kuma dukkan su biyun ana zarginsu da kai harin. Wani dan sanda mai suna Bictor Eruada ya gaya wa Kotu cewa wan danda ake tuhuma sun aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Yuli a gidan su. Ya kara da cewa fa dan ya auku ne sakamakon cacan baki da ya gudana a tsakaninsu da Mr Fabian Owotikwu. “Ana cikin haka sai Jonh da yaranta suka dauko wu ka domin su yi amfani da ita, su yanke wa Owotikwu al’auransa amma sun ji masa ciwo”. Inji Eruada.
Eruada ya ce Owotikwu ya ji mummunar rauni sakamakon farmakin da suka kai masa. Laifin ya sa bama sashi na 173 da 411 na manyan laifukan jihar Legas na shekara 2015. Sashi na 173 ya umurta cewa duk wanda aka samu da irin wannan laifin to zai zaman kurkuku na tsawan shekara uku yayin da sashe na 411 ya bada zaman shekara biyu.
Wa danda ake zargi sun musanta al’amarin. Mai shari’a Cif M. I. Dan-Oni ya bayar da belin wa danda ake zargi a kan ku di naira 50,000. Ta ce su kawo takar dan shaida na biyan haraji na tsawan shekaru biyu duk yana cikin shara di na bilin. Al kali ya daga zaman sauraran shari’an har sai 20 ga watan Ogasta.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: