Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Dan Shekara 25 Ya Rataye Kansa A Ondo

Published

on

Wani saurayi mai suna Ayo Paul ya rataye kansa a dakinshi dake Aule cikin karamar hukumar Akure ta Jihar Ondo. Majiyarmu ta bayyana mana cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar, inda al’amarin ya gigita makwabcin mamacin tare da bayyana shi amatsayin mutumin kirki.
Har yanzu ba a san dalilin da ya sa matashin mai shekaru 25 ya rataye kansa ba, amma wata majiya ta bayyana cewa maigidan su magayin ya je ya bude kofar Paul lokacin da baigan shi ba wajen gudanar da tsaftace muhalli na ranar Asabar wanda suka saba yi kowani karshan wata. Majiyan ta kara da cewa “ babu wanda ya san dalilin da ya sa Ayo ya rataye kansa domin kuwa shi mutumin kirki ne bai da wani matsa da kowa.
“ A yayin da ba a ga duriyar saba domin gudanar da tsaftace mahalli wanda yake gudana kowani wata sai maigidan su ya fara neman sa har zuwa dakinsa, lokacin da ya bude kofarsa sai ya ganshi rataye, sai maigidan ya sanar wa mutane abin da ke faruwa.”
Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Femi Joseph ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce, rundunar ‘yan sandar suna gudanar da bincike. Ya kara da cewa “ bamu san dalilin da ya sa ya dauki wannan mataki ba amma muna gudanar da bincike a kan al’amarin.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: