Bauchi Ta Fara Aiwatar Da Kudirorin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya Kan Mata Da Zaman Lafiya, Inji Matar Gwamna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Bauchi Ta Fara Aiwatar Da Kudirorin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya Kan Mata Da Zaman Lafiya, Inji Matar Gwamna

Published

on


Uwargidan gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar ta bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za a fara aiwatar da kudirorin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya a kan mata da zaman lafiya da tsaro masu lambobi 1325 a jihar Bauchi

Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar ta bayyana kwarin gwiwar ta da cewar, aiwatar da kudirorin za ta taimaka wajen inganta rayuwar mata a jihar.

Kudirorin masu lambobi 1325 wadanda aka samar da su akan mata, zaman lafiya da tsaro, a shekara ta 2000 ce kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ta bijiro dasu domin jaddada muhimmancin daidaiton jinsi domin bada dama, a dama da mata a cikin dukkanin fannoni na samar da zaman lafiya, aikin wanzar da zaman, magance rigingimu da kuma gudanar da shugabanci.

Hadiza Abubakar ta bayyana haka ne a yayin wani taron bita na yini daya wanda ofishin uwargidan gwamna ta shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar bunkasa harkokin mata da yara kanana akan batun aiwatar da kudirorin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya masu lambobi 1325 masu manufar inganta rayuwar mata, da tsaro, wanda ya gudana a gidan gwamnati dake Bauchi a kwanakin baya.

A cewarta, “Aiwatar da shirin ‘Action Plan’ na kasa da kudirorin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya zama wajibi saboda shigo da mata cikin sha’anin karfafa zaman lafiya da tsaro. Hakan wata hujjace da take nuna yadda rigingimu suka yin tasiri akan mata fiye da maza. Mata da yara su suke shiga cikin tasku ayayin da rigingimu suke sarke.

“Kullum burina shi ne ganin cewar, rayuwar mata ta inganta ta hanyar ganin kan iyali ya hadu ta yadda za a kawo karshen halin kunci da mata sukw ciki”.

Ta ce; “Nijeriya ta zo ta farko a shekara ta 2013 da ta aiwatar da shirin ‘Action Plan’ na kasa, da kuma kudirorin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya masu lambobi 1325, yayin da aka sake kaddamar da shirin ‘Action Plan’ na kasa a shekarar da ta gabata da nufin cike wasu gibi da ake dasu”.

“Ofishina ya kulla kawance da ma’aikatar bunkasa harkokin mata da kananan yara domin aiwatar da kudirorin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a mataki na jiha. Manufar wannan taron bita ita ce hada kan masu ruwa da tsaki wuri guda da zummar gudanar da aiki tare ta wajen hada karfi da karfe domin aiwatar da kudirorin a mataki na jiha. Kawo yanzu ina tsammani jihohi shida ne wadanda suka kunshi Bayelsa, Borno, Delta, Kaduna, Kano da Yobe suke aiwatar da shirin ‘Action Plan’ na kasa a Nijeriya”. A cewar matar gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza

Tun da farko cikin jawabinta, kwamishinya mai lura da ma’aikatar bunkasa harkokin mata da kananan yara ta jihar Bauchi, Hajiya Rukayya Muhammad Kewa ta baiwa taron jama’ar tabbacin cewar, gwamnati mai ci tana aiki tukuru domin tabbatar da inganta tsaro da karfafa ‘ya’ya mata ta yadda za su shiga a dama dasu a sha’anin bunkasa zaman lafiya.

Ta kuma bukaci mahalarta taron bitar, dasu jajirce a yayin taron bitar ta yadda za a samar da tsarin da zai taimaka wajen aiwatar da kudirorin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya masu lambobi 1325 a jihar ta Bauchi.

 

 

 

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai