Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Hatsarin Kwalekwale Ya Ci Rayukan Yara Biyu A Jihar Ribas

Published

on

Kwanaki goma kenan da aka samu wani hatsarin kwalekwale a karamar hukumar Degema dake Jihar Ribas, inda ya ci rayukan wandan su yara biyu a cikin fasinjoji guda 25 lokacin da kwalekwalen ya kife ranar Lahadi. Majiyarmu ta ce, yaran da suka rasa ransu su ne Detiny Amamima da kuma Ngowari Amamima dukkan su maza ne amma ba a bayyana kimanin shekarunsu ba, yayin da sauran fasinjoji guda 22 suka tsira. Da kamanin karfe biyu ne, kwalekwalen ya taso daga wani tsibirin da ake kira Marine Base cikin Jihar Port Harcort zai nufi karamar hukumar Okrika inda a nan ne lamarin ya auku. An bayyana cewa yaran da suka mutu dukka su ‘yan’uwan juna ne.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa, ‘yan sandar tsabirin Marine sun taba kama matukin kwalekwalan sanadiyya wani hatsari da ya taba faruwa a sati biyu da suka gabata.

“ Wannan al’amarin ya faru ne ranar Lahadi da yamma, ina a cikin fasinjoji 24 guda 22 ne kawai suka tsara, yara guda biyu sun bace kuma ahalin yanzu ana neman su,”inji wani mutum mai suna Samson.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Mista Nnamdi Omoni a kan lamarin, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce a yanzu haka sun cafke direban kwalekwalan domin ya amsa tabbayoyi a kan faruwar lamarin.

Omoni ya kara bayyana cewa yara guda biyu sun bace, mutane 22 suka tsira lokacin da kwalekwalan ya kife a tsakanin Abuloma da kuma Kalio Jetty cikin karamar hukumar Okrika.

“Direban kwalekwalan yana da hannu a kan faruwar lamarin kuma yana wajenmu domin ya amsa tambayoyin a kan lamarin, yara biyu kuma Destiny Amamima da Ngowari Amamima sun bace.

“’Yan sandar tsibin Marine da kamu ‘yan sandar reshan Okirika sun dukafa cikin ruwan domin binciken yaran guda biyu sannan su duba ko sun saka rigan ruwa ko kuma basu saka ba.

“Mun gargade su a kan su tabbatar da cewa  koda yaushe fasinjoji sun saka rigan ruwa, amma fasinjojin suna cewa rigunar sun tsofa sai dai mun umurcesu da su dunga sakawa hakanan kafin a kawo sababbi,” inji Omoni.

 

 

 

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: