Ruwa Da Wuta Ne Babban Matsalolin Da Harkar Ruwan Leda A Jihar Kano-inji Zakari Big-Alhayat. — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Ruwa Da Wuta Ne Babban Matsalolin Da Harkar Ruwan Leda A Jihar Kano-inji Zakari Big-Alhayat.

Published

on


An bayyana cewa babbar kalubalen da ke damun masu masu masana’antun samar da tsaftataccen rowan sha na leda a jihar Kano shi nena rashin samun ruwa kai tsaye daga fanfuna da kuma  matsalar rashin  tabbatacciyar wutar lantarki.Shugaban kamfanin ruwa na Big-Alhayat dake Kano. Alhaji Zakari Abubakar ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce yawanci sukan je su samo ruwanne sakamakon baya zuwa a fanfunansu dole tasa ake kawo musu daga baya ma ya sayi motoci da suke zuwa su sayo ruwanda zasuyi aiki da shi,hakama a bangaren wutar lantarki basa iya samun wadataccen wuta da zasuyi aiki dashi sai lokaci-lokaci ake kawowa dole saidai suyi amfani da janareto .

Alhaji Zakari ya ce duba da irin hidimarda akewa aikin wajen ingantashi sai aga daga karshe ba wani abu mai yawa ake samu na riba ba haka dai ake daurewa akeyi.Suna kuma kokari wajen ganin sun cika dukkan ka’idoji da dokikin hukuma wajen samarda ruwa mai kyau da inganci da tsafta dan kiyaye lafiyar al’umma.

Shugaban Kanfanin na Big-Alhayat ya ce, ya shiga harkar ruwane tun  yana karamin yaro  yake saida lemo da kankara  a akawatin soyoyo har takai ya sai firji yanasa llemon kwalba da kunun zaki da ruwa da akae sayarwa a doguwar leda,har takai yake sayen rowan da yawa harma ake zuwa a sara a wajensa.Sai wani ya bashi shawara ya rika yin rowan da kansa daga nan ya sami aron wuri yasai kayan aiki yake yin rowan.

Ya ce daga baya da ciniki ya karu ruwansu ya karbu saboda ingancinsa sai ya samo injuna na zamani da suke iya aikin tsaftace ruwa ba tare da ansa hannu ba suka inganta rowan ya zama bashida banbanci dana roba da ake zubawa saboda irin bincikenda sukayi da bin ka’ida ta hukumomi masu kulada ingancin abinci suna daukar shawararsu har suka kaiga nasara.

Alhaji Zakari ya ce suna kyakkyawar alaka da hukumar NAFDAC da ma’aikatar lafiya da hukumar tsaftace muhalli harma suna yaba musu bias irin kokarinda suke na bin ka’ida dan inganta harkar ruwansu.

Shima da yake karin bayani mataimakin shugaban kanfanin na Big-Ahayat  Muttaka Ahmad ya ce suna da dinbin ma’aikata da suke aiki a kanfanin,samada shekaru 10 kenan suke harkar ruwa suna amfani dad a ake dafa ruwa a tace  da ake kira R.O.Suna kuma taimakawa Gwamnati wajen kai wa dinbin matasa aikin yi da ake biyansu daidai gwargwadon aikinsu.

Muttaka Ahmad yayi kira ga Gwamnati ta tallafa musu dan karfafa musu gwiwa wajen samar da aiki ga matasa.





Advertisement
Click to comment

labarai