Tasirin Magani Gargajiya Cikin Al’ummar Hausawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Tasirin Magani Gargajiya Cikin Al’ummar Hausawa

Published

on


An wayi gari wata mata ‘yar asalin wannan gari da ake kira Hajjo na da’awar bayyanar aljanu a jikinta, wadanda suke amfani da ita wajen taimaka wa marasa lafiya, su samu waraka.

Umar Ayuba shi ne ma fi kusaci da Hajjo a kan harkar wannan bayar da magunguna, ya kuma bayyana wa wakilinmu Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki da  Lawal Umar Tiga, lokacin da suka yi tattaki zuwa wannan garin domin ganin abin da ke faruwa tare da bayar da labari ga masu karatunmu.

Sabaoda haka, Umar Ayuba ya ce tun farko kakanninsu suna bayar da labarin cewa, asalin faruwar wannan al’amar shi ne, lokacin da aka yi wa Hajjo aure takan wayi gari ta ga dukkan fantekokinta a cike da rubutu, sai ta kwashe ta zubar, Gobe ma haka za ta sake gani. Don haka sai aka hana ta zubarwa, aka ce maimakon zubarwa ta dinga bayarwa sadaka da niyyar, Allah ya biya wa wanda aka ba bukatarsa.

Daga nan sai aka fara fahimtar cewa, wannan rubutun da take bayarwa yana magani cututtuka. Labari ya fara yadu wa. Saboda haka mutanen garin da ke da larura suka fara kawo kokon bararsu. Gaba dai gaba dai, har abu ya fara nisa. Ganin haka mijin Hajjo ya ce, ba zai iya zama da ita ba, saboda yawan huldar da take da masu karbar magani. Nan fa aure ya mutu ta koma gida, ta ci gaba da bayar da magani abu kamar wasa, kullum abin sai kara bunkasa yake kamar  wutar daji.

Lokacin da wakilanmu suka je garin ba su iya yin tozali da Hajjo ba, saboda tsananin cinkoson jama’a, har a lokacin an dauko mutum biyu sun sume saboda tsanin cinkoso da zafi, amma dai duk da haka jama’a maza da mata sun yi dafifi, suna jiran shiga gurin aljani.

Dalili na byu da wakilan namu suka kasa yin ido biyu da Hajjo shi ne an ce a loacin aljanin na jikinta, yana kan aikin bayar da maganin.Saboda haka da aka ce masa ga ‘yan jarida nan sai ya ce ba zai yi magana da ‘yan jarida ba. Har wakilan na mu suka bar wurin, ba su iya ganin aljanin ba, ballantana su yi masa tambayoyi.

Ajanun da aka ayyana cewa suna shiga jikin Hajjo lokacin da take bayar da maganin akwai Likita da Danmama.

Likita yana aiki ranar Asabar da Lahadi shi kuma Danmama ranar Litin da Talata.

Yadda Likita ke gudanar da aikinsa shi ne, idan aka je da larurar da ke bukatar ofarashin, zai bayar da rubutu da wani magani ya ce a je a sha yadda cutar za ta taru wuri daya. Zai fadi ranar da za a dawo domin yin ofarashin.

Idan aka dawo a wannan ranar, sai a sa ka sayo sabuwar reza, zai tsaga cikin ya fitar da cutar da ke ciki, kamar yadda makusancin Hajjo, Umar Ayuba Ya fada.

Wakilan namu sun ci karo da Sama’ila Nasarawan Kuki jim kadan bayan fitowarsa daga dakin ofarashin, ya ce, lokacin da aljani Likita zai yi masa ofarashin, sai ya bukaci ya kawo sabuwar reza da kwalbar maltina da madata.

Ya ce lokacin da ake tsaga ciknsa yana ji, sannan kuma bayan an gama, ba a dinke ba, sai dai ya ji a soke shi a guri uku an kuma shafa masa auduga, aka ce ya sha maltina da madara, ya dan huta sannan ya fita, ya ce ya ji an ciro masa wani abu a ciki amma bai ga ko mene ne ba. Amma dai da aka tambaye shi ya yake jin yanayin jikin nasa, sai ya bayyana wa wakilan namu cewa, ka san shi sauki sai a hankali. Saboda haka aikin aljanin Likita shi ne yin ofashin da kuma aikin ido.

Sai aljani Danmama wanda shi kuma aka ce ya kware wajen bayar da maganin aljanu da sammu da mayu da makamantansu, wanda kuma yake hawa kan Hajjo tare da bayar da magani ranar Litinin da Talata.

Isa Haladu Anadariya, shi ne wanda ya wakilci sarkin Anadariya wajen yi wa wakilan na mu bayani, wanda ya ce, bayan da aljanun Hajjo suka bayyana, wadanda suka nuna cewa za su taimaka wa jama’a wajen ba su magani. Da abin ya fara karfi, sarkin ya jagorance su zuwa wajen hakimin Bebeji wanda suka bayyana masa yadda abin yake kuma ya zo da kansa, ya ga yadda abin ke gudana,

Kamar yadda Haladun ya ce, hakimin ma ya karbi maganin, sannan ya tambayi jama’ar da ke wurin cewa, ko suna samun sauki suka ce masa suna samu.

Shi kuwa Dakta salisu Muhammad kwararre a fannin fata, ya nuna cewa, a likitance babban ganganci da wauta ne wanda ba likita ba ya yi ofarashin. Domin kuwa dole sai wanda ke da ilimin likitanci zai iya wannan aiki in dai ana so a wanye lafiya. Domin a jiki akwai hanyoyin jini, akwai jijiyar ma da ake ce mata majinaciya wadda idan aka sake aka yanke ta, jini ya balle ba a nemi taimakon likita ba ana iya mutuwa.

Sannan dangane da maganar cewa aljani ya iya cire wani abu daga jikin mutum nan ma likitan ya musanta wannan, ya ce hanyar da aka fi amincewa da ita wajen neman waraka ita ce ta ilimi.

Sannan ya yi nuni da cewa, musamman wadanda aka ce aljani na yi musu ofarashin baya ga hatsarin yanka gurin da bai kamata ba, akwai kuma hatsarin shigar cuta, bayan an yi aikin. Tun da ba wani magani da za a bayar na kariya daga shigar kwayoyin cuta inda aka yanka, musamman ma da aka ce ba a dinke gurin da aka yi yankan.

Likitan ya ce ko da ma ana dinke wa, domin irin kayan aikin da aka yi aikin da su da muhallin da aka yi aikin duk a bin tambaya ne, wanda kuma babu gamsasshiyar

Amsar da za a bayar a kan wannan tambaya. Saboda haka, sai ya shawarci jama’a da ke da larurorin rashin lafiya da su je asibiti domin neman magani saboda nan ne kadai ya fi dacewa da su.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!