Zamanin Magudin Zabe Ya Wuce -Gwamna Ortom — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Zamanin Magudin Zabe Ya Wuce -Gwamna Ortom

Published

on


Gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom ranar Asabar ne ya bayyana cewar, lokacin da ake yi magudin zabe ya wuce, don haka ma ya yi kira masu shirin su yi madin zabe a shekarar 2019 da cewar su yi watsi da wannan shawarar.

Ortom ya yi wannan bayanin ne lokacin da ake bizne marigayi shugaban shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa (NUJ) reshen jihar Binuwai Comrade Dabid Ukuma a makarantar Firamare ta Anshiba, a  cikin karamar hukumar Ukum ta jihar.

Shi dai tsohon shugaban kungiyar ‘yan jaridun  ya mutu ne bayan gajeruwar rashin lafiya, ranar 25 ga watan Agusta 2018 yana da shekara 45 ya bar matar aure daya da  kuma ‘ya’ya uku.

Gwaman lokacin da yake magana ya bayyana cewar ga al’ummar jihar Binuwai maganar 2019, ba wani abinda mutum zai iya yi, dole ne aba mutane abinda suke so, a manta da wata maganar magudi.

Don haka sai ya yi kira da ‘yan Nijeriya wadanda suke jihar dasu lura da katin zaben su, saboda da ita za su iya canza al’amarin su, ya kuma ce marigayin mutumin kirki ne.

Shi ma da yake na shi jawabin Reberend Father Barnabas Nyam wanda yake daga majami’ar St. Michael’s Kuasi Parish Gbeji ya yi kira da mutane su shirya ma mutuwa, saboda dukkan mai rai mamaci ne.

Nyam ya yi kira da shugabanni su taimaka wajen yin ayyukan ci gaba, maimakon su rika yin abubuwan da zasu rarraba kawunan su.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!