An Raba Naira Tiriliyan Biyu Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Kananan Hukumomi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

An Raba Naira Tiriliyan Biyu Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Kananan Hukumomi

Published

on


Hukumar masana’antu da sanya ido ta kasa NEITI ta samara da cewar sakamakon karin farashi da aka samu na danyen mai, da kuma man da ake sarrafawa a gida Najeriya kudin shida da kasar take samu ya haura da aka samu daga mai, inda hakan ya sanya kananan hukumomi suka samu naira tiriliyan biyu a cikin zangon shekara ta biyu ta 2018.

Daraktan sashen bayanai da wayar da kai na hukumar Dakta Ogbonnaya Orji ne ya bayayana hakan a a cikin sanarwar da ya fitar a ranar litinin data wuce. Sanarwar tana kunshe ne a cikin nazarin da hukumar ta gudanar na tsakiyar shekara, inda ta kara da cewar,  3.95 da aka samar daga cikin asusun tarayya a cikin farkon watanni shida na 2018. Bayanan fitar da bayanan da aka samo daga hukukumar kididdiga ta kasa NBS, sanarwar ta kuma nuna cewar, a farkon shekara jihar Osun ta karbi naira biliyan 10.24 daga asusun tarayya aka kuma cire naira bilyan14.52.

Wannan ya nuna cewar, abinda aka cire daga asusun jiha ya kai yawan naira biliyan 4.28 fiye da wanda aka karba daga asusun tarayya. Har ila yau, asusun na jihohi an cire wasu kudi saboda bashin kasashen waje.

Ita kuwa jihar Delta, ta karbi kaso mafi tsoka na naira biliyan 101.19 a farkon shekara. Jimlar abinda aka cire na jiha ya kai naira biliyan 13.81 ko kuma kashi 13. Bisa dari na kudin da aka karba daga asusun tarayya a cikin shekarar.

A cewar Orji, nazarin na tsakiyar shekara a cewar, jimlar kudin da kwamaitin rabar da kudin na shekara ya fitar a zangon shekara ta biyu ya kai kashi 46 bisa dari samada da adadin da aka samu a 2017 da kuma kashi  127 bisa dari samada na 2016. Rahoton ya sanar da cewar, an rabar da naira tirilyan biyu  a zangon shekara ta biyu an kuma rabar da naira tirilian 1.38 duk a cikin shekarar, indakuma naira biliyan 886.38 kacal, aka rabar a zagon shekara ta bayu ta 2016. A farkon shekara ta biyu, ta 2018  itace karo na farko da aka rabar da naira tiriliyan biyu tun zangon shekarar 2014.

Wannan ya kai har sau sha hudu da aka rabar da naira tirilyan biyu. NEITI ta kuma nuna jin dadin ta akan kudin da aka rabar sakamakon  hawan farashin mai da aka samu da aka sarrafa aka kuma  sayar a cikin gida, inda hakan ya sanya aka kara samun kudin ga kananan hukumomin sakamakon farashin danyen mai da aka sayar a kasuwar kasa da kasa. Kudin da aka rabar a zangon shekarar 2018 ta biyu rahoton shine mafi yawa da aka samu a zangon shekara ta uku ta 2014.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!