Ban Yi Da Na-Sanin Garkuwa Da Dan Shugaban Jam’iyyar APC Ba –Fatima — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Ban Yi Da Na-Sanin Garkuwa Da Dan Shugaban Jam’iyyar APC Ba –Fatima

Published

on


Wacce ake zargi da yin garkuwa da dan Bukar Dalori, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Bornu, Fatima Muhammad ta ce sam ba ta yi da na sanin yin garkuwa da yaron dan shekaru hudu ba.

Fatima ta fadi hakan ne a yayin da jami’an yan sanda suka gabatar da ita a gaban manema labarai a yau Litinin a garin Maiduguri na jihar Bornu.

‘Sam ban yi nadamar yin garkuwa da yaron ba, domin na aikata hakan ne don in samu kudi, akan kudi ko dan cikina zan iya garkuwa da shi, ina sane da cewar dan shugaban APC ne, shiyasa ma na yi garkuwa da shi, don na san zan samu kudi, in na samu kudin zan morewa rayuwata, toh mai zai sa in yi da na sani?’ Inji Fatima

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bornu ya shaida wa manema labarai yadda suka kama Fatima da wasu yara kanana guda biyu a otel din Akbarka dake Maiduguri a ranar 21 ga watan Satumba.

Fatima wacce ake zargin ta sace yara biyu a makarantarsu, inda ta neme tukuicin naira miliyan 20 kafin ta saki yaran, jami’an ‘yan sanda na musamman masu kama ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane ne suka kama ta, dama tana da juna biyu, daga bisani ta haihu a inda take boye da yaran.

Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutum biyu da ake zargin sun taimakawa Fatima wajen sace yaran.

 

Advertisement
Click to comment

labarai