Aikin Gona Da Harkar Noman Karo Suna Inganta A Jihar Bauchi – Dokt Ilyasu Gital — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Aikin Gona Da Harkar Noman Karo Suna Inganta A Jihar Bauchi – Dokt Ilyasu Gital

Published

on


Dakta Ilyasu Aliyu Gital Shi ne babban manajan hukumar bunkasa aikin gona ta Jihar Bauchi BSADP, ganin yadda damina take neman kaiwa karshe, wakilinmu a Bauchi  MUAZU HARDAWA ya ziyarce shi don jin irin shawarar da suka ba manoma a daminar bana da kuma yadda aka kaddamar da sayar da motocin noma iri, tare kuma da tabo batun inganta nomar karo a Jihar Bauchi ga yadda hirar su ta kasance:

Da farko bukatar manoma shine taki, wane tsari kuka bi na sayar da taki a bana?

Akwai hukumar NAMET ta kasa wacce ke lura da yanayi su ke bamu yadda tsarin damana ke kasancewa da sauran hasashen yanayi  wanda ya nuna mana abana za a samu ruwa mai yawa kuma damanar za ta sauka da wuri, don sun  kiramu Abuja sun sanar da mu kamar yadda suke yi kowace shekara, saboda hakane muka samu gwamna muka sanar da shi aka kaddamar sayar da taki da wuri  kuma har yanzu ake sayarwa manoma.

Yanayin duniya ya nuna kowace damina da irin nata zuwan kuma ana samun sauye sauye daga abin da aka saba tabbas kowa ya sani daga shekaru biyar da suka wuce akwai sauyi yanzu ana zafi sai sanyi ko ana sanyi sai zafi, to dole mu yi taka tsan tsan da neman mafita a kimiyyance. Don idan ka lura tun ana zafi kafin ruwa ya sauka aka fara walkiya aka samu ruwan sama tun daga watan hudu zuwa watan biyar.

Amma shuka sai da aka kai watan biyar aka fara a kudancin Bauchi arewaci kuma watan shida, don haka daminar ta yi kyau kuma zata wuce watan goma har zuwa watan sha biyu. Haka kasashe irin su Niger su Cotono duk a bana  sun samu damina mai kyau. Musamman ganin a Afirka bamu da irin su girgizar kasa ko ambaliyar teku mai rusa gidaje, saiko a Afirka muna da annobar kwari amma gwamnatin tarayya ta tashi tsaye shekarun baya an yi feshi tsakanin kasa da kasa an rage karfinsu don haka muke neman mutane su ci gaba da addu’o’i irin wadanda koyayensu ke kasa Allah ya kawar da su, kuma mun yi nasara a bana ba a samu wannan damuwa ba.

Amma ya kamata mutane su yi la’akari da irin koshin da kasa take yi da ruwa a wasu lokuta yake bata amfani, ko kuma gyara muhalli ta tone magudanun ruwa saboda gudun barnar ambaliyar ruwa kamar yadda ya faru a wasu jihohi ya kamata a rika daukar mataki tun da wuri da kuma shawarwarin malaman gona saboda gudun asara.

Me za ka ce game da tsarin sauya abin da aka shuka bara da wanda za a shuka a bana don samun amfani mai yawa?

Mun dauki hanya biyune ta yanayin zuba taki, wato a dawo da zuba takin gargajiya a hada dana zamani don takin gargajiya ya fi rike kasa. Kuma akwai tsarin kato huta garma huta wato (conserbation agriculture), dabarace ta noma da ba  sai an shigar da katafila a cikin gona a kowace shekara ba sai lokacin da kasa ta fara tauri idan saran ramin shuka yana wahala sai ko mutum ya nemi maganin ciyawa.

Haka kuma karan ko ciyawa za a bar su ya kasance sun ruba sun zamo taki don haka muke nuna wannan dabara ga manoma don tana rage sare daji batun da ke kawo sauyin yanayi da lalacewar muhalli. Mutane sun gwada tsarin  sun ga fa’idarsa, don haka muke son ku taimaka mana wajen wayar da kan jama’a.

A bana wajen raba taki ba a samu kura kurai sosai ba, don an bi hanyar da manomine zai ci gajiyar rangwamen da ake taimaka masa ta hanyar rabawa karkashin kungiyoyin manoma da masu unguwanni da suka karbi kudin mutanensu da ke bukataba da kuma sayarwa kai tsaye da takin bai samu ba. An fara kawo taki da wuri kuma an raba takin da gwamnati ta saya hannun gwamnatin tarayya har yanzu akwai taki a jibge ana ci gaba da kawo wani kuma ana yin taki dan Bauchi . Haka  Ina aka kwana game da batun nomar karo a Jihar Bauchi.

Mun fara hidimar karo kamar da wasa amma yanzu ta kankama don a Afirka Nigeria da Sudan sune kan gaba wajen kasar noma karo, a Nigeria kuma ba kamar Jihar Bauchi da Yobe , muna da halin mu noma karo giredin da duk ake bukata saboda yana gyara kasar noma ba tare da kashe kudi mai

yawaba. Don a baya algush ya kashe harkar karo a kasar nan don haka yanzu muka bukaci a gudanar da harkar a kungiyance sai aka zabi shugabannin manoman karo  wanda ke da kokarin nazari da kuma ilmantar da abokan huldarsa da neman ilmin harkar.

Yanzu muna da manyan manoma karo a Jiha da suka karbi dashe suka dasa kuma yanzu duk ya girma ana cin moriyarsa, abin da ya saura shine su kasance a kungiyance suna iya ware kowane karo giredi giredi donhaka muke son mayar da wannan jihar babbar cibiyar hada hadar noman karo ta duniya.

Wace daraja karo ke da shi  kuma menene amfaninsa?

Duk wani maganin da ka sha a yanzu zai yi wahala a ce ba karo cikinsa duk bawon kafson da ake yi da karo ake yinsa, kuma  kayan lemon kwalba na shaye shaye duk akwai karo a ciki don su jima basu lalace ba kuma idan karo ya shiga ciki sai ko ya gyara ciki amma baya cutarwa, don haka duniya an yi ittifakin ba abin da ya fi karo amfani a fannin hada magunguna. Haka ta fiskar hada kayan amfanin gida irin su fenti da robobi da adon kujeru da jikin bango  duk da karo ake ingantasu, don haka kullum  kasuwar karo na sake bunkasa a duniya ana samun masu bukatarsa daga ko wane sako, don haka muke kiran manoma su tashi tsayesu himmatu a harkar nomar karo saboda idan ka shuka ya shekara  biyar sai ko ka ci gaba da diba kurum ba tare da bayi ko noma  da makamantansuba, haka kuma a duk shekara za ka iya shuka a gonar don samun amfanin abinci na yau da kullum.

Don haka karo a kullum mutuncinsa karuwa yake yi a duniya kuma zai taimaki manomanmu da matasan mu da basu da abin yi samun madogara da ingancin rayuwa da samun kudin shiga matukar suka rungumi wannanharka ta nomar karo.

 

Advertisement
Click to comment

labarai