An Fi Samun Koma Baya A Rayuwar Jama’a A Jihohin Sakkwato Da Katsina Da Bauchi, Inji UNDP — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

An Fi Samun Koma Baya A Rayuwar Jama’a A Jihohin Sakkwato Da Katsina Da Bauchi, Inji UNDP

Published

on


Jahohin Sokoto, Katsina, Bauchi, Yobe da kuma Zamfara sune suke a kasa a cikin rahoton da hukumar  UNDP na shekarar 2018. Kididdigar ta yi kuma nazari a kan na shekarar 2016.

Har ila yau, nasarar da aka samu na HDI ya nuna cewar an samu ci gaba wajen fannin kowon lafiya, samun ilimin zamni da kuma ingantar rayuwa. Jihohin da kuma suka taka rawayar gani sun hada da, Legas da Abuja da Bayelsa da Akwa Ibom da kuma Ekiti.

Wadanda kuma suke bi masu sun hada da Delta da Kross Ribas da Ogun da Ribas da Abia da Enugu da Edo da Imo da Osun da Kwara da Nasarawa da Ondo da Anambra da Filato dakuma Benuwai sauran sun hada da Taraba da Kogi da Oyo da Ebonyi da Adamawa da Kaduna da Gombe da Nijar da Kebbi da Jigawa da kuma Kano.

A bisa kokarin da jihohin suka yi, jihar Legas nata ya kai yawan 0.6515 wanda ya kasance fiye da sauran na jihohi. Har ila yau, ta rike kambun ta, inda ta kai matsayi na farko a shekarar 2013 na HDI  da yawan ta ya kai 0.6716.

Abuja ita ce ta kai na biyu 0.6289 kuma ya haura zuwa shida ta kuma kai na bakwai a shekarar 2013 na HDI da yawan 0.5112.

Bugu da kari, yawan ya kai  0.5909, jihar Bayelsa  ta zama na uku inda ta sauka zuwa na biyu a shekarar 2013 daga yawa 0.621.

Jihar Akwa Ibom ta kai na hudu da yawan 0.5641 kuma ta rike kambunta na hudu da yawan 0.5698.

Ekiti ta kai na hudu inda take da yawan 0.5608, kuma tana daya daga cikin jihohin da suka yi kokari bayan data kai mataki na sha daya ta haura da sha shida a shekarar 2013.

Jihar Sokoto bata tabuka wani abin kirki ba, inda ta kai mataki na 37 tana kuma da yawan da ya kai   0.2910 a shekarar 2016, inda ta kai mataki na 36 a shekarar 2013 da yawan 0.1942.

Ma’ana a nan duk da cewar jihar ta ja da baya, a kan kai wa matsayi amma yawan karfin ta ya karu a lokuta biyu.

Jihar  Katsina  ta kai hawa na hudu, inda ta kai mataki na 36, sai dai, yawan nata ya karu zuwa 0.2364 a shekarar 2013 kuma yawn adadin ta ya kai  0.3031 a cikin shekarar  2016 HDI.

Jihar  Bauchi nata ya kai yawan 0.3238, inda ta kai matsayi na 35. Amma a shekara 2013 ta kai mataki na 29, inda take da yawan of 0.2636.

Jihar Yobe, ta kai mataki na 34, inda take da yawan 0.3249. A shekarar 2013, ta kai mataki na 37 da yawan 0.1247. jihar Borno ta kai mataki na  33 da yawan 0.3276; inda a shekarar 2013, ta kai mataki na  34 da yawan 0.2135. jihar  Zamfara nada yawan  0.3392 sabanin a shekaru uku da suka shige inda ta kai mataki na  30 da yawan 0.2623.

Yawan da ake dashi na HDI  ya kai  yawan 0.5114, inda jihohi  23 suka yi kasa. A shekarar 2013 HDI ya kai yawan 0.5060.

A rahoton da hukumar NHD ta fitar a shekarar 2018 ya mayar da hankali ne a kan cimma nasara a kan rayuwar al’ummar yankin Arewa Maso Gabas.

A lokacin da aka gabatar da rahoton a garin Abuja a ranar juma’ar data gabata da dare Ministan kasafin kudi da tsare Sanata Udo Udoma ya ce, don shawo tattalin arzikin  da samar da ci gaba a yankin Arewa maso Gabas kasar nan tana yin kokari wajen dakile ta’addaci a yankin.

A cewar sa, ta’asar ta yan Boko Haram a yankin ta lalata al’amuran tattalin arziki da kuma ci gaba a yankin.

A karshe Udoma ya yi nuni da cewar, rahoton kamar tunasarwa ce ga hukumomin da suka bayar da agaji a yankin.

 

Advertisement
Click to comment

labarai