Ba Abin Mamaki A Nasarar Da Gwamnatin Ganduje Ke Samu –Hon. Sheka — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Ba Abin Mamaki A Nasarar Da Gwamnatin Ganduje Ke Samu –Hon. Sheka

Published

on


HON. NAZIRU ZAKARI SHEKA, shi ne dan majalsar day a yiwa tsararsa fintinkau ta fuskar kyakkyawar mu’amala da al’ummarsa, tshon shugaban Karamar Hukumar Kumbotso wanda jama’a sukemasa lakabi da Dambumai hawa da yawa,  sannan kuma tsayayyen wakili a majalisar dokokin jihar Kano wanda kullum ake jinsa, musamman a harkokin cigaban da al’ummarsa. A tattaunawarsa da wakilinmu a Kano ABDULLAHI SHEKA.

Dan Majalisar ya yi cikakken bayani kan kan Nasarar da Jam’iyyar APC ta samu zaben fidda gwanin day a gabata, sannan kuma ya yi tsokaci kan hadin kan dake gudanar tsakanin wakilan al’umma a majalisar dokokin jihar Kano da bangaren zartaswa, , sannan kuma ya yi gudu har da zamiya kan ayyukan da  Gwamna Ganduje ke yiwa Jama’ar Kano lugudensu, ga yadda tattaunawar ta kasance.

Kwanan nan aka gama zaben fidda gwanin APC, Kuma kamar yadda Jama’arka ke maka kirari da ka yi ta-ta yi, ka samu nasarar lashe wannan zabe da tazara mai yawan gaske, shin ko mene ne sirrin hakan?

Alhamdulillahi da farko muna yiwa Allah godiya musamman kan nasarorin da gwamnatin Ganduje ke samu a jihar Kano, kuma alhamdulillahi yanzu gwamnatin a kaso 100% an ci nasarar sama da kashi 95 na manyan alkawuran da aka yiwa Kanawa, wannan ya hadar da batun harkar lafiya, al’amarin harkara kiown lafiya lamari ne wanda kullum ke kwana ya kuma tashi cikin zuciyar mai girma Gwamna Ganduje, duk hakilon da ‘yan adawa keyi, wannan bai hana gwamna ci gaba da ayyukan alhairi ga jama’ar Kano ba. Hakan tasa gwamnatin Ganduje ta ciri tutar kammala hamshakan ayyukan da ko hasidin iza hasada yasan tamu ba irin tasu bace.

Maganar zaben fidda gwani wannan ai a fili lamarin yake, sanin asali ne yasa kare cin alli, domin tabbacin amincewar da Jama’ar Kano suka yiwa Gwamantin Ganduje yasa ya amince da yin zaben kato bayan kato, wanda irin zabe sai namijin gaske wanda ya tabbatar da yana da kyakkyawar danganta da jama’arsa ya isa ya aiwatar da irin wanann salon zabe, Alhamdulillah yanzu kowa ya ga irin yadda zaben ya gudana kuma Jam’iyyar APC tayi abin azo gani musamman ganin yadda zaben ya gudana.

Wasu na hakilon cewar magudi aka yi a lokacin zaben fidda gwanin, shin ko me zaka ce dangane da haka?

Ina tabbatar da maka da cewa dan adawa ko ruwa ka zubar sai yace ka tada kura, kuma ka taba jin mara kishin cigaban Jihar Kano da Kanawa an burge su, ai wannan al’adar wasu maragurbin ‘yan siyasa ne kawai, amma amsa cewa za ayi zaben fidda gwanin ta hanyar kato bayan kato ke tabbatar maka gaskiyar maganar da makaho yace a yi wasan jifa domin ya tabbatar day a taka dutse. Ayyukan alhairin da aka shimfidawa Kanawa ne wasu mara kishi ba son a cigaba da aiwatarwa,hakan tasa suke neman yiwa Gwamna Ganduje da Gwamntinsa zagon kasa, kuma ta Allah bat a suba. Ai ga wasu Jihohin nan zaben ma ya gagara amma anyi shi lafiya an gama lafiya, ‘yan kallo lafiya mai wasa lafiya.

Ganin Karamar Hukumar da kake wakilta karamar Hukuma ce daga cikin kananan Hukumomin kwaryar birnin da kewaye, ko me za ka ce dangane da wadanda ka kayar a zaben fidda gwanin?

Alhamdulillahi kamar yadda aka san Nazari Zakari Sheka ni bani da abokin rigima, kowa nawa ne mutukar kana kishin Karamar Hukumar nan da bani da waddata ta fita, wadanda muka nemi wannan kujera ai daman mutanen mu ne kuma ina tabbatar maka da cewa yin hakan shi ke kara haske farin jinin Jam’iyyar APC. Duk wadanda muka yi wannan takara dasu ina da tabbacin suma cigaban Kumbotso ne gabansu, don haka zamu yi aiki tare wajen ciyar da wannan karamar Hukuma gaba da yardarm Allah. Kofa a bude ta ke domin karbar duk wata shawarar da ake ganin zata taimaka wajen cin zaben shekara ta 2019.

Karamar Hukumar Kumbotso na cikin kananan hukumomin da ayyukan gwamnati ke gudana gwargwadon iko, shin ko mene sirrin hakan?

Wannan shi ma yana cikin abubuwan da na mai da hankali akai, domin zaman al’ummar karamar hukumata lafiya shi ne kwanciyar hankali a gare mu, wannan tasa muke kokarin samun zama lokaci daban daban da al’ummomin mu don sauraron bukatunsu domin gabatarwa Gwamnati.

Bayan haka kuma muna yin duk mai yiwuwa domin ganin jama’a sun fahimci inda gwamnati ta sa gaba. Kasancewar ‘yan adawa wadanda basa bukatar ganin Gwamnati  ta ci nasarar da ake bukata ke ta surutai iri daban daban, wasu don rashin tai do har kazafi suke yi domin daukar hankalin mutane, amma mantawa suka yi al’ummar Kumbotso wayayyu ne sun san wanda ke kokarinkawo ci gaban al’umma sun kuma san ‘yan amshin shata.

Idan muka kalli shekaru uku da doriya na gwamnatin Ganduje, kasancewarka guda cikin ‘yan Majalisar da suka yi uwa suka kuma yi makarbiya wajen ganin jam’iyyar APC ta samu nasara, shin wane abu za ku tabbatarwa da al’ummar Kumbotso cewar laya tayi kyan rufi?

Wannan kuma ai lamari ne a bayanne Allah shaida Gwamna Ganduje na yin bakin kokari, musamman idan aka dubi halin tattalin arziki da kasa baki daya ke fuskanta a wannan lokacin, musamman a fadin tarayyar Najeriya yana cikin gwamnoni kalilan da basu taba yin batan watan biyan albashin ma’aikatan su ba. Yanzu haka cikin wadannan Shekaru uku da doriya masu albarka, akwai abubuwa masu motsa zukata, dubi aikin shifida bututun ruwa, kammala aikin babbar gadar sama data dara sauran tsawo a fadin Najeriya, haka aikin gadojin nan biyu, guda dake shatale talen titin zuwa Madobi da kuma wadda ke kusa da barikin Bukabo, dubi aikin Gadar kasa mai fukafukai a itn zuwa gidan Zoo, haka inganta harkar samar da ruwan Sha, an yiwa tsarin tattara haraji garanbawul domin tafiya dai dai da zamanin da muke ciki, dawo da kimar aikin gwamnati

A matsayin ka  na wakili ko akwai wani abu da ya kamata jama’a su fahimta dangane da harkar majalisa?

Alhamduillahi aikin majalisa aiki ne wanda ke bukatar kyakkyawar nutsuwa domin lamari ne wanda duk ayyukan gwamnati ya ta’allaka da sahallewar majalisar, mu a Kano muna yiwa Allah godiya musamman samun shugaban majalisa wanda ya san abinda ya ke, kuma dukkan mu al’umma ce a gaban mu. Wannan tasa ake aiki ba dare ba rana, haka itama bangaren zartarwa suna bayar da hadin kai kamar yadda ake bukata, wannan ne ya haifar da kyakkyawar danganta ka tsakanin majalisa da bangaren zartarwa, kowa na ganin kimar dan uwansa.

Mene ne sakonka ga al’ummar da a karo na uku suka sake sahalle maka wannan dama ta wakiltarsu a majalisar dokokin jihar Kano?

Alhamdulillahi sakona ba ya wuce godiya ga jama’a bisa amincewa da suka yi da nagartarmu suka tura mu wakilce su, sannan kuam ske yin duk mai yiwuwa wajen kare kimar wakilcin da muke, sai kuma bukatar  kara hakuri abubuwa na nan suna tafiya, nan bada jimawa ba zamu baje kolin ayyukan da muka yiwa al’umma kowa ya ganewa idonsa, kuma duk wanda ke tare da  wannan jam’iyya da ma sauran al’ummar da ke wannan jiha ba za su manta da irin gudunmawar da suka bayar ba, sai kuma yiwa mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari  fatan kara samun nasara cikin yakin da yake da barayin lalitar gwamnatin Tarayya, a ci gaba da yiwa jihar  Kano da kasa baki daya addu’a, Allah ya ci gaba da tabbatar mana da zaman lafiyar da muke gani ahalin yanzu.

Advertisement
Click to comment

labarai