Rikicin APC A Zamfara: Yari Ya Je wajen Buhari — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Rikicin APC A Zamfara: Yari Ya Je wajen Buhari

Published

on


A jiya Juma’a ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ta APC a jihar Zamfara, a fadarsa da ke Billa, Abuja.

Majiyarmu ta shaida mana cewa, wannan shi ne karo na biyu zuwan gwamna Yarin fadar shugaban kasar tun lokacin da rikicin jam’iyya APC ya turnike a jihar ta Zamfara. Har ila yau dai majiyar ta mu ta ruwaito mana cewa, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya raka gwamnan na Zamfara fadar shugaban kasar.

Ana ganin gwamnan na jihar zamfara zai yi amfani da damar ganin shugaban kasar wajen bayyana masa halin da jihar ke ciki dangane da rikice-rikicen da suka addabi jam’iyyar ta APC wadda ta kai ga har sun kasa fitar da dan takarar gwamna da sauran mukamai.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!