Wane Aiki Gwamnati Ta Yi Da Bashin Naira Tiriliyan 13 Da Ta Ciwo -Atiku — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Wane Aiki Gwamnati Ta Yi Da Bashin Naira Tiriliyan 13 Da Ta Ciwo -Atiku

Published

on


Dan takarar Shugabancin Kasa a inuwar Jami’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya kalubalanci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayyanawa alumman Nijeriya aiyukan da yayi da Naira tiriliyan 13 da ya ranto saboda gudanar da ayyuka a karkashin mulkin shi.

Yace ana ta gunaguni akan Naira tiriliyan 6 da PDP ta ranto a shekara 16 na mulkin ta, alhalin anga ayyukan cigaban kasa da PDP tayi a Nijeriya. Alhaji Atiku Abubakar ya zargi Gwamnatin Buhari ta APC da kin maida hankali gurin gudanar da ayyukan da zai amfani alumman kasa sai zargi da yada karerayi  ga Dan takarar PDP. Atiku yace; Buhari ya  gayama yan Najeriya me kayi da bashin Tiriliyon sha uku (N13Tr) da ka ciwo a shekaru sama da  uku da ka kwashe kan karagar Mulkin kasan nan.

An wallafa wannan jawabin ne a shafin yakin niman zaben Atiku Abubakar ta Instagram .

A jawabin da tsohon mataimakin Shugaban kasar yayi ta bakin kungiyar yakin neman zabensa  a Abuja a ranar Laraba, ya zargi APC da rashin aikin yi ta yanda suka bar lamarin Shugabancin da sauke hakkokin su, inda suka fi maida hankali da zargi tare da karairayi ga Dan takarar shugabancin kasa na PDP. “Domin ba wa yan Najeriya ansa, muna so kungiyar yakin neman zaben Buhari da su dauki kalubalen nan ta hanyar ansa wadannan tambayoyi.”

“Ku sanar damu aiki daya da Gwamnatin Buhari ta kirkiro, ta fara kuma ta gama a shekaru uku da suka wuce.” “Ku sanar damu alheri daya da yake a Gwamnatin Buhari.” “Ku fadi alkawari daya da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika.” “ku fada mana suna dan kudu daya da ke Shugabancin cibiyar sirri ta kasa.” “Ku fadi dan ta’adda daya da aka kama, aka kai shi kotu kuma aka daure shi a karkashin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari,”

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!