2019: Yaki Tukuru Za Mu Yi Don Kwace Mulki A Hannun APC -Kauran Bauchi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

2019: Yaki Tukuru Za Mu Yi Don Kwace Mulki A Hannun APC -Kauran Bauchi

Published

on


SANATA BALA MUHAMMAD KAURAN BAUCHI, Shine dan takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar PDP, a hirarsa da wakilinmu KHALID IDRIS DOYA da wasu ‘yan jarida ya shaida cewar a babban zaben 2019 ba za su taba bayar da dama APC ta sayi kuri’un jama’a a babban zaben ba, inda ya shaida cewar an sha su sun warke tun a zaben cike gurbin sanata da aka yi a Bauchi. Ya kuma shaida cewar za su yi shiri na musamman domin ganin sun samu nasarar kwace mulkin jihar Bauchi don su shimfida mulki mai nagarta. Ga hirar:

Wasu jama’an Bauchi na kukan yanayin da ake ciki a yau, wace hanya ko wasu sabbin lale ne za ka bullo da su domin kwalliya ta biya kudin salubu

Wannan sabon lalen dai shine a fara hada kan jama’a a hada kan al’umma, saboda abun da yake gabanmu kalubale ne babba wanda dole ne sai an jajirce. Mutane wanda basu san Allah ba basu kuma san ya kamata ba, abun da kawai suke yi sun zo sun hau doron bayan Dattijo shugaban kasa Muhammadu Buhari suka samu kujeru amma abun da suke yi ya zama daban da yadda aka dauka da yadda aka tsammata, ana yi musu kyakkyawar tsammani amma su a wajensu wayonsu ne dabararsu, kafircinsu ne, fir’aunancinsu ne ya basu wannan mukaman da suke kai a yanzu. Saboda haka ne suke sata suke duk abun da suke so, kuma sai suke raba kanmu, su dauki kan wannan su gwara da na wancan, su dauki wannan su daura su yarda shi, su sake dauko wani su sake daurawa, don haka su kansu da suke gidansu sai an taimakesu an cire musu wannan mummunar akidar da ke zuciyarsu.

‘Yan fansho na kokawa da yanayin da suke ciki, shin idan ka samu nasara ta yaya za ka yi da su?

Da farko zan ce ma’aikata sun san wannan tafiyar da muke yi tasu ce, kuma ma sune muke tsammanin ma ko ba a kirasu ba za su zo su bayar da tasu gudunmawar su, su taka nasu rawar a wannan juyin mulkin da muke son yi na kwato ‘yancin al’ummar jihar Bauchi, saboda kuwa mun shiga wani hali, babu kudin albashi babu kudin fansho ba share gari ba a kyautata wa dattawa, ba a taimakon mata, ba a baiwa dalibai tallafin karatu ba a komai, matasa da mata da kowa ma ya shiga cikin ha-‘ula’i a wannan lokacin wannan ne ya sanya muke ganin aski ya zo gaban goshi. Amma batun ‘yan fansho an ba zan taba barinsu su tagaiyara ba, hakkokinsu zai ke fita a duk lokacin da ya dace.

Ya kake kallon hasken wannan gwagwarmayar da aka sanya a gaba?

Hasken nasa akwai haske sosai, amma abu ne wanda ba za mu dauka da kamar wasa ba, za mu yi tamkar yaki ne. domin yaki da azzalumi dole sai an dage sai kuma an dirje; duk abun da suke so su yi na amfani da kudi, su yi amfani da hukuma musamman ma hukumar zabe, da kuma sauran abubuwan da suke son su yi amfani da matasa a zo a yi abun da bashi da amfani wato ta’addanci, kuma kun ga abaun da suka yi a zaben cike gurbi na sanata da aka yi kwanakin baya a Bauchi, sun zo sun soke mana kuri’unmu sun yi amfani da kudi, to mun riga mun gane, kuma muna son jama’an jihar nan su  sani yunwar da ba zai kaika kashe maka kishin ruwa na kwana bakwai ba to bai kamata a saida ‘yanci ba. wannan kudin da ake bayarwa ba za mu bari a bayar da kudin ba ma, saboda ma’aikata ne suke zuwa su raba kudin kuma kudin na mutanen Bauchi ne. za mu sanya mutanen Bauchi su kwace kudin wadanda suka kawo kudin mu yi musu shegen duka mu koresu. Kuma, in ta’addanci ne muma mun iya ta’addancin duk wanda ya kwana lafiya shi ya so. Sannan hukumar da ake amfani da su, ya kamata mu tuna musu su fa, su sani sune suke da alhakin zaman lafiya, mu ba za mu sake yarda a kawo hukuma ana soke mana kuri’a ana kawo kudi ana rabarwa a mazabu ana fadin abun da bai kamata ba saboda kawai a daura wadannan azzaluman.

Ana ganin dukkanin wanda ba ya cikin tafiyar shugaba Buhari kamar ba mutumin arziki ba ne, ta yaya za ku yi kokarin kawo sauyi ko talaka ya fahimci a wannan karon ba jam’iyya za a bi ba?

To, ai jiki magayi, kowa ya ji a jikinsa kuma kowa ya gani. Idan an ce wanda bai tafiyan Buhari ba mutumin kirki ba ne, shi wannan M.A din da yake tafiyar Buharin me ya tsinana wa jama’a? azaba ya gana wa mutane, shi Buharin baya nan ne aka gana wa jama’a azaba a jihar Bauchi?. Babu mukamin da Buhari bai baiwa jama’an jihar Bauchi ba meye suka yi da mukaman? Ai ba M.A bane kawai azzalumin, akwai azzalumai da yawa a APC, meye suke yi wa Bauchi? PDP kuma kun ga abun da muka yi a Bauchi a lokacin da muke rike da mukamai, ni daya ne Minista kowa ya san abun da muka yi.

A Facebook muna ganin hotonka ana gwamawa da na Buhari a gefe guda, kenan PD-AC ne ko yaya ne abun yake?

Ni ban san yadda wannan abun ya fito ba (dariya), wata kila an ga cewa abun da muke yi wa talaka ya zo daidai ne, tun da daman mune muka yi juyin mulki da NPP, amma shi yanzu yana APC ni kuma ina PDP.

Ya alakarka da shi Buharin?

Ni akwai alaka mai kyau kuma na zaman lafiya a tsakani.

A kwanan nan ka kafa kwamitin sulhunta ‘ya’yan Pdp mene ne dalilinka na yin hakan?

Wannan kwamitin da take karkashin Sanata Bala Adamu Kariya da wasu dattabai su tara an kafa ta ne domin a samu maslaha da zaman lafiya hadi da sulhu kana da daidaita ‘yan takara da wadanda suka tsaya takara daban-daban Allah bai basu nasara ba da suke cikin jam’iyyar PDP. Sannan kuma, kwamitin tana da nasaba da jawo wadanda aka yi musu balagada a sauran jam’iyyu musamman ma wadanda suka yi takara aka rinka kwada musu gora a kansu har suka watse ba tare da cimma wata matsaya ba don haka mu sai muka bude fuka-fukanmu da kirjinmu domin mu karbesu a cikin jam’iyyarmu ta PDP domin ita lemar tana da fadi.

Akwai wasu jiga-jigai masu fada aji a jihar nan da tunin sun shiga wasu jam’iyyun ya za ku yi wajen jawo sun shin za ku bisi gida-gida ne ko yaya?

Tunin irin wadannan masu hannu shuni kuma masu ruwa da tsaki a siyasar Bauchi da Nijeriya mun yi magana da su kuma za mu ci gaba da magana da su. Amma a ganinmu wadannan kwamitin dattaban da muka kafa su ma yayunsu ne kuma shugabanni ne a wajensu domin mun nuna musu suna da girma suna da kima idan su zo suka yi musu magana cikin yardar Allah askin da aka fara har ya zo jikin goshi za a samu a karasa.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!