Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Neja Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Neja Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar

Published

on


An nemi magoya bayan jam’iyyar ADP da su tabbatar sun kauda bambance bambancen da ke tsakaninsu dan baiwa jam’iyyar daman samun nasarar zabe mai zuwa, shugaban jam’iyyar ta jiha, Alhaji Tanimu Sarki Kwamba ne ya yi kiran a lokacin da yake karban dan takarar kujerar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar a babban zabe mai zuwa a sakatariyar jam’iyyar da ke minna.

Sarki Kwamba yace ‘yan takarkaru da dama sun fito neman wannan kujera ta gwamna amma Hon. Isah Kawu ne Allah ya baiwa wannan damar, dan haka lallai za su yi aiki ba dare ba rana dan fuskantar babban zabe mai zuwa.

Da yake karin haske ga wakilin mu, daraktan kamfe na dan takarar gwamnan, Rabaran D. S Galadima yace jam’iyyar ADP tana duban cancanta da dacewa ne shi yasa duba da irin namijin kokarin da dan takarar na su a baya lokacin da yake dan majalisar jihar da lokacin da ya Shugabanci majalisar dokokin jihar, jam’iyyar ta gamsu da kasancewarsa dan takara,

Hon. Isah Kawu ya bayyana cewar ADP za ta kafa gwamnatin jama’a ne dan jama’a, dan haka kurakuran da jam’iyyar PDP da APC suka tafka lallai mu tabbatar mun kawo gyara akai, ba za mu sake amincewa da siyasar ni da ‘yan uwana ba a jihar nan domin shi ne ya hanawa jihar cigaba.

Dan takarar yace maganar mataimakin gwamna an bar a yankin Neja ta Arewa, dan haka dole ne a tabbatar an zabo mutum mai gaskiya da amana wanda ke da akidar cigaba dan ganin mun hada hannu mun yi aiki tare idan mun kafa mulki.

Wajibin mu ne mu dawo mu dawo da martabar siyasar jihar nan, musamman dan ganin mun baiwa jama’a damar taka rawa mai muhimmanci wajen cigaban jihar, domin turakun da muke da shi ina da yakinin lallai za mu iya kafa mulki a jihar nan.

Tsarin gwamnatin mu zai zamo tsari ne irin na shugaban kasa da firaminista, domin mukaddashin gwamna wanda ake cewa mataimakin gwamna za mu ba shi karfi ta yadda zai iya yin aiki ba tare da kiran umurnin gwamna ba. ADP tana da abin da sauran jam’iyyun ba su da shi, shine gaskiya da amana da cika alkawali, duk abubuwan da muka yiwa jama’a alkawali a lokacin yakin neman zabe lallai sai mun cika shi.

Hon. Isah Kawu wanda tsohon dan majalisar jihar ne da ya wakilci karamar hukumar Bida karo biyu, kuma ya taba rika shugabancin majalisar dokokin jihar, haka tsohon dan jarida ne wanda aka shaide shi da alkibla. Yana daga cikin ‘yan takarar da za su gabza da gwamna Abubakar Sani Bello a shekarar 2019.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!