2019: Sanatocin Da Ba Za Su Koma A Zauren Majalisar Dattawa Ba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SHARHI

2019: Sanatocin Da Ba Za Su Koma A Zauren Majalisar Dattawa Ba

Published

on


Bisa ga dukkan alamu, akwai alamun da ke tabbatar da cewa adadi mai yawa na yan majalisar dattijan tarayyar Nijeriya, masu ci a yanzu, sun yiwa taliyar zauren majalisar cin qarshe- a wannan babban zave mai zuwa, a zabin majalisar na tare(9). Yayin da wasu daga cikin su ba za su dawo ba, ta dalilin neman wasu muqamai, wasu ta dalilin shan kaye a lokacin zaven fidda gwani.
A halin da ake ciki yanzu, akwai yuwuwar sama da 30 daga cikin su, sun yi ban-kwana da zauren majalisar. Har wa yau kuma, xayan biyu ne zai faru a ran 17 ga watan Nuwamba mai zuwa- a wani matakin da hukumar zave mai zaman kanta ta qasa INEC, na sauya wasu yan takara.
Amma idan hukumar bata aiwatar da canje-canjen, a lokacin da ta ayyanan, waxannan su ne yan majalisar da ake sa ran ba za su dawo zauren ba:
Jihar Adamawa:
Abdulaziz Nyako (APC Adamawa ta tsakiya) tare da Ahmed Abubakar (APC, Adamawa ta kudu), suna daga cikin waxanda ba za su dawo zubin majalisar na tara (9) ba.
Sanata Nyako wanda yanzu haka ya nuna sha’awar tsaya wa takarar kujerar gwamnan Adamawa, qarqashin jam’iyyar ADC, wanda shi kuma Abubakar xin, aka maye gurbin sa da Ahmed MoAllayidi a zaven fidda gwanin jam’iyyar.
Jihar Bayelsa:
Haka zalika kuma, Forster Ogola, Ben Murray Bruce tare da Emmanuel Paulker duk ba za su wakilci jama’ar mazavar su ba a zauren majalisar, wannan babban zace mai zuwa.
Wanda shi Forster Ogola (PDP, mazavar Bayelsa ta kudu) ya rasa tikitin jam’iyyar sa ta PDP ne, ta dalilin shan gaban sa da Mista Lawrence Ewhrudjakpo- kwamishinan ayyukan jihar. Yayin da a Bayelsa ta gabas kuma, Ben Murray Bruce, ya bayyana rashin komawar sa a zauren ne ta dalilin tsarin karva-karva a tsakanin qananan hukumomi uku da ke da wakilci a majalisar. Wanda Emmanuel Paulker (PDP tsakiyar Bayelsa), wanda sunan sa ya rikito qasa a lokacin zaven fidda gwani.
Jihar Benue:
Jiha ce ta tsohon shugaban majalisar dattijan, David Mark, mai wakiltar kudancin jihar Benue, tun daga 1999, wanda sai a wannan karon ya tava qasa, a lokacin zaven fidda gwani-wanda alamu ke nuna cewa bana ba za a dama dashi ba.
Jihar Borno:
A jihar Borno, sanata Baba Kaka Garbai, ba zai kkma a zauren majalisar ba. Sanata Garbai (APC, tsakiyar Borno), wanda gwamnan jihar, Kashim Shettima, zai maye gurbin sa a zave mai zuwa.
Jihar Cross River:
A can kuma Mista John Enoh (APC, tsakiyar Cross Rivers) wanda aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaven fidda gwanin takarar gwamna a jihar, a qarqashin jam’iyyar APC. Wannan shi ne abinda ya hana shi dawowa a zauren majalisar.
Jihar Ebonyi:
Bugu da qari kuma, shima Sonny Ogbuoji (APC, Ebonyi ta kudu), ya rasa damar sa ta komawa zauren majalisar dattijan, a wannan zavan 2019 mai zuwa. Wanda takarar kujerar gwamnan jihar a APC, ba ta wauce allunan tallar yan takara ba.
Jihar Enugu:
Sai kuma Gilbert Nnaji (PDP, gabashin Enugu) shima ya rasa tikitin takarar sa a qarqashin jam’iyyar PDP, wanda ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan jihar, Chimaroke Nnamani, wanda yanzu ya nuna ba zai koma a zauren ba.
Jihar Ekiti:
A can kuma, Sanata Fatima Raji Rasaki ce ta rasa nauyin sake koma wa zauren majalisar Dattawa- bayan shan qasa da ta yi a zaven fidda gwani.
Jihar Gombe:
Haka zalika kuma, a jihar Gombe Sanata Usman Nafada da Joshua Lidani, duk sun gama cin taliyar su ta qarshe a zauren majalisar- zubi na 9.
A hannu guda kuma, yayin da Nafada (PDP Gombe ta kudu), da ya faxa komar abokan adawa- a zaven fidda gwani, a takarar kujerar gwamnan jihar, su 12 a PDP, a halin yanzu bai da ta faxa. Wanda shi kuma Mista Lidani ya tunkuri qasa a hannun yar majalisar wakilai, Binta Bello.
Jihar Imo:
Shima Hope Uzodinma (APC, Imo ta yamma) ba zai dawo zauren ba. Wanda surukin gwamna Rochas Okorocha- Uche Nwosu, ya sumurmuxa a qasa a lokacin zaven fidda gwanin takarar gwamna a jam’iyyar APC. Haka ta kasance ga takwaran sa na gabashin jihar Imo, Sam Anyanwu, da ya sha qasa a zaven fidda gwanin takarar kujerar gwamna a jam’iyyar PDP, a hannun Emeka Ihedioha.
Jihar Katsina:
A can kuma jihar Katsina, Abu Ibrahim tare da Umar Kurfi, suma ba za su samu zarafin komawa zauren dattivan ba.
Baba dattijo xan shekara 72- Sanata Abu Ibrahim (APC, Katsina ta kudu), ya yanke shawarar xaukar hutu ne. Yayin da shi kuma Mista Kurfi, aka shantale qafar komawar sa.
Jihar Kwara:
Sai kuma zancen Rafiu Ibrahim da Shaaba Lafiagi, wanda ya nuna basu ba zauren- sai dai ko wani jiqon idan da rabo.
Ibrahim wanda ya janye wa gwamnan jihar, Abdulfattah Ahmed, samun damar wakiltar mazavar. Savanin Lafiagi (PDP, Kwara ta arewa), wanda ya rasa kujerar sa a qoqarin xare takarar kujerar gwamnan jihar a qarqashin PDP.
Jihar Lagos:
Cunkus xakin tsumma- ta tsame hannun Sanata Gbenga Ashafa daga batun dawowar sa zauren majalisar, yayin da xan majalisar dokokin jihar Bayo Osinowo, ya tumurmusa shi a qasa- a zaven fidda gwani, wanda APC ta gudanar.
Jihar Nasarawa:
Mista Aruwa Gyunka (PDP, Nasarawa ta arewa) ne bai yi nasara ba a karon battar qarfen zaven fidda gwanin takarar kujerar gwamna a jam’iyyar PDP.
Jihar Niger:
Sai kuma Sabi Aliyu Abdullahi da takwaran sa David Umaru, sun fita daga cikin lissafin yan majalisa- zubi na tara. Wannan ya zo ne ta dalilin zaven fidda gwani.
Jihar Ogun:
Daxin-daxawa kuma, an yiwa baki xayan yan majalisar dattijawa daga jihar kaxar xinyar makaho.
Saboda yadda Buruji Kashamu, zai gaji Bola Kalejaiye a kujerar. Haka zalika, sauran sanatoci 2 na APC, Lanre Tejuoso (Ogun ta tsakiya) da Gbolahan Dada (Ogun ta yamma), waxanda aka maye gurbin su da gwamna Ibikunle Amosun, da shugaban ma’aikatan sa Tolu Odebiyi, a zauren.
Jihar Osun:
A jihar Osun ma, ba ta canja zani ba, inda sanatocin suka yi faxuwar guzuma. Inda sanata Olusola Adeyeye (APC, Osun ta tsakiya) da Babajide Omoworare (APC, Osun ta gabas) suka rasa tikitin sake dawowa, a zaven fidda gwani- yayin da Ademola Adeleke ya tsaya zaven fidda gwani a kujerar gwamna, kuma ya sha qasa.
Jihar Oyo:
Inda sanata Rilwan Akanbi (APC Oyo ta kudu) ya rasa samun nasarar da zata bashi zarafin komawa zauren majalisar dattijan.
Jihar Plateau:
A nan ma bata canja zani ba, inda Joshua Dariye tare da Jeremiah Oseni, aka yi waje rod dasu.
A Plateau xin dai, inda sanatan su na tsakiya, Dariye, ke ci gaba da zaman jarun na kimanin shekaru 14- bisa zargin cin hanci da rashawa, a lokacin da yana gwamna. Yayin da shi kuma Mista Useni (PDP, Plateau ta kudu) shima ba shi a zauren a wannan jiqon.
Jihar Rivers:
A mazavar Rivers ta kudu maso-gabas kuma, Magnus Abe, ya tava qasa a qoqarin samun tikitin APC- na zaven fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar.
Jihar Yobe:
Sanata Bukar Abba Ibrahim (APC, Yobe ta gabas), ya sahale wa gwamna Ibrahim Geidam, domin ya maye gurbin sa a majalisar dattivan.
Jihar Zamfara:
A Zamfara ce turnuqu ya kacame, inda qura ta hana baki xayan yan takarar APC rawar gaban hantsin samun tsaya wa – a zaven 2019 mai zuwa. Hukumar INEC ta kafe kan cewa, tunda ranar 10 ga October ta wuce ba tare da gudanar da zaven fidda gwanin ba, bakin alqalami ya bushe- an rufe qofa suna waje.
Kafin wannan matsaya ta hukumar INEC, Ahmed Sani Yerima (APC, Zamfara ta yamma), ya haqura da takarar sa, inda ya barwa gwamna Abdul’azeez Yari, yayin da shima sanata Kabiru Marafa (APC, Zamfara ta tsakiya), akwai yuwuwar ba zai koma a zauren ba, bisa aniyar sa ta takarar gwamna a jihar.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!