Jam’iyyar PDP Alheri Ce Ga Al’umman Nijeriya -Kubarachi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Jam’iyyar PDP Alheri Ce Ga Al’umman Nijeriya -Kubarachi

Published

on


Kawo yanzun ‘yan siyasa suna ta tofa albarkacin bakunan su game da takarar Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar, wanda Jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar domin ya yi mata takaran shugabancin kasar nan a babban zabe na 2019.
ALHAJI BALA KUBARACI GARKUWA, fitaccen dan siyasa ne wanda ya taka rawar siyasan a dukkanin manyan Jam’iyyun nan guda biyu, da farko ya yi PDP ya koma APC, a yanzun haka kuma ya fice daga APC din ya koma Jam’iyyar PDP. A wannan zantawan da ya yi da wakilinmu, UMAR A HUNKUYI, ya yi fashin baki ne a kan dalilansa na komowa Jam’iyyar na shi ta asali watau PDP, da kuma yanda yake kallon ‘yan takaran da Jam’iyyun biyu suka tsayar tare da dalilansa a kan kowannen su. A sha karatu lafiya:

A wasu lokuta baya kadan ka yi suna ne a cikin Jam’iyyar APC, amma kuma ga shi a yanzun mun ji kana tallata dan takaran Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, to ko mene ne dalilin hakan?
Kamar yanda na sha gaya wa mutane, in dai har ana son a sami gyaran da ya dace mai ma’ana a kasar nan, wanda zai fitar da mu daga cikin wannan taskun da al’umman kasa suke a cikin sa, to Atiku shi ya fi cancanta da ya shugabanci kasar nan. Domin yana da abubuwa da halayen da suka fifita shi a tsakankanin dukkanin sauran ‘yan takaran nan.
Da farko dai Atiku, mutum ne wanda in mun duba tarihin baya, akalla tun daga shekarar 1999, duk wani Gwamna a kasar nan, ko Minista, ko ma’aikacin gwamnati a wancan lokacin ko yana Jam’iyyar PDP ne, ko APP ko AD a wancan lokacin, to tabbas Atiku ya taimake shi, hatta gwamnonin nan wadanda a yanzun za ka ji wasun su suna kokarin yi ma shi rashin kunya, gabakidayan su ba wanda bai zama yaron Atiku ba, ta hanyoyin da ya taimaka ma su.
Atiku, mutum ne wanda Allah Ya yi wa baiwan rashin nuna bakin ciki a rayuwar sa, shi mutum ne mai son ya ga cewa al’umma sun ginu, shi a kullum yana son ganin al’umma a cikin farin ciki da walwala, ba shi da keta, ba shi da bakin ciki a rayuwarsa. Sannan kuma a siyasance ma, a Nijeriya yanzun haka, babu wani gogaggen dan siyasa wanda ya san ma’ana da manufofi na siyasa kamar Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar. Domin duk inda ka kewaya a cikin shiyyoyin kasar nan, a bangaren Yarbawa ne, ko a bangaren Inyamurai ne babbalantana a nan bangaren arewacin kasar nan, Atiku yana da magoya baya, kasantuwar irin yanda ya amfanar yake kuma ci gaba da amfanar da al’umma.
Ni a matsayina na Musulmi, ina sane da cewa, Ma’aikin Allah, (SAW), ya shahara da fifita a kan dukkanin Annabawan Allah, (AS), da yawan kyauta wane Sarfa, jinkai da tausayi, wanda ba ya misaltuwa. Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar, ya debo irin wannan dabi’a ta Manzon Allah, (SAW), sai ya kasance shi mutum ne mai tausayi wanda ba ya son ya ga duk wani dan Adam a cikin wahala. Ka lura da kyau ka gani, duk na tare da Atiku, ba za ka same shi a cikin kunci da wahala ba.
Ba kuma wani mutum a Nijeriyan nan, tun daga zamanin su Sardauna, walau a cikin ‘yan siyasa ko attajirai, wanda al’umma suke amfanuwa da arzikin sa kamar Atiku Abubakar. Yana da Kamfanoni birjik a kasar nan, makarantu manya da kanana, cibiyoyin bayar da tallafi kala-kala, da makamantansu masu yawa, wadanda yawancinsu duk ba ya kafa su ne domin neman riba ba, sai domin ya taimaka wa al’umma. Shi kadai ne mai diban ‘ya’yan talakawa yana kai su waje suna karatu ba kuma domin siyasa ba, bilhasali ma, ba kasafai yake son a san yana yin hakan ba. Shi kadai ne wanda matukar koken ka ya kai gare shi, tabbas zai taimaka maka, ba kuma la’akari da ya sanka ko bai san ka ba, shiyyar da ka fito, kabilar ka ko Addinin ka ba, manufarsa ya taimaki masu bukata.
Atiku ne kadai a halin yanzun wanda matukar Allah Ya ba shi mulkin Nijeriya, da izinin Allah, cikin shekara guda da hawansa, talakan Nijeriya zai tabbatar da ya samu ‘yancin kansa, sauki kuma ya zo ma shi daga cikin irin wannan bakar wahalar da yake dandana a halin yanzun.
Amma ina tabbatar maka, in har aka yi kuskure shugaban da ke kan mulki a halin yanzun ya zarce, to sai ka ga mutane suna tafiya kamar su kama da wuta saboda wahala. Saboda ko a yanzun haka, Mai girma Shugaban kasa, ya tara mutane ne wadanda suke bakaken azzalumai ne kuma manyan barayi a kewaye da shi, wadanda suke cutar da jama’a, kuma kansu kadai suka sani.
Don haka, ina kira ga al’umman Nijeriya, matukar suna son kasar nan ta dawo cikin hayyacin ta, to su yi dango su zabi Atiku Abubakar, domin shi ne kadai mafita a wannan kasa ta mu Nijeriya. In kuma har suka sake, suka zabi wani wanda ba Atikun ba, to ina matukar tausaya mana irin taskun da za mu shiga cikin ta a wannan kasar tamu Nijeriya, Allah Ya kyauta.
To amma ba ka ganin wannan takaran tana da zafi, kasantuwan shi Atikun zai fafata ne da wanda ke kan Shugabanci a halin yanzun, sannan kuma shi ma Shugaba ne da ya fito daga arewacin kasar nan tamkar shi kansa Atikun?
Ai wannan takaran mai sauki ce, takara ce ta yin zabi a tsakanin ci gaba da zama a cikin bakar wahala, da kuma neman samun ‘yanci da kuma saukin rayuwa, takara ce ta in zabin ci gaba da zama a karkashin mulkin marasa tausayi da imani, zuwa ga wanda ya san kima, daraja da mutuncin dan adam, watau Atiku Abubakar, don haka, mutane wayar masu da kai kadai ake da bukatar a ci gaba da yi, domin kowa yana dandana wa a jikinsa a halin yanzun. Ina tabbatar maka, da zaran al’umman kasa sun fahimci ko wane ne Atiku Abubakar, to karfe 11 ba ta cika a ranar zabe face Buhari ya ruguzo daga kan kujerar da yake a kanta a halin yanzun.
Saboda ai Buhari ya rigaya ya bata da mutanan Nijeriya, domin na farko, ya yi masu alkawurra a matsayinsa na wanda a baya ake masa ganin tamkar wani karamin waliyyi ne shi, amma ko guda daya ya kasa cika masu shi. Daman can mu ‘yan PDP ne muka gudu muka koma APC saboda sharrin Boko Haram, amma ga shi yanzun sharrin ma ya fi na Boko Haram din, ga dai Boko Haram din tana nan, ga satan mutane, ga bayin Allah ana kashe su da ba su ji ba, ba su gani ba. Ga talauci, mutumin da a baya kafin hawan Buhari yake da jarin milyan 20, a yanzun ya dawo ba shi da jarin ko kwabo, a yanzun haka mutanan da suka gudu suka bar Nijeriya ba a san adadin su ba.
A zo har gida cikin iyalanka a dauki mutum, mutumin ma da bai taba ganin Naira 200,000 ba a rayuwarsa, a ce sai ya kawo Naira milyan daya kafin a sake shi. Kana son ka yi tafiya domin sada zumunci, amma yanzun zumuncin ya gagari mutane sai dai ta waya.
Kafin mulkin Buhari muna siyan shinkafa Naira 7,000 ne, amma yanzun ta koma Naira 20,000, muna biyan kudin makarantar yaran mu ne Naira 5,000 zuwa 8,000, yanzun ya koma Naira 30,000. Asibitoci ba magani, sai dai ka je asibitocin kudi, kuma fa shi da kansa ne Buharin ya ce, in har ya ci zabe ba wanda zai kara zuwa wajen kasar nan neman magani, sai ga shi ya tafi wajen ya kwashe wajen watanni uku da kudin talakawan Nijeriya da sunan wai ya je neman maganin. Buhari ne fa ya ce, in ya hau mulkin kasar nan a cikin watanni shida da hawansa, lantarki zai wadaci Nijeriya, ga shi yanzun lantarkin ma kara lalacewa ya yi. Buhari ya ce mana in ya hau zai samawa mutane milyan 20 ayyukan yi, sai ga shi da hawansa sama da mutane milyan 30 sun rasa aikin yi. Leadership, in na dinga lissafo maku barnar da Buhari ya yi ne, ina da tabbacin da Naira 10 babu mai siyan shi.
To a karshe wace shawara za ka baiwa al’umman Nijeriya kan wannan tafiya ta Atiku Abubakar?
Shawarar da nake baiwa ‘yan Nijeriya, su tsaya su yi nazari da kyau, Atiku Abubakar rahama ne ga al’umman Nijeriya, kar mu yarda da gwamnatin ‘yan farfaganda, gwamnatin fada ba cikawa, duk da ana cewa dai jiki magayi, kamar yanda nake da tabbacin kowa jikinsa ya gaya ma shi a halin yanzun. Ina kara jaddada mana in har aka kuskure wannan gwamnatin ta zarce, to wahalar da za a sha sai ta nunnunka ta yanzun, Allah Ya kiyaye ba na mana fatan hakan. Don haka, in har muna neman sauki daga halin da muke cikin sa yanzun haka a cikin kasar nan, to mu yi fitan dango mu zabi Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar, domin shi ne kadai zai fitar da mu daga cikin kangin wannan masifa da bala’in da muke ciki.
Allah Ya zaunar mana da kasarmu lafiya, Ya kuma yi mana maganin wadannan azzaluman da suke zaluntar mu.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!