Manyan Bankuna Biyu Daga Kasashen Wajen Sun Kulle Ofishinsu A Nijeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Manyan Bankuna Biyu Daga Kasashen Wajen Sun Kulle Ofishinsu A Nijeriya

Published

on


Babban Bankin Kasa CBN ya sanar da cewar, manyana Bznkuna biyu na HSBC da kuma na UBS sun kulle ofisoshin dake Nijeriya.
CBN ya sanar da ha kan ne a ranar Juma’ar da ta wuce a cikin rahoton da ya fitar, inda Bankin ya kara da cewar, manyan Bankunan sun dauki matakin ha kan ne saboda da yadda zuba jari ya yi kasa warwas a kasar nan a cikin shekara daya da ta wuce.
Bugu fa kari, Babba’ Bankin na CBN ya kara da cewar, zuba jari kai tsaye na kasar waje a cikin Nijeriya, ya sauka zuwa Naira Biliyan 379.8 daidai da kwatankwacin dala Biliyan 1.2 a cikin farkon zango shekarar daga Naira Biliyan 532.63 kwatankwacin dala Biliyan 1.7 a farkon shekara.
Koda yake Bankin na CBN, bai bayar da dalilin kulle Bankunan biyu ba.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ruwaito Babban Bankin na CBN, ya ce, yadda tattalin arzikin kasar ya kasance zangon zagayen rabin shekara ana da yakinin an samu karin hawan farashin mai da kuma sarrafawa, amma bashi da kuma fargabar kakar zaben shekarar 2019 na shugaban kasa zai janyo koma baya.
Kwarin gwaiwar da ma su son zuba jari suke dashi a cikin kasar nan, ya yi matkar rauni tun a cikin watan Agusta bayan da Babban Bankin Kasa CBN ya bukaci Kamfanin sadarwa na MTN dake Nijeriya ya dawo da dala Biliyan 8.1 cikin Nijeriya da Kamfanin ya fitar zuwa kasar waje.
A bisa binciken da Bankin na HSBC ya gudanar, a ranar 18 ga Yuli ya ce, tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari na mulki, zai iya yi wa tattalin arzikin kasar nan illa ganin cewar babu wasu tsare-tsare da gwamnatin ta sanar wajen kammala sauye-sauye da kuma raba kafa a kan ciyar da tattalin arzikin kasar a gaba mai makon ci gaba da dogaro da mai.
CBN ya kara da cewar, masu bayar da bashi su ma su na jin tsoro don kada bashin su ya makale har zuwz kashi 30 bisa dari, har ila yau, bashin da baya yin aiki, ya sauka zuwa kashi 12.4 bisa dari a cikin watan Yunin 2018 daga kashi 15 bisa dari a cikin shekarar data wuce, inda ha kan ya nuna akwai sauran jan aiki a gaba.
Don shawo kan matsalar, Babban Bankin Kasa CBN, ya umarci bankuna dake kasar nan su kara kaimi wajen karbo basussuka don kaucewa tabbaka asara a fannin tattalin arzikin kasar nan.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!