Illar Zargi A Zaman Aure — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Uncategorized

Illar Zargi A Zaman Aure

Published

on


Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon. Yau zan danyi tsokacine akan zargi. Wannan kalma ta zargi ba kalma ce me dadi ba, sai dai duk da haka mutane a yau sun doru a kai, ba fa mace ba ba ga namiji ba.

Muna cikin wani zamani na rashin yadda yayi yawa cikin al’umma musamman ga ma’aurata ,wadanda su aka fi so su yadda da junansu fiye da kowa a duniya,sai gashi a yau mace bata yadda da mijinta ba miji bai yadda da matarsa ba.

Mace

Yana da kyau ta bangaren mace ta zama me yadda da mijinta kar ta zama me yawan zarginsa da wasi_wasi a cikin alamuran da yakeyi. A duk lokacin da aka samu gidan da akwai zargi a cikin zamansu to wannan gida albarka ba ya shiga ciki sai fitina da tashin hankali a kullum. Haka miji ya daina zargin matarsa ta kowacce fuska, ya tsaya su fahimci juna, domin da a ce ana zama da zargi to gara a ce an hakura da auren baki daya don zai fi alheri. Haka ko a tsakanin yara ne iyaye su daina zarginsu akan wani abu, hakan zai fi haifar da nitsuwar zuciya.

A duk lokacin da mace ta matsa wa kanta da zargin miji karshe ta hadu da wata larurar saboda kullum lissafi da tunaninta miji na can wani wuri yana aikata ba daidai ba, idan yana gaisawa da wata, tunaninta kila budurwarsa ce ko bazawararsa, yana da kyau mu yi zama da tsarkakken zuciya a duk inda muke.

Haka da kowadanne irin mutane zama ya hada ku to ki kyautata zato. Ta kai a yanzu mace kan iya bibiyar duk motsin mijinta saboda tana zarginsa, haka shi ma namiji kan iya bibiyar matarsa saboda bai yarda da ita ba, saboda Allah a nan shin me muke son nuna wa yaran da muka haifa? Ko kawai muna so mu nuna musu zama da amana sun kare a duniya? Yadda muka dauka a yanzu akan abokan zamanmu yaranmu da ‘yan’uwanmu za su dora fiye da haka, karshe a yi ta samun matsaloli da fitintunu a cikin al’umma.

Duk macen da za ta kasance me zargi to kuwa dole za ta zama marar wadatar zuci, don a duk lokacin da miji ya yi mata alheri to fa gani za ta yi ya yi wa wata dubunsa, wannan zai sa ba za ta yaba ba balle ta yi godiya. Mu sa ni a mafi yawan lokuta mu ke haddasa wa kanmu matsaloli wanda ba za mu iya shawo kansu ba. Mace ta sa ni mijinta shi ne mutum na farko da zai zamo amintaccenta sai kuma yaranta su biyo baya, haka shi miji wadannan su yakamata ya yarda da su ya kuma amince dasu saboda sune makusantansa fiye da kowa. Aure da yawa sun mutu, wasu sun samu tangarda an warware ,wasu har yanzu ana fuskantar matsala don ba a gano bakin zaren maganar ba duk a dalilin zargi. Mata mu gyara dabi’unmu akan mazajenmu musamman a bangaren abinda ya shafi zargi, duk wata mace rufin asirinta shi ne mijinta, gatanta kuma ya kasance cikin daraja a cikin al’umma, saboda haka mu rage zargi akan mazajenmu, mu kyautata musu zato me kyau a cikin rayuwarsu, hakan zai sa mace ta kasance abin kwatance a cikin al’umma.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!