Connect with us

BIDIYO

Murucin Kan Dutse: Shin Takarar Iyantama Za Ta Hade Kan ’Yan Fim Na Kudu Da Arewa?

Published

on

A wani yanayi mai jan hankali, fitaccen jarumin finafinan Kannywood, wanda a ke yiwa lakabi da Murucin Kan Dutse, wato Alhaji Hamisu Iyantama, ya fito takarar mataimakin shugaban kasa, inda ya ke mara wa takwaransa jarumin finafinan Kudu kuma dan takarar jam’iyyar Probidence People’s Choice, wato Bictor Okhai, baya.

A 2007 dai Iyantama ya taba fitowa takarar gwamnan jihar Kano, inda wasu ke kallon hakan a matsayin dalilan su ka sanya gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau a wancan lokaci ta yi amfani da shugaban hukumar tace finafinai, Malam Abubakar Abdukarim Rabo, ta ingiza keyar Iyantaman gaban kotu, kafin daga bisani Allah Ya wanke shi.

A kakar zabe ta bana da yawa ba su yi zaton Iyantama zai sake fitowa takara ba, musamman ma da a ka gan shi a cikin tawagar ’yan Kannywood da su ka kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarar goyon baya, duk da kasancewarsa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC. Don haka sai a ke tsamman cewa, ko da Iyantama zai sake yin takara, to takarar gwamna zai nema, amma katsam sai a ka ga sanarwa da kuma fastocinsa sun cika gari a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Hakazalika da dama za su yi zaton cewa, Iyantama zai fito neman gwamnan ne, la’alla ko don yadda bidiyon abin kunyar da ya bulla, wanda a ke zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da karbar Daloli na goro. Sai a ke ganin kamar Iyantama zai yi amfani da wannan dama ya amshe kujerar gwamnan, musamman don ganin yadda babbar jam’iyyar adawa ta jihar, PDP, ta fada cikin rikicin shugabanci da neman fada-a-ji tsakanin jagorointa.

To, amma ba cinya ba wai kafar baya, idan a ka dubi abokin burmin Iyantama na takara, wato Mista Okhai, za a iya hasashen cewa, wannan wata dama ce ta musamman wacce za ta bai wa masana’antun shirin fim a Najeriya da ke bangarori guda biyu damar hade kansu, don neman mafita, saboda kasancewarsa shi ma fitaccen jarumin finafinai ne a Kudu, kamar yadda Iyantama ya ke a Arewa.

Yanzu dai za a zuba idanu a ga yadda masu sana’ar shirin fim a Najeriya za su dauki lamarin. Shin za su ba wa na waje ne alhali gida ba ta koshi ba ko kuwa za su yi dakan daka shikar daka tankaden bakin gado? Lokaci ne zai bada wannan amsa, amma dai koma mene ne an shaidi taken Jarumi Iyantama na Murucin Kan Dutse!

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: