Connect with us

KASUWANCI

Kamfani Mai Na Oando Zai Tallafawa Harkar Noma A Neja Delta

Published

on

Kamfanonin mai na Oando Plc da Nigeria Agip Oil da kuma cibiyar zuba jari a fannin samar da mai ta qasa NPIMS sun bayyana aniyar su ta zuba jarin su a fannin noma don inganta fannin a qasar nan. Sun sanar da hakan ne a lokacin gudanar da taron shekara na na manoma a qarqashin shirin Green River Projec da aka gudanar a garin Igbo-ogene dake cikin jihar Bayelsa a ranar Asabar data wuce. Bayanin hakan wanda yana qunshe ne a cikin sanarwar da suka fitar sunce, shirin ya faxakar da wayar da kan da ake buqata akan mahimmancin noma don jagorantar ciyar da tattalin arzikin qasar nan, musammana yankin Niger Delta. Sanarwar ta ce, Oando da abokin huxzar sa JV sun rabar da sama da miliyan 2.71 kayan kamun kifi guda 37,669, irin Rogo guda 200,563 kayan shuka Filanten guda 400,051 da kuma irin Masara dana Doya guda 87,003 ga manoma. A jawabin sa a wurin taron, Babban jami’in gudanar da shirin, sashen samar da makamashi da ma’danai na Oando Dakta Ainojie Irune ya ce, “mun samar da shirin ne domin taimakawa masu tasowa yadda zasu koyi darasi a nan gaba kuma akwai abubuwan darasi da qasar zata koya daga cikin shirin a kan fara yin abu qarami har ya zama babba. Ya yi nuni da cewa, abin ya dogara ne kacho kam a kan kamfanoni masu zaman kansu wajen yin haxaka don yin amfani da damar wajen taimakawar su don jihar ta shiga cikin sahun masu fitar da kaya zuwa qasashen duniya. Shi kuwa mataimakin Shugaba kuma Manajin Darakta na kamfanin NAOC Mista Lorenzo Fiorillo, ya zayyana shirin da JP yake dashi ne a nan gaba a kan shirin na Green River, da ya haxa da horas da matasa su 350 a aikin noma a 2019,tare da shirin basu tallafin dogaro da kai ga matasa su 945 a fannin koyon kasuwanci da sauran su. Ita kuwa wakiliyar NAPIMS Uwargida Edina Osifo, ta bayyana cewa, NAPIMS zai ci gaba da bayar da tallafi a fannin na noma. A qarshe ta ce, matasa suna amfani da shirin kuma ya na da kyau aga matashi ya zamo zakara a 2019 kuma ina kira ga mata kada suma su bari a barsu a baya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!