Connect with us

RAHOTANNI

Mutum 3,805 Suka Kamu Da Kanjamau A Wannan Shekarar A Bauchi

Published

on

A ranar 1 ga watan Disamban kowace shekara ne majalisar dinkin duniya ta ware na musamman domin tunawa da cutar nan mai hanzarin karya garkuwar jikin mutum wato (KANJAMAU), a bisa haka, hukumomi da kungiyoyin da abun ya shafa su kan yi gangamin fadakar da jama’a kan illar wasa da hanyoyin kamuwa da wannan cutar, da kuma wayar wa jama’a kan dangane da yanda za su bi domin kariyar kai da kuma yanda masu dauke da cutar za su ke domin samar wa kansu lafiya ko lafawar cutar.
A bisa haka ne shugaban hukumar yaki da zazzibin cizon sauro, tarin fuka, cuta mai karya garkuwar jiki na jihar Bauchi (BACATMA), Dakta Muhammad Sambo Alkali ya shaida cewar hukumarsu ta tashi tsaye wajen yaki da cutar, da kuma rage karfinsa, a cikin shagulgular tunawa da wannan ranar, sun kira wani taron manema labaru a karshen makon nan, inda yake shaida wa ‘yan jaridan cewar, a cikin wannan shekarar ta 2018, an samu mutane dubu uku da dari takwas da biyar (3,805) da suka kamu da cutar a jihar ta Bauchi, yana mai bayanin cewar an samu raguwar masu kamuwa da cutar.
A shekarar da ta gabata dai wakilinmu ya shaida mana cewar hukumar ta bayyana cewar mutane dubu 4,079 ne suka kamu da wannan cutar ta KANJAMAU, inda ake samu raguwar masu kamuwa da cutar a bisa kokarin hukumomin da abun ya shafa da kuma kara wayar da kan jama’a illolin cutar.
Dakta Muhammad Alkali, ya ke cewa baya ga gangamin fadakarwa ana kuma yin dubiya kan nasarorin da aka samu na yunkurin rage yawan mace-mace da kuma kyamar juna da ake yi wa masu dauke da cutar, ya ce duk a irin wannan ranar suka shiga lunguna da sakuna domin shelanta wa jama’a abun da ya dace kan cutar.
Ya ce, daga kididdiga ta nunar da cewar a shekarar 2001 cutar tana da karfin kashi 6.8 daga cikin al’umman jihar, inda a yanzu haka, an rage kaifinta zuwa 0.6 a cikin kashi dari.
Ta bakinsa “Mu kan yi kokarin bin hanyoyin kare dukkanin wadanda ba su kamu da cutar ba, wajen ganin mun tabbatar basu kamu ba; haka su kuma wadanda suka kamu mu daurasu kan hanyoyi da suka dace. Babban abun da muke yi dai shi ne kokarin fadakarwa, ka san idan wasu sun san hanyoyin kariyan kai, wasu kuma basu sani ba ko kuma mantuwa, don haka muke amfani da kafafen sadarwa da kuma shiga cikin lunguna da sakona wajen fadakarwa domin a samu shawo kan yanayin kamuwa da cutar da kuma yaki da kamuwa da cutar, domin jama’a su san cutar, su kuma san hanyoyin kare kai, wannan matakan namu sun taimaka sosai wajen rage yawaitar kamuwa da cutar nan musamman a jihar Bauchi”. in ji Dakta Muhammad.
Dakta Alkali ya ce, yanzu haka hukumomi sun sanya wani muradin da suke son cimmawa daga nan zuwa shekarar 2020, inda ake son a yi gwaji ga jama’a akalla kashi 90 da kuma shawo kan cutar zuwa kashi 90 a bisa, “muna son mu tabbatar mun samu riskar wadanda suke da matsalar kan wannan cutar akalla kashi 90 da aka gwada aka tabbatar suna dauke da wannan cutar daga nan zuwa 2020. Sannan, a cikin kashi 90 da aka yi musu gwajin muna son ya zama cikin kashi 90 suna samun magani yadda ya kamata; a cikin kashi casa’in da suke samun magani muna son akalla su ma an rage wa cutar karfi zuwa kashi 90 daga nan zuwa shekarar 2020. Wannan shi ne manufar da muke son cimmawa daga nan zuwa shekarar 2020 mai taken ’90,90,90 by 2020’,” Inji shi
Ya yi bayanin hanyoyin da ake bi domin daukan wannan cutar ta KANJAMAU “hanyoyin kamuwa da wannan cutar kashi uku ne, na farko ana iya kamuwa da KANJAMAU ta hanyar jima’i, na biyu kuma ana iya daukan wannan cutar ta hanyar daukan jini ko karin jini, walau ta amfani da ababe masu kaifi irin su reza, allura ne ko kuma aski matukar dai jinin wanda ke dauke da cutar ta gauraya a na wanda bai kamu ba, to zai iya daukan cutar. Hanya ta uku kuma shi ne macen da take da juna biyu za ta iya ba shi, ta wajen haihuwa gabanin haihuwar ko kuma bayan haihuwa ko ma dai a lokacin shayarwa duk uwa ta kan iya baiwa danta wannan cutar don haka mun fitar da wani tsari na kare yara daga kamuwa da wannan cutar koda mahaifiyarsu tana dauke da cutar”. In ji sa
Ya ce, daga shekarar 2017 sun duba mutane 16,588 kan cutar, daga cikinsu sun daura mutane dubu 13,503 a bisa magani domin rage karfin cutar, ya kuma kara da cewa, ya shaida cewar kashi 98 na wadanda suka daurasu a kan magani suna nan suna shan maganin yadda aka daurasu, inda kuma maganin ya samu nasarar kashi karfin kwayar cutar zuwa kashi 71 kawo yanzu.
Daktan ya kara da cewa, sun yi nasarar gwajin cutar KANJAMAU ga mata masu ciki (juna biyu) su dubu 102,591, “a bisa gwajin haihuwa ga masu juna biyu, mun samu mata masu juna biyu da suke dauke da wannan cutar, inda suka haifi ‘ya’ya 72 ba tare da su ‘ya’ya sun kamu da wannan cutar ba, don hakan mun samu nasarar ne a sakamakon gwaji da tabbatar da daurasu kan maganin da ya kamata,” Inji Dakta Alkali, ya kuma kara da cewa suna da cibiyoyin gwajin mata masu juna biyu a fadin jihar Bauchi 323 don haka ne ya nemi mata masu juna biyu suke bayar da gudunmawarsu ta hadin kai domin tabbatar da wannan.
Ya yi amfani da wannan damar wajen gode wa gwamnatin jihar Bauchi da ofishin matar gwamnan jihar Bauchi hadi da kungiyoyin tallafi na kasashen waje masu bayar wa hukumar tallafi kan yaki da cutar KANJAMAU, ya nuna gamsuwarsa kan yadda ake samun ci gaba a wannan lokacin.
Dakta Alkali ya bukaci jama’a da suke kokarin bayar da hadin kai a dukkanin lokacin da hukumomin da suke kokarin kawar da wannan cutar suka zo domin fadakar da su ko kuma bukatar su yi musu gwaji, ya bayyana cewar suna da kalubalen rashin sahale adadin dukkanin masu dauke da wannan cutar a jihar Bauchi, sai ya bayyana cewar yanzu haka suna da shirye-shiryen da za su gudanar kashi-kashi domin fadakarwa da kuma nusar da jama’a illolin da ke cikin wanna cutar domin ganin an samu raguwar kamuwa da shi da kuma yakarsa.
Wakilinmu dai ya shaido mana cewar tun a shekarar da ta gabata ne kudurin yin gwaji kafin aure ya zama doka a jihar Bauchi, da kuma kudurin hana kyamatar masu dauke da cutar, inda jihar ta sanya dokar duk wanda aka samu da nuna kyama wa masu dauke da cutar zai fuskanci hukunci, hakan na taimakawa wajen yaki da cutar da kuma shawo kansa hadi da rage masa karfi a jihar ta Bauchi.
Usman Ziko shi ne shugaban masu dauke da wannan cutar a jihar Bauchi ya yi tsokaci kan halin da suke ciki, inda ya shaida cewar suna samun kyakkyawar fahimta a tsakaninsu da ma’aikatan lafiya don haka ne ake kara samun ci gaba na rage kamuwa da cutar a jihar ta Bauchi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: