Connect with us

KASUWANCI

Nijeriya Ta Yi Tsimin Dala Biliyan 21 Ta Hanyar Rage Shigo da Abinci A Cikin Wata 34 — Emefiele

Published

on

Gwamnan Babban Bankin Qasa CBN Godwin Emefiele ya sanar da cewa, yawan abincin da ake shigowa dashi duk wata zuwa cikin Nijeriya ya faxi daga dala miliyan 665.4 a cikin Janairun 2015 zuwa dala miliyan 160.4 a cikin Okutobar 2018. Ya ce, ragin da aka samu an same shi ne a fannin Shinkafa, Kifi, Madara, Sikari, Alkama. Ya ci gaba da cewa, za’a ci gaba da kare tsarin. An kuma samu ragin daga dala miliyan 665.4 a Janairun 2015 zuwa dala miliyan160.4 a Okutobar 2018, inda hakan ya nuna cewar, an samu ragin kashi 75.9 busa xari na rarar sama da abincin da aka shigo dashi. Babban abin da yake na zahiri shi ne, kashi 97.3 bisa xari na ragin shigo da Shinkafa, inda aka samu kashi 99.6 bisa xari na Kifi dake da kashi 81.3 bisa xari na Madara 63.7 sai kashi na Madara da kuma kashi 60.5 bisa xari na Alkama. Ya ce, muna farin ciki da samun wannan cin nasarar da muka samu, inda ya ce, wannan tsarin ana sa ran zai ci gaba don samar da daidaito a fannin tattalin arzikin qasa. Emefiele ya bayyana hakan ne liyafar cin abincin dare a Legas. Da yake tsokaci a kan fannin kuxi ya ce, idan aka yi la’akari da rawar da CBN yake takawa wajen rage shigiwa da kaya cikin qasar nan, ya qara inganta ayyukan sa na fannin kuxi. Ya ce, zamu ci gaba da baiwa manoma tallafi, da bayar da tallafi a fannin matsakaitan sana’oi ta hanyar shirin mu na noma na Anchor Borrowers da kuma sauran tallafi na kasuwanci. Acewar sa, CBN a kwanan baya ya gabatar da shirin bayar da tallafi na kuxi na RSF a bisa kashi tara bisa xari na sababbin ayyukan noma da kuma samar da ayyukan yi. Acewar sa, a cikin shirin na Anchor Borrower ya taimaka wajen rage shigiwa da Shinkafa cikin qasar nan. Ya ce, a cikin Okutobar 2018, Jimlar manoma su 862,069 sun noma kadadar data kai yawan 835,239 na amfanin gona da ban-da-ban har sha shida da suka amfana da shirin na Anchor Borrowers wanda kuma ya smar da ayyukan yi har guda 2,502,675 a xaukacun faxin qasar nan. Har ila yau, saboda mahimmancin da shirin yake dashi, a ranar 21 ga Nuwambar 2018, kwamitin tsarin kuxi ya bayar da shawarar a faxaxa shirin zuwa ga fannin noman Tumatir, Manja da kiwon kifi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!