Connect with us

LABARAI

2019: Jirgin Yakin Neman Zaben Atiku Ya Isa Ilorin

Published

on

Jirgin yakin neman dan taakarar jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya isa zuwa yankin Arewa ta tsakiya. Za a gudanar da zaben ne a Ilorin, jihar Kwara.
Atiku dai ya fara yakin neman zaben sa ne jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso kuddancin Nijeriya a ranar litinin.
Haka kuma, bayan na Arewa maso tsakiyar, sai kuma ranar Alhamis a Ibadan, jihar Oyo.
Daraktan yada shirye-shiryen PDP na kasa, Kola Ologbondiyan tare da sakataren jam’iyar PDP na Kwara ne suka tabbatar da labarin.
Ashaolu ya bayyana cewar, za su gabatar da taron ne a ‘Metropolitan Skuare’. Ya kuma yi kira ga magoya bayan su da su fito kwansu-da-kwarkwata domin nuna goyon bayan su ga jam’iyar da dan takara.
A cikin wata sanarwar manema labarai da Ashaula ya fitar, ya yi wa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo barka da zuwa jihar wurin taron kaddamar da gidauniyar tallafin kananan yan kasuwa wato ‘Trader Moni’.
Sai dai kuma, ya zargi ziyarar da ya kai, in da ya ce, ziyarar siyasa ce ta salon sayen kuri’un mutane. “Mun lura cewa, tun a shekarar 2015 aka kaddamar da wannan shirin ‘TraderMoni’ din, a tsawon shekaru 3 daga 2015, mataimakin shugaban kasar bai taba kai ziyara wata jiha ba kan shirin, amma yanzu da karasowar zabe, ya shiga yawon kai kudin tallafin a Kasuwannin Nijeriya.”
“Muna fatar kada wannna ya zama wata makarkashiyar saye mutane ce a zabe mai zuwa.”
“To kuma, muna gargagadi wurin raba kudin, kada asa son-kai wurin rabawa.”
“Dole ne mataimakin shugaban kasa tare da mukarraban sa su yi adalci wurin rabon ba tare da kula da wace Jam’iyar siyasa mutum yake ba. Saboda wannan shirin Gwamnati ne ba wai na Jam’iyyar siyasa ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: