Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Cafke Gungun ‘Yan Fashi Da Makami A Imo

Published

on

Rundunar ‘yan sandan na F-SARS da ke jihar Imo ta samu nasarar cafke gungun ‘yan fashi da makami da garkuwa da mutane wadanda suka addabi yankunan Ndiuche da kuma Arondizuogu cikin jihar. Kwamishinan jihar Dasuki Gladanchi ya bayyana cewa, wadanda ake zargin dai su ne; Chikwendu Udeoye dan shekara 34, Agafechukwu Ojukwu dan shekara 34, sai kuma Madwell Odenigbo mai shekaru 45, wadanda rundunar ‘yan sandan F-SARS wanda kwamanta Geoffrey Bictor yake jagoranta, suka cafke a ranar 23 ga watan Nuwamba ta shekarar 2018. Kwamishinan ‘yan sandan ya ce, “Wadanda ake zargin an samu nasarar cafke su ne a Ndiuche Arondizuogu cikin karamar hukumar Ideato da ke jihar Imo, wanda rundunan ‘yan sanda na F-SARS wanda kwamanta Bictor Godfrey yake jagoranda, karkashin kulawar ASP Banjoko Oluwemimo bayan bayanan sirri da suka samu.
“Wadanda ake zargin dai su ne; Chikwendu Udeoye dan shekara 46 da kuma Agafechukwu Ojukwu mai shekaru 34, dukkanin su ‘yan asalin Ndiuche Arondizuogu da ke cikin karamar hukumar ldeato. Sai kuma Madwell Odenigbo dan shekara 45 daga garin Umuakam cikin karamar hukumar Ideato ta Kudu. “’Yan fashin sun addabi yankin da fashi da makami da kashe-kashe da kuma yin garkuwa da mutane a cikin kwanakin nan. Ana kokarin cafke sauran ‘yan fashin wadanda suka gudu.”
Galadanchi ya bayyana cewa, za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban shari’a, sannan a tursasa musu barin jihar. Kwamishinan ya kara da cewa, duk lokacin bikin Kirsimeti, rundunar tana kara wasu dubaru a cikin yankuna wadanda za su dakile ayyukan ‘yan ta’adda, kamar yadda babban Sufeto ‘yan sanda ya bayar da umurni.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!