Connect with us

WASANNI

Babban Burina Shi Ne Buga Wa Real Madrid Wasa –Depay

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Lyon, Memphis Depay, dan kasar Holland ya ce yanason watarana ya buga kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ko Barcelona domin a cewarsa duk duniya babu kungiyoyi masu darajarsu.
Depay, dan shekara 23 ya koma Manchester united a shekara ta 2015 sai dai kwallon bata karbeshi ba a kungiyar inda daga baya kungiyar Lyon ta siyeshi sai dai da sharadin cewa idan za ta siyar dashi sai ta fara tuntubar Manchester United din.
Depay ya ce, yana tunanin watarana zai koma Real Madrid ko Barcelona , inda ya ce wannan shi ne babban burinsa kuma yana saran nan gaba burinsa zai cika amma kuma sai ya cigaba da dagewa da buga wasa mai kyau.
Ya ce abin da yafaru dashi a Manchester united daga Allah ne kuma yana fatan zai dawo da kokarinsa a kungiyarsa ta Lyon indai yanason shiga Real Madrid ko Barcelona wadanda basa siyan ‘yan wasan da ba kwararru ba kamar yadda aka sani.
Tsohon kociyan Manchester united, Luis Ban Gaal ne ya siyo dan wasan daga kungiyarsa ta PSB dake kasar Holland akan kudi fam miliyan 30, sai dai dan wasan bai buga abin a zo a gani ba a kungiyar inda a watan janairun kakar wasan data gabata kocin kungiyar na yanzu Jose Mourinho ya siyar dashi zuwa Lyon din.
Kawo yanzu dai tauraruwar dan wasan tana haskawa a gasar rukuni rukuni ta kasar Faransa inda yake tallafawa kungiyarsa wajen samun nasara a wasanni kuma suna buga gasar cin kofin zakarun turai
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: