Connect with us

KASUWANCI

Kasuwar Hannun Jari Ta Yi Asarar Naira Biliyan 581 A Watan Nuwamba

Published

on

A cikin watan Nuwamba, Kasuwar hannun jari ta kasa NSE ta yi asarar naira biliyan 581. Kyan da aka yi hada-hadar su a kasuwar, sun kai na naira tiriliyan 11.852 a ranar 31 ga watan Okubar 2018, ya sauka zuwa naira tiriliyan 11.271 a ranar 30 ga watan Nuwamba. Kokarin da kasuwar ta yi shine mafi muni a a cikin wanan satin. Sakamakon hakan, dukkan shiya ta fadi a kan hudu daga cikin biyar na kasuwancin da aka yi cikin satin, inda aka samu asara da kashi 2.5 bisa dari na wannan satin, inda ta yi daidai a a kan 30,874.17.
A cikin shekarar zuwa yau, an kara samun asarar da ta kai kashi19.3 bisa dari . Har ila yau, a satin day a wuce, hada-hada a kasuwar ta ragu da kashi 25.2 bisa dari da kashi 50.6 bisa dari da miliyan 249.422 da kuma biliyan 2.393. An kum samu jimlar shiya da ta kai biliyan 1.199 wadda kudin ta ya kai naira biliyan 14.277 a cikin hada-hada guda 15,841 a cikin satin da masu zuba jari suka zuba suka zuba a kasuwar data kai ta shiya biliyan 1.282 da aka kiyasta kudin sun kai naiar biliyna
3.142 da aka yi musayar su a cikin satin day a wuce na hada-hadar data kai 11,467.
Masu yin fashin baki a kamfanin Betiba Capital Management sun yi kiradadon cewa, sunja kunne akan kiyaye hakan a nan gaba. Kasuwar a cikin rahoton ta data fitar na satin, ta sanar da cewa, hada-hadar kudi an auna tat a kai yawan shiya miliyan 963.315 da kudin ya kai naira biliyan 7.536, inda ka yi hada-hadar da ta kai 8,871.
Acewar ta, hakan ya sanya an samu kashi 80.38 bisa dari da kuma kashi 52.79 bisa dari na kudin shiga. Kayan da ake yin amfani dasu sun kai shiya miliyan 83.001 na shiya miliyan, inda kudin su ya kai naira biliyan 4.213 na hada-hada guda in 2,802.
Wanada yazo na uku sune kayan da masana’antu suka sarrafa shiya data kai miliyan 60.782, inda kudin ya kai naira biliyan1.976b da kuma hada-hadar data kai ta 1,639 deals. Hada-hada uku ta Bankunan DiamondPlc, Access Ban Plc da kuma Kmafanin Inshora na Unibersal Insurance Plc, da nasu ya kai shiya miliyan 512.535, daidai da kudi naira biliyan 1.367 a cikin hada-hada guda 1,437, inda aka samar da kashi 4 9.57 bisa dari. Farashin kayan sun fadi kasa a cikin satin, inda kuma farashin kaya sha hudu ya sauka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!