Connect with us

WASANNI

Mourinho Ya Yi Amai Ya Lashe

Published

on

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, ya ce burin da ya dauka na zama cikin kungiyoyin hudun farko a gasar firimiya a karshen Disamba ya sauya saboda bashi da ‘yan wasan da zai iya yin hakan.
Mourinho ya yi fatan ne kafin karawar da Manchester United ta tashi babu ci da kungiyar Crystal Palace a ranar 24 ga watan Nuwamban da ya gabata inda ya ce kungiyar tasa za ta iya zama cikin manyan kungiyoyin hudu na farko.
Haka kuma bayan da kungiyar ta buga 2-2 a gidan Southampton, ya sa ta koma ta bakwai, ba ta cikin jerin wadanda za su buga gasar Champions League a wannan matakin idan har aka kammala kakar wasa a haka.
Rabon da Manchester United ta yi nasara tun 3 ga watan Nuwamba da ta ci 2-1 a gidan Bournemouth inda ta buga canjaras da kungiyar Crystal Palace da kuma kungiyar Southampton a satin da ya gabata.
“Kungiyoyi da dama sun samu canji a kungiyoyinsu amma banda kungiyarmu saboda bamu siyi ‘yan wasan da ya kamata ba kuma bama buga wasa irin na yadda ragowar kungiyoyin suke bugawa” in ji Mourinho
Manchester United itace ta biyu a cikin rukuni a gasar cin kofin zakarun turai yayinda kungiyar Jubentus take mataki na farko kuma tuni kungiyar tasamu tikitin zuwa zagaye na biyu na gasar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!