Connect with us

MANYAN LABARAI

Paparoma Zai Ziyarci Hadaddiyar Daular Larabawa A Watan Fabrairu  

Published

on

Paparoma Francis, zai ziyarci birnin Abu Zahbi na hadaddiyar daular larabawa, a kokarin shi ne na ganin ya samar da alaka mai kyau tsakanin mabiya addinin Kiristanci da na Musulunci, fadar Vatican ce ta bayyana wannan a yau Alhamis, inda ta ce Paproman zai yi ziyarar ne a watan Fabrairun shekarar 2019.

Babban limamin Kiristan zai ziyarci kasar ne bayan da yarima mai jiran gado na kasar ya gayyaci paparoman, tare da hadin gwiwar cocin mabiya darikar Katolika na kasar ta hadaddiyar daular larabawa, paparoman zai halarci babban taron tattaunawa tsakanin mabiya addinai wanda za a gabatar a ranakun 3 zuwa 5 ga watan Fabrairun shekarar 2019.

Paparoman mai shekaru 81 a duniya ya ziyarci wasu daga cikin kasashen Musulmi a duniya, inda ya fara ziyartar kasar Turkiyya a shekarar 2014, sai kasar Azarbaijan a cikin shekarar 2016, da kuma kasar Masar a cikin shekarar 2017, sai hadaddiyar daular Larabawa da zai ziyarta a mtsayin kasa ta hudu a jerin kasashen Musulmi.

Daga cikin batutuwan da Paparoma Francis zai fi maida hankali a ziyarar da zai yi sune, samar da fahimta a tsakanin mabanbantan ra’ayoyi da fahimta, sannan sai tattaunawa don yakar masu ra’ayin rura wutar gaba tsakanin mabiya addini, musamman mabiya addinan Musulunci da na Kiristanci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: