Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kori Ma’aikatan Da Ba Su da Kwarewa A 2020

Published

on

Gwamnatin tarayya za ta fara korar Malaman makarantar da ba su cancanta ba a cikin kasar nan daga watan Janairu 2020, sakamakon karewar wa’adin da ta ba su na su daukaka cancantar na su kafin karewar watan Disamba 2019.

Magatakardan hukumar tantance malaman makaranta, Farfesa Josiah Olusegun Ajiboye, ne ya bayyana hakan a Abuja, sa’ilin da yake magana da manema labarai.

Farfesa Josiah Olusegun Ajiboye ya ce, “Gwamnati ta dauki wannan matakin ne tun da jimawa, na cewa duk malamin makarantar da bai cancanta ba, ko ba shi da rajistta da hukumar tantance malaman ta kasa har ya zuwa watan Disamba 2019, ba za a ci gaba da kyale shi yana koyar da dalibai ba a cikin aji.

Ya yi nuni da cewa ya zuwa yanzun hukumar tantance malaman ta yi rajistar Malaman da suka cancanta milyan biyu a sassan kasar nan, ya ce duk wani malamin da bai yi rajistan ba ya zuwa watan Janairu 2020, za a fitar da shi daga cikin ajin koyar da dalibai.

Shugaban hukumar ya yi nuni da cewa, sun gudanar da kidayar malaman makarantun a Jihohi shida, da wadannan Jihohin ne za mu fara saboda muna da alkalumman yawan wadanda suka cancanta da kuma wadanda ba su yi rajistan ba.”

A cewar sa, Jihohin shida sun hada da, Nasarawa, Ogun, Ebonyi, Jigawa, Kros Riba da Bauci.

“Da wadannan Jihohin ne za mu fara, mu kuma ci gaba har sai mun tsarkake dukkanin makarantun kasar nan daga illar malaman da ba su cancanta ba.

Magatakardan ya nanata mikidarin cancantar da ake nema daga kowane malamin makaranta domin koyarwa a cikin kasar nan, wanda shi ne, takardar shaidar NCE, wanda da ita ce malami zai iya yin rajista da hukumar na su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!