Connect with us

MANYAN LABARAI

Muna Nan Kan Bakar Mu Na Shiga Yajin Aiki Gobe –Kungiyar Malaman Makarantun Kimiyya Da Fasaha

Published

on

Kungiyar malaman manyan makarantun kimiyya da fasaha ta kasa (ASUP) ta ce har yanzu tana kan bakar ta na tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani a dukkan makarantun kimiyya da fasaha da suke a fadin kasar nan, a gobe 12 ga watan Disamba, 2018.

Shugaban kungiyar na kasa, Malam Usman Dutse ne ya bayyanawa manema labarai  hakan a yau Talata, bayan zaman tattaunawa da ‘ya’yan kungiyar suka gudanar a garin Legas, kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da rashin cika alkawarin da ta daukar wa kungiyar a shekarun 2009 da kuma 2017.

Muna da taron kungiyar mu na kasa a ranar 17 ga watan Disamba, amma kafin ranar zamu fara yajin aikin sai baba ta gani, ban san mai zai biyo baya a zaman taron ba, ba zamu janye wannan matakin yajin aikin ba, har sai an biya mana dukkan bukatun mu, ba wata makarantar da za ta gudanar da wani abu daga gobe Laraba.’ Inji Dutse
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!