Connect with us

KASUWANCI

Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Karu Da Dala Miliyan 101 Daga Kimiyyar Sadarwa – NITDA

Published

on

Darakta Janar na Hukumar kimiyya ta kasa NITDA, Dakta Isah Ibrahim Pantami ya sanar da cewar, a cikin zango uku na shekara sadarwa ta kimiyya ta taimakawa wajen samarwa da tattalin arzikin kasar nan dala miliyan 101. Pantami ya sanar da hakan ne wani taron kamfanonin kimiyya da sashen kimiyya na hukumar ya shirya a garin  Abuja a ranar juma’ar data wuce. Ya ci gkba da cewa kimiyyar ta (start-up),ta taimaka wajen samar da jimlar dala miliyan tara ga tattalin arzikin kasar nan a cikin watanni uku na shekarar, inda ya kara da cewa, hakan ya kuma karu zuwa dala miliyan 57 a cikin zangon na biyu na shekarar har ya kyuma kark haurawa zuwa dala miliyan 35 a cikin zangin shekarar na uku. Ya ce, a bisa wknnan dan karamin kikarin da muka yi am samu gagarumar nasara a fannin a yau. Ya ci gaba da cewa, a cikin zangin farko na 2018 kimiyyar ta start-ups ta tara dala miliyan  tara, inda a zangon shekarar na biyu kuma aka tara dala miliyan 57 haka a kwanan baya a zabgon shekarar ta uku aka tara dala miliyan  35. Ya yi nuni da cewa, wannan babbar nasara ce da ba’a taba samu ba a fannin a tarihin kasar nan. Ya sanar da cewa, amfanin da kayan gida na kimiyya ya karu sosai a kasar nan, musamman bayan da gwamnatin tarayyar ta wanzar da tsarin a sayi kayan da ake sarrafawa a cikin kasar nan. Acewar sa, hukumar ta kuma kai rahotin hukumomin gwamnati da suka ki bin umarnin na gwamnati ga hukumar EFCC na kin yin amfani da kayan da ake sarrafawa na kimiyya a cikin kasar nan. Ya ce, bayan da EFCC ta  tuhumi manyan jami’an na hukumomin sun shiga taitayin su inda hakan ya sanya aka kara samun hukumomin na gwkmnatin da dama da suke yin amfani da fasahar ta cikin gida. A wata sabuwa kuma, ministkn sadarwa Mista  Adebayo Shittu, ya danganta yadda aka samu nakasu wajen kai kimiyyarr Nijeriya mafi kasa a duniya saboda rashin samar da tsare-tsaren da suka dace da kayan aiki a kasar nan.  Shittu ya sanar da hakan ne wani taro a garin Abuja, inda ya ce cibiyar ana bukatar ta dinfa samar da bayanai da ake bukata  don yin nazari a kansu. A karahe ya ce, ana kuma son cibiyar ta samar da hanyoyin yin hadaka don ciyar da fannin sadarwa na kasar nan gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!