Connect with us

RA'AYINMU

2019: Sai A Yanzu Ne Ikon Alkalanci Zai Dawo Hannun Talakan Nijeriya!

Published

on

Manufar gudanar da zabe na zango-zango shi ne, bai wa masu kada kuri’a damar su yi wa wadanda su ka zaba alkalanci kan amanar da su ka damka mu su a lokacin zaben baya. Wannan ne dalilin da ya sa kasashe duniya, wadanda su ke bin tsarin dimukradiyya su ka saka wa kansu abinda a ke kira da wa’adin zango.
Wannan dama ta yin alkalanci a kan wadanda a ka zaba ba a hannun kowa ta ke ba face talakan kasa. Shi kundin tsarin mulki ya bai wa damar da alhakin yin wannan alkalanci, kamar yadda su kuma wadanda a ka zaba a lokacin zaben da ya gabata su ne wadanda su ke da iko da alhakin yin alkalanci kan yadda za a tafiyar da kasar daidai gwargwadon bukatar talakan kasa. Karewar wa’adin zangon mulkinsu ya na nufin cewa, waccan dama tasu ta zo karshe kenan; yanzu kuma iko ya dawo hannun talakan da ya tun asali ya zabe shi.
Ashe kenan abin lamarin ya zama na hannun karba hannun mayarwa kenan kuma abinda ka shuka shi za ka girma, domin idan har talaka bai sarayar da nasa ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi ba, to babu yadda za a yi duk wanda a ka zaba bai kulla ma sa abin a zo a gani ba ya sake zarcewa.
Kamar yadda a lokacin da wanda a ka zaba ya ke dage wa a kan wani abu kai da fata ya ce shi ya ke son aiwatarwa a lokacin da ya ke kan mulki la’alla ko a na so ko ba a so, haka nan shi ma talakan kasa ya na da damar da zai dage kai da fata ya ce ya gamsu ko gamsu da sake zaben wanda ya ke kan mulki ba, domin shi ma tasa damar kenan.
Dole ne talakan kasa ya gane cewa, shi ne mai wannan damar ta yin hukunci a lokacin zabe, ba wani daban ba kuma babu wanda zai iya sarayar ma sa da wannan dama matukar ba da yardarsa ba. Don haka kada a zare ma sa idanu a dora shi oan tafarkin da zai kai shi ya baro shi, domin wannan wata dama ce wacce a baya talakan kasa ya taba gwada kuma ya yi nasara, inda a babban zabe na shekara ta 2015 shugaban kasa mai ci ya fadi a zabe, kuma a ka rasa yadda za a yi a juya sakamakon zaben, saboda talaka ya jajirce a kan cewa lallai sai an ba shi abinda ya zaba.
Wannan ya na nuna cewa, ashe talakan Najeriya zai iya yin amfani da damarsa da kuma ikon da kundin tsarin kasa ya ba shi ba tare da wani ya iya tauye ma sa ba a babban zaben 2019. Saboda haka talaka zai iya amincewa wadanda su ke kan mulki su zarce bisa son ransu ko kuma su yi kememe su ki yarda, idan har ba su gamsu da yadda a ka tafiyar da amanar da su ka aiki shugabannin da ke kai su aiwatar mu su ba.
Babban abinda zai iya kara bai wa talakan kasa kwarin gwiwa shi ne, tabbas yanzu akwai karancin tafka magudi a zabukan Najeriya. Wannan ya samo asali ne tun daga babban zaben 2015, kuma za a iya cewa, kullum cigaba a ka kara samu kan hakan.
Don haka kiranmu ga talakan Najeriya shi ne, kada gwiwarsa ta sage har ta dauka cewa, zaa iya ba shi abinda ba shi ya zaba ba; talaka ya fita filin zabe da kwari gwiwa cikin dakakkiyar zuciya tare da kyakkyawan zaton cewa za a sanar da wadanda su ka samu kuri’a mafi rinjaye a matsayin wadanda su ka lashe zaben 2019 ba tare yi ma sa wuru-wuru ba.
Abin misali a nan shi ne, idan talaka ya gamsu cewa, gwamnatin APC a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta rike amanar tare da aiwatar da alhakin nauyin da kai talaka ta dora ma ta a 2015, to ka fita gaba-gadi ka sake zabenta ba tare da fargabar cewa, za a murde wannan zabe ba.
Haka nan kuma, idan talaka bai gamsu da yadda APC da Buhari su ka rike amanar da a ka dora mu su ba, to talaka ya fita da niyyar kawar da gwamnati, don kawo wacce za ta iya rike wannan amana tasa.
Bugu da kari, idan har talakan Najeriya ya na jin cewa, a yanzu jam’iyyar PDP ta ji a jikinta, saboda korar karen da talakan ya yi ma ta a 2015 karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa kuma dan takararta, Goodluck Ebele Jonathan, har jam’iyyar ta yi nadama da danasani ta hanyar sauya dan takara maimakon ta sake tsayar da Jonathan, sai ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, to talaka zai iya fita gaba-gadi ya zabi PDP bisa tsammanin cewa, za ta gyara kurakuranta na baya, ba tare da fargabar za a murde ma sa zaben ba.
Wannan zabi ya rage wa talakan Najeriya n shi kadai, idan a ka yi la’akari da kundin tsarin mulkin kasa da kuma dokokin zabe. Fatanmu dai shi ne Allah ya kawo mafificin zabi a 2019!
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!